Chapter 32
Chapter 32
dakai cewa, karku fasa daurin auren nan, inason a daura auren nan a yau bayan angama sallar isha, sannann kuma kai kaneson kawakilci yarona Mubarak, daga baya koda zuwa jibine zaizo yadauki matarsa" Bakaramin dadi daddy yajiba , yayiwa sarki godiya soaai sannan suka katse wayar, Faisal dake zaune jigum, yayi tagumi, azuci yake fadan "nikam dai banda sa'a, a kullum sainaga samu saikuma naga rashi, shikenan na rasa rumaisa, 😰) □□□□ □□□□ □□□□ Cike dajindadi daddy yashiga mota yaje gidan abba yasanar dashi komai da mai martaba yace asanar masa, shima yayi na'am da wannan abin, kuma ya amince da a daura auren rumaisa da Mubarak bayan sallar isha, Goron da suka saya kawai sukaje suka dauka, sukayi alwala suka nufi masallaci, Sukayi salla isha bayan angama, tun ba'a fara fitaba, abba yakarasa gurin liman, yasanar dashi cewa yanason ayi daurin auren 'yarsa a yanzu, lamarin ya girguza liman dakuma mutane dake cikin masallacin, sunyi mamakin yin daurin aure cikin dare, Haka dai aka rabawa mutane goro bayan angama daura auren yarima Mubarak da Rumaisa, ( saidai kawai muyi musu fatan Allah yabasu zaman lafiya) Sannan kowa ya watse, abba yakoma gida cike da farin ciki, yagawa umma da haj luba, komai dake faruwa suma sunyi farinciki soaai, abba yanemi alfarma a gurinsu cewa karsu fadawa rumaisa komai dake faruwa, subarta kawai ayi mata AUREN BAZATA,, Rumaisa na dakinsa sai faman kuka take, jitakeyi kamarma yau dinnance ranar mutuwarta, saboda ita yanzu jitayi kamar batada sauran wani amfani a duniya yanzu tunda aka rabata da Majnoon dinta.. ( amarya rumaisa ansha kuka ) Wazai iya zuwa yafadawa rumaisa cewa, tafa zama amarya yakamata yadaina kuka😜😜 https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr [10/20, 10:54 PM] +234 905 395 7618: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 117 and 118 Via *OHW* _A love story_💝 _Bayan kwana biyu_ *KOGI* Umman Mubarak tasamu lfy sosai, domin yanzu dakowama zata iyi yin fira, ta warke sumul tadawo kan karagarta ta sarauniyar kogi, Mubarak mahaka shima yasamu sauki, amma haryanzu zuciyarsa tana cike da zogi da radadin rashin matarsa da kuma yaronsa, Yan kwana biyun nan duk ya kauracewa mutane, bayason zama cikin mutane yafison zama shikadai, Yauma kamar kullum yana zaune ciki dakinsa yayi jugum yana tunani ya game hannayensa akan kirkijinsa yana kallon saman dakin, shima bashida labarin aurensa da rumaisa, Mai martaba da ummansa suka turo kofar dakin suka shigo, suna murmushi, Mubarak yabisu da kallo har suka karaso kusa dashi suka zauna, Mai martaba yadafashi yana kallonsa yace "Mubarak komai daya faru dakai mukaddarine daga Allah, mutum bai isa ya gujewa kaddarar saba, yakamata ace kayi imani da kaddara, anason kowanne musulmi yayi imani da kaddara ta alkhairi ce kota shairi, karfa kakasacin jarabawar da Allah yake maka" Hawaye suka soma sauka kan kumatun Mubarak, zaiyi magana kuka yakubuce masa yasoke kansa cikin kirjin mai martaba yana kuka yace "kashe sufa akayi, kuma KISAN GILLA, kisan rashin imani, mesukayi masa, meyarona yamasa, yaro karami dan shekara daya, haba wannan rashin imanin yayi yawa ..." yakarasa maganar yana kuka, Mai martaba yarika shafar Bayansa a hankali, sannan yasauke nunfashi yace "kayi hakuri komai mai wucewa ne, kadaina kuka" Umma tayi ajiyar zuciya sannan tace "kadaina kukan nan mana Mubarak, mamaci adu'a yakeso ba kukaba" Sai lokacin aka samu yadan sassauta kukansa yafitar dakansa daga cikin kirjin mai martaba yashare hawayesa sannan yace " insha Allah umma daga yau nadaina kukan nan zanci gaba da rayuwa kamar yadda kowa yakeyi" Murmushi mai martaba yayi "haba kokaifa, ai hakan yafi" Suduka sukayi murmushi, sannan mai martaba yayi gyaran