Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

Majnoon Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

cike da fargaba, Washe gari Tatashi bataji motsinsaba, tafito taje har dakinsa bata ganshiba, hankalinta yasoma tashi, ta zurawa lamarin Allah edo, Haka har yamma tayi baidawo hankalinta yatashi sosai duk ta sukukuce, takasa yin komai, sai taji gidan duk baya mata dadi saboda baya nan, Misalin karfe 10:03 na dare tana rakube akan kujera cikin falo tana jiran dawowar fahad, amma taji shiru, gangadine yafara dibarta, bata ankaraba bacci yayi awon gaba da ita, 11:00 fahad ya dawo gidan, yanayin bude motarsa kawai nagani nace akwai matsala domin kuwa da karfi tsiya ya turo kofar, Sai kuma naga yana fitowa a hankali, yana tangadi kamar zai fadai ko ba a fadamin ba nasan giya yasha yayi mankas domin ko tsayi gagara yi yayi yana tangadi yafadi sai kuma yagagara tashi, Bodyguard dinda ke tsaye a bakin kofar suna kallonsa sukazo gurin, " oga lfy" Cikin murya irin ta yan maye fahad yace " kudaukeni kukaini ciki" Yadago musu hannayensa, ba musu suka rika hannayen suka dagashi sama suka sark'afahi suka nufi cikin gida dashi, A falo suka sami rumaisa tana bacci, duk da acikin maye yake amma hakan bai hanashi ganin rumaisa a kwanceba, yacewa bodyguard din "ita wannan metakeyi anan" dayan bodyguard din yace "bacci take oga" fahad yayi gyatsa kamar zaiyi amai sannan yace " bacci,,, bacci, ya fada cikin salon kasala, sai kuma yace "to kuma kuje kuyi bacci, ni kubarni anan nima anan zan yi bacci" sukace "toh oga" suka karasa dashi bakin kujera daya suka ajiyesa sannan suka fita suka wuce dakinsu, koba komai yau zasu Huta da tsaron wannan mashayin... Yadade a kwance kafin yayi yunkuri iya karfinsa sanna yasamu ya mike, tangadi yake sosai da kyar ya iya yakarasa gurin rumaisa, yayi gyatsa kamar zaiyi amai, Sautin gyatsar yaratsa kunnen rumaisa da sauri ta farka ta ganshi a kanta, yana mashalo, cike da zafin nama ta mike, edonta duk suncinciko da kwalla, tana kallonsa, wannan bazai taba shiryuwaba, a zuci tafad'a, duk ta firgita, yazu kam tsoron fahad take domin yazamo ibilis, mutum bayajin nasiha, fahad dake tangadi yace "zonan Rumaisa" rumaisa ta makale kafad'a tana shirin yin kuka, Fahad yace" bazaki zoba, toshikenan bara nazo ni" yayi taku daya zuwa biyu yana kokarin karasawa gurinta tangadi ya hanashi sandin cafet din yajasa yafadi rakwassss a gurin daidai dani table din da ke tsakiyar falon yafadi, dani table yarabu gida biyu, Rumaisa ta toshe bakinta takara tsorata ganin fahad kwance cikin glass, A hankali takira sunansa, taji shiru, dafe kai tayi ta rosa kuka tace na shiga ukku" Dasauri ta nufi hannyar fita domin yanzu ba bodyguard ko daya agurin, takara bakin gate tana kuka a lokacin mai gadi yafito, da fitila a hannunsa" hajiya lafiya, yana fada yana dalla mata fitilar Rumaisa tace " fahad zai mutu yana ciki" takarasa maganar tana kuka, Mai gadi ya tsorata sosai, dasauri yace " hajiya yana ina" rumaisa ta nuna masa kofar shiga falon " yana ciki" Mai gadin baijira takara magana ba ya zura da gudu yanufi cikin falo, harta daga kafa zata bisa, saikuma ta tsaya cak, zuciyarta na harbawa tara2, yau gata a bakin gate, kuma ita kadai, ai kuwa bazata watsar da wannan damar ba, dole tabar gidan da sauri takarasa wurin key din kofar tana kokarin budewa, cikin sa'a kuwa yabude, ta tura kofar tafita waje, unguwar shiru kake jinta, tsoro yakata jitakeyi kamar ta koma cikin gidan, wata zuciyar tace "ina ai komai tsoron da zataji gwara tatafi" tayi tsaye a bakin kofar tana kuka. tambayar kanta take, to ina kuwa