Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Majnoon Book 1 Complete Hausa Novel 1,190 words 0 views Progress saved
Download Book

kuma jimamamin rashin lafiyar yaronsu, basason komai yasami fahad... ***** ***** ***** Wani irin katon falone, yasha ado da kamshin turare, wata dattijuwar mata mai kimanin shekaru 45 ce zaune tana kallon tv cikin nishadi da kwanciyar hankali, Zarah tafito daga cikin dakinta tayi shirinta nafita tana kamshin, fuskar nan tasha make-up tayi kyau abinta sai murmushi take, takarasa bakin kujerar da matar take zaune ta zauna kusa a ita tana murmushi, ummana kallo kike" Matar data kira da umma ta dubeta tana murmushi " ey, ina zuwa kuma haka aka chaba wannan adon haka" Zarah ta sunkuyar dakai, tana sosar kanta, kamar marar gaskiya "umma gidan su maryam zance kinsan yau ake bikin antyn ta " Umma tace " haka nefa, toh shikenan amma dai kirki dade a gidan domin kinsan halin mahaifinki baya son fitar nan dakike, idan yadawo bak'ya nan babu ruwana" Zarah tayi murmushi tace " insha Allah bazaima dawo ba yatarar bana nan, da wuri zan dawo, nidai zan tafi saina dawo" Harta mike zata tafi umma tace "zarah naga kwana biyunan kindaina fita aiki lafiya kuwa" Zarah tadan langwabe kai tana kallon umma tace "ummana banga ribar fita aikin nan ba domin kona fita bana samun natsuwar zuci, ummana kawai kitayani da adu'a Allah yasa na iya jure bakin cikin dazan shiga nan gaba" Umma ta dube tadan zare ido da mamaki " wane irin bakin ciki kuma 'yarnan, meke damun kine a gurin aikin" Zarah tayi murmushi a lokacin duk kwalla sun cika mata edo, tana sauri tabar gurin kar umma ta gane kuka take shirinyi tana fadan " saina dawo zan fada miki umma " dasauri ta fice daga falon tafita harabar gidan, Umma ta tabe baki "toh" sai kuma tayi shiru tana kallon kofar da zarah tafita, sannan tace " Allah yakauta, ina jiran dawowarki" ita kadai take maganar sai kuma tajuya taci gaba da kallonta, Zarah na fita hawaye suka sauko mata, dasauri tashige motar ta,ta daura kanta kansitari, tana hawaye, zuciyarta har wani zafi take mata, rashin faisal a gareta ba karamin tashin hankali bane, a duk lokacin da suka hada edo dashi wani irin sonsa yake kara shiga zuciyarta, saboda ta sami salamar zuci yasa tadaina zuwa gurin aikin domin tagaji da irin wulakanci da faisal kemata, amma duk da haka haryanzu zuciyarta cike take da kaunarsa, Sitarin motar ta daka tana hawaye sannan tadaki kirjinta daidai gurin zuciyarta tana fadan "laifin kine zuciyata, kece kika sakani komai, kece kika ingizani inda ake wulakantani, inda aka daukeni marar zuciya mai nacin soyayya... kuka takeyi cike da tausayi, cikin kukan take fadan "meyasa kika kamu dason maso wani, tabbas kuwa kin sakani a koshin walaha,..." kuka ya kubuce mata, takasa karasa maganar ta saukar dakai kan sitiri, ta jima a hakan kafin ta dago kanta, tatsayar da kukanta sannan tashare hawayenta, ta sai-sai ta kanta, ta kunna motar tayiwa mai gadi hoh ya wangele mata kofa sannan tafice tabar gidan... *Wacece zarah...* Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:45 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 61 and 62 Via *OHW* _A love story_💝 *Wacece zarah* Zarah heesham shine asalin sunananta, black beauty ce ga diri ga k'ira sonkowa kin wadda yarasa, Zarah ta kammala karatunta na degree yanzu haka tana aikine a wani company, a company ne suka hadu da faisal, tun farkon haduwarsu da ita tafara nuna masa so amma shi saiya rika basarwa, Hakan yasa tanace harsaida takai data furta masa, tun da ta furta masa cewa tana sonsa kuwa a take a gurin ya yi watsi da maganar tare da dayima wulakanci, ko