murya kafin yace " amm daman munzone musanar dakai, cewa yakamata kaje Abuja kazo da matarka, domun azo nan asha Biki" Gaban Mubarak yafadi cike da mamaki yake cewa "mata kuma abba yaushe akayi auren banace afasaba, nifa bana sonta" Umma tayi saurin cewa "to mudai ko baka sonta mun riga mun daura muku aure saidai kayi hkr, domin mu bazamu zamo butuluba, a yadda naji labari, yarinyar nan tayi maka taimako sosai a rayuwarka" Mubarak yafara gunguni, mai martaba yace "katashi kaje kayi wanka, kafin kafito zansa ashirya maka motoci, kaje kazo da matarka" Amma abba, nifa bana sont..." mai martaba yadaga masa hannu yadakatar dashi dacewa "indai kanason farin cikinmu, to katashi katafi, ta wannan hanyarne kadai zamu sakawa yarinyar nan aka abinda tamana akanka" yana gama maganar yamike yanufi hanyar fita, umma ta mara masa baya, atare suka fita, sukabar Mubarak zaune akan gado zuciyarsa cike da sake2, Har suka fita Mubarak kallon kofar yake, bayan sun fita yaja tsaki, sannan yatashi akasale "wannan wane irin AUREN BAZATA ne, aure babu ko soyayya" yafada yana kokarin shiga toilet yayi wanka, Bayan yafito yazo bakin mirrio yashafa mai, sannan yaje yadauko wasu hadandin kayan sarauta yasaka, bakaramin kyau yayiba, yafito yarimansa sak, yazo bakin mirror yana kallon kansan, sai kuma yayi murmushi, Wani irin farin ciki yakeje a yanzu bayan fitowarsa daga toilet wanda shikansa baisan da zuwansa ba, Tun a lokacin daya samu labarin matarsa da yaronsa sun mutu, baikara tsintar kansa cikin farin cikiba kamarna yanzu ba, Saida yafeshe jikinsa kaf da turare sannan yafita, koda yakarasa harabar gidan, Mai martaba yasa anjera masa motoci a kalla zasukai guda biyar, Yana zuwa yashiga mota ta tsakiya nan suka fita daga hatabar gidan suka hau hanya, mai martaba yayi musu fatan Allah yakai lafiya yadawo dasu lfy, Suna barin gidan, mai martaba yakira abban Rumaisa yasanar dashi cewa gasu Mubarak nan kanhanya, Abba rumaisa yayi farin ciki sosai, bayan sun katse wayar Sannan yaje yasanar da umma da haj luba, nan fa suka shiga gyaran gidan, rumaisa tana dakinta, cikin bakin ciki batasan irin wainar da ake toyawaba, Sai bayan sungama shirya gidan tsaf sannan umma taje dakin rumaisa, a kudundune tasameta gefen gado, kamar shege a gurin rabon gado, Umma tazauna kusa da ita, tafara yimata 'yan nasihohi akan tadauki kaddara akan abinda yafaru da ita, Nasihohin sun ratsa jikinta sosai, daga kashe dai umma tace "yanzu dai kitashi kije kiyi wanka domin zamuyi baki a gidan nan, kuma dan Allah karki nuna masu alamar kina cikin damuwa, kisaka fuskarki a murmushi kinji" Murmushi karfin hali Rumaisa tayi " tohm umma insha Allah zanyi kokarin yin hakan" Umma ta mike tana murmushi "tohm shikenan idan kin gama wanka kikirani nazo zabama miki irin kalar tufafin da zaki saka" Rumaisa tace " tohm" tana gama fada, umma tajuya tana kokarin barin dakin, Rumaisa ta kwalla mata kira , ta juyo , Rumaisa tace "umma halam bakin waye zasuzo" takarasa maganar tana Murmushi, itama dai fada mata din nan da akayi baki na nan zuwa, harta soma jin farin ciki, wanda batasan meye dalilin yinsaba, Umma tayi murmushi tace "bakin abban kine " tana gama fada ta fice tabar dakina, Rumaisa tatabe baki "bakin abba, daga ina kuma? " itaka kadai take magana, Murmushi kawai tayi sannan tafada toilet, Wanka tayi sosai domin tana wankan tanajin nishadi, kamar bata cikin wata damuwa, karasa wannan tafito, Bayan tafito harta zauna tana shirin fara mekup tatuna da umma tace takirata idan tafito, Tashi tayi ta janyo hijab tasaka, tana kokarin bude kofar, a daidai lokacin umma taturo kofar tashigo, tayi turus tana kallonta tana sosa kanta " amm daman
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37