zata je, kalaman mahaifinta ta tuna nacewa zai mata aure da faisal kotanaso kobataso, hakan yasa taji batason zuwan gidan, toh ina zataje, Kakarta tafadi mata a rai, mahaifiyar abba, gurinta zataje domin tana da tausayi sosai kuma tana son rumaisa, Tohm amma kuma ba'a garin takeba a sokoto take, taya za a yi tasamu motar sokoto a yanzu cikin daren nan, ta tsaya tana nazari... jin mai gadi yafito yana kiran hajiya! hajiya!! a cikin gidan ta kara firgita, mai gadine yana kokarin fitowa waje.. Rumaisa tace kafa menaci banbakiba, nan ta famtama da gudu tsiya tabar kofar gidan ta ratsa unguwar cikin duhun dare... Mai gadi na fitowa yaga babu hajiya, kuma kofar gidan a bude abin, yadafe kansa yafashe da kuka, domin yasan dacewa gudu tayi, yafito waje yaleka yaga babuta babu alamarta, kuka yafarayi.... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:45 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 55 and 56 Via *OHW* _A love story_💝 *NOTE* _ina mai baku hakuri, saida nayi typing ya goge hakan yasa nayi wannan a gurguje, sai kunyin hakurin ganin correcting mistakes, ngd_ "Nashiga uku, yanzu idan oga yatashi yasan dacewa hajiya ta gudu wlh zai iya illatani,wlh bazan zauna a gidan nan ba, dole inje innemota, idan kuwa ban sameta bazan dawo gidan nan ba" mai gadi yafada, Dasauri yashiga dakinsa yafara hada kayansa yana kuka, saida yagama hada kayan kaf sannan yafito, cike da tsoron kar wani yagansa, ya sulale yafita yabar gidan, Rumaisa kuwa sharara uban gudu kawai take, ita kanta batasan inda takeba, ballema harta samu hanyar zuwa sokoto, Daidai wani layi ta karyo kwana, karnuna na kwance a gurin sunaji gudun mutum, suka tashi suka fara haushi, a daidai kwanar tayi kicibus dasu, Cike da tsoro da fargita ta famtama ihu, daman dai tuncen rumaisa tsoron kare take, karnukan sukaji ihu ta, ai kuwa nan suka biyota, cab bata mayi guduba yanxu tafarashi domin wani masifaffen gudu danaga rumaisa nayi, nikaina banzaci zata iya yinsaba, gudu take tana kuka, Wani irin sabon karfi yazo mata, su rumaisa anga mutuwa... lol😝 Karnukan na biye da ita suna mata haushi, ita kuwa tana gudu tana kuka ratsa unguwar kawai take bata masan inda takeba, tana cikin gudun kawai jitayi tafada ciki wani rame fancamm!!! saida bakinta yadaki gabar ramen, bakin ya fashe da jini, duk jikinta ya goge, ta duke a kasan ramen tana maida nunfashi,ta toshe bakinta duk da zafin dayake mata amma a haka tadaure, saboda batason karnukan suji kukanta, Karnukan sukazo gurin sai haushi suke amma basu gantaba, suka yi tsaye a gurin suna sintiri, saida suka gama zagayensu sannan suka bar gurin, saida taji gurin yayi shiru sannan ta saki bakinta shanshekar kukanta kakeji sannu2, Sai a lokacin tasamu natsuwar duba ramen data fad'a, da kyal ta mike tsaye tana hawaye, duk jikinta ciwo, Irin ramun nanne na gefen titi, (lamba 2) tana daga kanta kuwa sai taga titi, wata irin ajiyar zuciya tayi tana nishi, Da gyar ta iya kama bakin ramen, tafito tahau titin tayi tsaye, tana kallon titin gefe da gefe, tsif kakejin tati babu ko motsin lade, a hankali tafara tafiya tana tangadi tare da hawaye, zafin ciwon yasakata kasayin kuka, ta dafe kafarta dai dai gurin dake mata ciwo, tadan jima tana tafiya kafin tafara jin kukan wani ubu a bayanta kamar motace ke shirin zuwa gurin, da sauri ta juyo, tana juyawa kuwa saitaga hasken fitilar mota, tayi tsaye a gurin ta d'aga hannu tana yiwa motar alamar ta tsaya, Motar bus ce taxi, tundaga nesa driver ya hangi mutum namasa hannu, hankalinsa yatashi duk jikinsa yadau

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37