Chapter 13
Chapter 13
rawa a tunaninsa irin yan fashin nan ne wadanda zasu nemi taimako, idan katsaya kataimaka musu sai kuma suyi maka fashi, tsoro yakashi sosai, yanayinta bai nuna tana cikin natsuba sannan kuma sai yaganta tana hawaye hakan yasa wata zuciyar tace masa yatsaya, Daf da ita dirver yazo yatsaya, ya kura mata edo yana kallonta, rumaisa tana kuka take fadan "dan Allah malam katai makamun walh saceni akayi" shidai yayi kuru yana kallonta kyankyawar gaskice, a zuci yake fadan "wannan ba mutum bace Aljanace" nan yafara kwararo adu'oi, naneman tsari Ganin baice mata uffan ba yasa tafara Taku takaraso kusa da motar, a lokacin driver ya dube bakinta yaga duk jini, yakara tsorata sosai, azuci yace "wayyo Allahna yau hadu da aljana mai cin mutane" muryarsa narawa yake furta "kukuke ganinmu bami muke gani kuba, dan Allah karki cutamun wlh ni taimakonki natsayayi" Rumaisa tace "wlh ni mutum ce kamar kai, idanma baka yardaba ga hannuna kataba kaji" ta zura masa hannun tana kuka, Jikinsa narawa yakai hannunsa saman jikin Rumaisa, sai yaji laushi, Yadubeta yayi ta maza yace "malama lafiya meya fito dake cikin wannan tsohon daren," Rumaisa ta fashe da kuka tana fadan "dan Allah kataimakeni kakaini sokoto, wanine ya saceni,na samu kubuta daga hannunsa, shine na gudu" Har a lokaci bai yarda da rumaisa ba leko kansa yayi ta glass din motar yana kallon kafar Rumaisa ko zaiga kofato, sai yaga kaface irin tasa a lokacin ya kara tabbatar dacewa itama mutum ce kamar sa, ajiyar zuciya yayi sannan yace "kwantar da hankalinki, Allah ne yakawo miki ni, domin ni yanzu haka Sokoto zan nufa, ya bud'e mata kofar motar sannan yace "shigo muje" Bakaramin dadi rumaisa tajiba, tace "nagode, nagode" tashare hawayenta sannan ta zagaya tashiga motar suka lula zuwa sokoto, A cikin motar yadauko wani tsumma ya mikawa rumaisa yace " ga wannan ki goge jini dake jikinki, kafin zuwa gobe idan mun sauka sai mu nemi clinic agubaki" Ba musu rumaisa ta karba, ta goge jikinta sannan tasa tsumman ta toshe bakinta dai dai gurin dake fitar da jini, Divern yadan kauda kansa daga tukin dayake ya dubi rumaisa yace " kekuwa garin yaya aka saceki daga sokoto zuwa abuja" Nan Rumaisa tashiga kwararo masa bayani, amma saidai tamasa karya, saboda bata gaya masa gaskiyar cewa ita yar Abuja bace, Bayan tagama gaya masa, Driver yayi ajiyar zuciya sannan " Allah sarki, sai kuma yayi shiru sai cen sannan yace " Allah yaka kareki daga shairinsa" Tace "ameen" sai kuma tayi shiru, bata mason yawan surutu saboda ciwon dake bakinta, dama zai kyaleta da yafi mata, Driver yace " nikuwa kinga lodi ne yakawoni garin nan, kuma nasauke shine zan kara komawa na dauko sannan kuma nadawo" Girgixa masa kai kawai rumaisa tayi, Nan dai yaci gaba da xuba mata suturu, sai kace bbc, Rumaisa kuwa banda toh da him babu abnda take ce masa, Daya lura dacewa bata son yawan magana, dolensa yakyale ya maida hankalinsa ga tukinsa Gudu suke tsalawa kamar sutashi sama koda akace maka asuba takusa sun kusa karasowa sokoto.. Karfe 8:30, na safe suka karasa sokoto, lokacin har rumaisa tayi bacci, Mutumen yatadata, tatashi yace " gamu munzo sokoto, ni a nan zan tsaya cikin gareji domin baza a barni na fita ba" Rumaisa Tace "tohm " tana kokarin fitowa daga cikin motar, Driver yasaka hannunsa cikin aljihu yaciro naira 200 ya mikawa rumaisa " ungo wannan kyasamu ki hau keke napep" Rumaisa ta karba tayi masa godiya, sannan yace "toni zan wuce " Rumaisa ta kada masa kai cikin yanayin tausayi, sannan ta sauko daga cikin motar, shikuwa ya rufe motar yafice