da gargadin cewa karta kara bijiro masa da irin wannan maganar, Amma duk da haka zarah bata daina binsa ba tanayi masa magiya akan yakarbi soyayyarta amma faisal yaki, kullum wulakancinsa kara karuwa yakee. Zarah tayi masa kuka har ba iyaka amma kwata2 yakiji tausayinta, shi ace warsa baya kaunarta, shi bata yimasa baki daya, duk wulakanci na duniya faisal yayiwa zarah akan yaga yacire mata sonsa a cikin zuciyarta amma ina yakasa...hakadai zarah taketa hakuri dashi, tana kara lallashin zuciyarta akan ta dage wata rana zatayi nasara akansa, ( wace rana ce wannan ) oho Iyayen zarah ma'aikatan kwainatine, mahaifinta da mahaifiyar duk aiki suke, mamarta doc ce, mahaifinta kuwa librarian ne a wata university, Su biyune a gurin iyayensu daga ita sai kanwanta Nafisat wacca suke kira da feena... _Wannan kenan_ ***** ***** ****** Haj lubace zaune a daki tasaka rumaisa gaba tana tambayarta akan tagaya mata yadda wannan abin yafaru kuma ta sanar da itada meye silar faruwarsa, rumaisa kuwa bayan kuka babu abinda take, hajja luba tace "to nidai nagaji da wannan kukan naki, tunda bazaki fadamunba, ni zan koma waje idan kingama kukanki saiki kirani kisanar dani" tana gama fada ta mike tsaye, Rumaisa tayi saurin riko hannunta, tana shanshekar kuka tace "zan fada, dan Allah kizauna wlh zanfada " Haj luba tayi ajiyar zuciya sannna ta zaune tace "fadamun ina jinki, meye silal faruwar komai" ta fada ta kallon rumaisa edo cikin edo, Muryar rumaisa na rawa tafara fadawa hajja luba, komai daya faru, harda dukan da abbanta yamata akan saita aure faisal, tun bata karasa gayawa hajja luba, Hajja luba ta dakatar da ita, zuciyarta tadau zafi zanta yabace sosai cike da masifa take fadan "shi Usman (abban rumaisa) shine zai miki auren dole, harda duka, wato kenan badan Allah yasa kinzo nanba , dasaidai kawai naji auranki daga sama, to wlh bai isaba, yadda yake nuna ikonsa akanki nima haka inada iko akansan domin nice na haifesa, hajja luba tayi shiru tana huci, sannan ta kara kallon rumaisa tace "kikace kinada wadda kikeso koh" Rumaisa tace "eh inada" Haj luba tace "ya sunansa kuma d'an gidan waye" gab rumaisa ya tsinke yafadi, domin acikin labarin data bawa hajja luba bata sanar da ita cewa mahaukaci take soba, rumaisa tayi shiru tana kallon hajja luba, batasan sunan majnoon ba ballema hartasan sunan iyayensa, a wane gari yake oho, itama bata saniba, tsoro takeji karta fadawa hajja luba cewa wadda yakeso mahaukacine ne, domin tasan dacewa, zata dauki maganar tata ashirmen banza, Tayi shiru hajja luba ta tsureta da edo, bakinta na rawa ta soma furta " bansan..." Hajja luba ta dakatar da ita domin duk zuciyarta tadau zafi, wani irin haushin abban rumaisa takeji, tace " bana mason kifadamun sunansa ko sunan iyayensa, wlh babu makawa shizaki aura kuma nayi miki alkawarin indai ba mutuwa nayiba saikin auresa" sai kuma ta koma fada " maganar banza maganar wofi yanzu ai zamani ya chanza andaina yiwa mata auren dole, 'yar jikan tawa kwaya daya tak, za'a nemi amata auren dole salon idan aka kaita gidan mijin bakin ciki yanemi kasheta, toh bai isaba wollah" Rumaisa tayi shiru sauraronta kawai take, tasoma ganin nasara acikin lamarinta da majnoon, amma saidai tana fargabar ya Hajja luba zata dauki abin idan har taji labarin cewa mahaukaci takeso" Dafa kafadunta Hajja luba tayi hakan yayi sanadiyar fitowarta daga duniyar tunanin data shiga Hajja luba ta dubeta tace "kitashi kije kiyi wanka, kizo kici abinci, insha Allah gobe zamu koma abuja, kuma ina mai tabbatar miki dacewa zaki aure wadda kikso" Rumaisa ta rungumeta

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37