Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 29

Chapter 29

Majnoon Book 1 Complete Hausa Novel 1,195 words 0 views Progress saved
Download Book

su biyu da sukayi jugum, falon yayi tsit, shanshekar kukan rumaisa kawai kakeji, suna jiran dawowar su abba, Ji sukayi anturo kofar falon anshigo, dasauri suka maki ganin su abba sunshigo, Haj luba tayi saurin kallon abba tace " ina fatandai komai lafiya" abba jiki a sanyaye yace " kuzauna zan muku bayani" tunda suka shigo, edon rumaisa yana kan Mubarak, taga yanayinsa ya chanza, kuma sannan ko kallonta baiba, Bayan sun zazzauna abba yace "lamari ya lalace, domin abinda kowa yayiwa gudu yafaru, kabir yatuna da waye shi" Umma, haj luba, rumaisa duk saida gabasu yafadi, Cike da fargaba haj luba tace "abinda najima ina tsoro kenan yanzu gashi yafaru, to meya sanar daku" Abba yace "yace mana sunansa Mubarak kuma shi dan sarkin kogi ne sannan kuma yace yanada mata harda yaro daya" Ihu kad'an rumaisa tayi saida tasoma ganin jiri, zuciyarta ta harba da karfi, tafashe da kuka, Haj luba ta tabe baki tace " ahaf ai saida nagaya muku, amma kukaki saurarona, kaidai burinka 'yarka tasamu lafiya, wlh usman kacika sonkai dayawa" tafada tana nuna abba, Daddy yayi saurin cewa "hajiya ayi hakuri yanzu dai komai yafaru yariga ya wuce, maganar auren Rumaisa yanzu babu ta, da kyar ma muka samu yazo gidan nan domin yayi bankwana da ita, yamatsa akan cewa dole yanzu zai koma gida" Kuka sosai rumaisa takeyi, ta dago kanta muryata na sharkewa ta dube majnoon dinta wanda yanzu yazamo cikakkan mutum kuma ayanzu zata rasashi tace "nice silar duk wannan, daya faru kaka, kidaina ganin laifin abbana, nataka SO a gefe mai tsini tayadda edanuna suka rufe akan cewa saina aure Kabir, ninasan dacewa wannan bakomai bane face KADDARA TACE, kuma.ban isa na guje mataba...." kuka ya hanata karasa maganar, Sai a lokacin Mubarak yadubeta, tayi matukar bashi tausayi, shima hawayen yake yace "bazan iya auren ko wace 'ya macceba a yanzu, kiyi hkuri, koda ace an daura auren nan ne kafin nasamu lafiya to tabbas idan na warke zan tarwatsa auren, ki godewa Allah ba' a daura auren nanba" Kuka sosai rumaisa takeyi, dasauri tatashi tanufi dakinta da gudu, kawayenta sukabi bayanta, Mubarak ya dube abba yace "nagode da karamcin da kuka yimun, Allah yasaka muku da khairan" Duk falon suka amsa da ameen, Mubarak ya mike tsaye sannan yace " nizan wuce, sai Allah yasake sadamu da alkhairinsa" sannan yajuyo yadube faisal yace "muje koh" Faisal ya mike cike da farinciki, jiyakeyi kamar, burinsa nadaf da ciki, na auren rumaisa, Suka fita tare suduka, daddy yabasu motarshi, suka shiga, sannan sukayi sallama dasu Rumaisa tana tsaye ta Window tana kallon lokacin da Mubarak yashiga motar, jiri taji yafara dibanta, edonta suka fara lunshewa, daidai lokacin da su Faisal suka fita daga harabar gidan, a daidai lokacin rumaisa ta zube kasa somammiya.. Kawayenta sukayo kanta suna jinjigata amma ina, bata mosti, dasauri leemart tafita taje takira abba, yana shigowa dakin yakira doctor, Bayan sun yayyafa mata ruwa ta farka tana kuka, Umma tana rike da ita tana hawaye, ta dube ta "yanzu shikenan umma an rabani da majnoon, wlh umma zan mutu, majnoon shine burina, dan umma kuce yadawo" Hawaye umma takeyi, tace "kintaba ganin anmutu an dawo, to hakama Mubarak bazai taba dawowa garekiba, kedai kawai kiyita rokin Allah yabaki wanda yafishi" Rumaisa takara fashewara da kuka tana fadan "babu shi umma babu wanda yafimun majnoon a cikin zuciyata,,, kutai makamun kuce yadawo,. Wlh zan mutu 😭.." nan dai taci gaba da sabbato sai kace wata zararriya, Likita nazowa ya burma mata allurar bacci, sannan yasamu yaduba, sannan ya tabbatarwa su abba dacewa, jininta yana gaf da