yabar gurin, yabarta tsaye a gurin Zuciyarta tashiga harbawa 9-9, nan tafara zancen zuci yanzu gata cikin garin sokoto saidai kuma btasan inda zata jeba, daman duk zuwan dasuke a motar abba suke zuwa, kuma idan sukazo basa wuce wuni daya, sai kuma sukoma, hakan yasa ko sunan unguwar da kakar tata take bata saniba, shiru tayi tana kallon garejin, sai taga kowa harkar gabansa yake babu wanda yadamu dawani, a hankali tafara taku ta sami wani gefen acikin garejin ta rakube tana cizon labba duk ciwo takeji a jikinta, *** ** Wata babbar motace bus irin wadda tasauke rumaisa yanzu taja birki a cikin garejin, mutane sai fitowa suke, Yafito daga cikin motar zuciyarsa fal da farin ciki, a hankali bakinsa yake furta " alhamdulilla" Kallon daya nayiwa mutum daya fito daga cikin motar yanzu, naga kamar nasansa, tsaye yayi yana kallon garejin gefe da gefe, Caraf edonsa yafada kan rumaisa datake rakube a gefen gereji, zare edo yayi cike da mamaki, yakara furta " alhamdulilla" cikin sanda yake tafiya, kamar barawo yazo sata, ta yadda bazataji hayaniyar zuwan saba har ya karasa gurinta, da zuwansa ya cafki hannunta, cike da tsoro da firgita rumaisa ta daga kanta ta kallesa, gabanta yayi mummmunar faduwa, taje zatayi ihu ya toshe mata baki..... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:45 PM] +234 905 395 7618: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 59 and 60 Via *OHW* _A love story_💝 Tsorata sosai abban fahad yayi a lokacin da aka sanar dashi cewa fahad yana asibiti, Bayama 9ja suna American shida umman fahad amma a ranar suka hawo jirgi suka shigo 9ja, Karfe 10:30 na safe jirginsu yasauka a airport dake garin abuja, tun a cikin jirgin mahaifiyar fahad take kuka, abban fahad sai lallashinta yake, da kyardai yasamu ta saurara, Suna saukowa cikin jirgi motoci suka dira a airport din, daman abban fahad yasa a kawo musu moter, nan suka shiga motar suka suka wuce asibiti, Suna karasawa bakin asibitin abban fahad ya dubi asibitin ya tsuke fuska "wht anan aka kawomin yaro" yafada a sanyaye, ransa a bace ya shiga asibitin a wulakance yake kallon mutane, yakarasa dakin da fahad yake, a kwance suka samesa duk ansaka masa bandej a jiki, umman fahad takarasa gurin fahad tana kuka, tarike masa hannu, Abban fahad kuwa ma'aikatan yahau da masifa, fada sosai yayi musu ransa ya bace daga karshe yake cewa "wannan wane irin kauyancine da gigadanci, zaku kawomin yarona wannan karamar asibitin me suka sani, asibitin da kowane talaka zai iya kawo d'ansa, abban fahad yayi huci ya dube ma'aikatan, duk sunkuyar da kansu kasa, sannan yace "duk na koreku daka aikin tsaron yarona, domin naga bazaku iyaba" ma'ai katan suka shiga bashi hkr, amma sam yaki hkr, mahaifiyar fahad itama fada tamusu sosai itama ta goyi bayan maganar mijinta, sannan abba yafita yaje yasami likita yace yanaso ya bashi transfer zai dauke yaronsa daga asibitin zuwa wani babban asibiti, ba musu likitan ya yanka masa, yakarba suka dauki fahad suka bar asibitin dashi, wata babbar asibiti suka kaisa, saboda har a lokacin bai farka ba. Duk glass yayanke masa jiki, Likitoci sukayi masa aiki sosai sannan suka bada yakinin cewa insha Allah daga nan zuwa gobe zai farka, Abban fahad yace "toh shikenan" anan suka wuni asibiti suna jinyarsa, mahaifiyar fahad ta tambayi abban fahad "waishin meya faru da fahad ne" abban fahad yace " nikuwa ta ina zan sani, bayan nidake duka bama kasarnar, mudai jira yafarka sai ya gaya mana da kansa" Haka suka zauna ko wannesu cike da bacin rai da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37