hayewa dan haka ayi gaggawar nema mata farin ciki, yana gama basu bayani sannan yafice yabar gidan, □□□□ □□□□ □□□□ Su faisal kuwa sai tsala uban gudu sukeyi akan titi kamar zasu bar duniya , amma duk da haka shi Mubarak gani yake kamar ba gudu ne Faisal keyiba , Anan daf da kiran sallar la'asar suka karasa garin kogi, faisal ya zarce sai gidan mai martaba, Bayan sun karasa Mubarak kallon gidan yake duk yaga gidan yasauya masa, a harabar gidan faisal yaja birki, babu kowa a gurin, duk suna wurin sallah, Cike da kasaita da faduwar gaba, Mubarak yafito daga cikin motar, yana kallon harabar giadan ba kowa da saurin yake tafiya yanufi cikin gidan batare dawata ko wani yaganshiba, faisal yana bayansa harya karasa falon da ummansa take ciki, yana bude kofar yaji gabnsa yafadi, Kallo daya yamata saiga hawaye, cikin kuka bakinsa ya furta Umma!!!" Saida kanta yasara a lokacin dataji muryasa, duk ila hirin jikinta yadau rawa, jitakeyi kamar almarane, bada gaske bane muryasa, a hankali kanta ke juyawa gurin dataji sautin muryar nafitowa, Caraf edonta yafada kan Mubarak, a lokacin mubarak ya zuro da gudu ( kusa masa slow gurin karatun, yanayin gudun sa😫) Kukan farin ciki take duk dacewa har yanzu bata gasgata lamarinaba, yunkurin tashi tayi sai kuma takasa hannu ta nuna masa bakinta na rawa tasoma furta mu..baa..rakkk" bata karasaba ta sulale kasa somammiya, Da gudu yakaraso gurinta ya tallabo kanta yana kuka, yana kiran sunanta "ummaaaaaa.... https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr [10/20, 10:53 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 109 and 110 Via *OHW* _A love story_💝 Faisal dake tsaye a gefe abin tausayi yabasa sosai harda su hawaye, Motsin mutane faisal yaji suna shirin shigowa gurin, Dasauri yakarasa gurin, Mubarak cike da tsro yake cewa " mutanefa suna zuwa, kazo mubar gurinnann" Ko kallonsa Mubarak baiba, kukansa kawai yaci gaba dayi, Bodyguard ne su biyu suka shigo wurin, ganin mutane aciki, yasa sukayi saurin karasa cikin cike da zafin rai, Faisal tuni jikinsa yadaurawa, Mubarak ya juya musu baya, tayadda bazasuga fuskarsa saba, bayan sun karasa kusa da mubarak daya daga cikin bodyguard din yadaka masa tsawa " waye kai!!" Mubarak yayi shiru, yaci gaba da kukansa, bodyguard din yakara daka masa tsawa yana kokarin kai masa duka, Cikin zafin zuciya Mubarak ya juyo da karfi, Sukayi edo hudu da bodyguard din saida yaja da baya saboda tsoro, cikin rawar murya bakinsa ke furta "prince Mubarak! !" Da gudu yajuya yafita waje, dayanma yabi bayansa suka fita, □□□□ □□□□ □□□□ Daidai lokacin mai martaba yafito daga masallaci, yana kokarin saka takalmansa, bodyguard din suka karaso gurin suna hucin gajiya, da gudun da sukayi, d'ayan yana nuna kofar shiga cikin gidan bakinsa na kokarin furta " prince Mubarak a dakin ummansa" Gaban mai martaba yafadi, cike da razana yace " yarima Mubarak a ina" Saida bodyguard din yasamu natsuwa sannan yace "dakin ummansa " Mai martaba ya daukesa da wawan mari cikin zafin rai yace "kaba ganin wanda yamutu yadawo, d'ana Mubarak ya mutu, tsawon shekara biyu, shine yanzu zakacemun kaganshi" Bodyguard din yana dafe da kumatunsa yace "wlh idan karya nake karka barni nakara nunfashi a duniya, prince Mubarak yana cikin gidan nan" Jin rantsuwarsa yasa gaban mai martaba yakara faduwan, kasa saka takalmin yayi, saboda zumudi, yanufi cikin gidan, kamar zai hada da gudu wurin saurin tafiya, Harya karasa bakin kofar falon, a daidai lokacin Mubarak yatashi yana kokarin fitowa , sukayi kicibus da mai martaba, Saranda mai martaba yayi yana kallonsa, ayya kuwa wannan ba mafarki nakeyi bane, ko kumadai fatalwarsace, Kafin zuciyarsa tagama saka2, Mubarak

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37