Chapter 27
Chapter 27
sosai, saura mintuna kadan a fara daura aure, koshi dan daddy baya nan ne yatafi airport dauko faisal ... □□□□□ □□□□□ □□□□ *Airport* Jirgi yadira a airport dake abuja, cikin gaggawa su faisal suka fito, daman daddy yakaraso shima su yake jira duk ya kagu suzo, domin yaga lokaci yana tafiya, Tundaga nesa faisal ya hangi daddy, da sauri suka karaso gurinsa, faisal yayi hug dinsa cike da fara, "you're wll com my son" faisal yayi murmushi yace " thanks daddy, faisal ya nuna adnan dake tsaye a bayansa yace "daddy wannan aboki nane sunansa adnan" Cikin gaggawa daddy yace " oya let's go, daga baya idan an gama dauren auren mayi magana a gida, kushiga muje lokaci na tafiya" Nan suka shiga mota, daddy yajasu suka nufi gidan abba.. □□□□□ □□□□□ □□□□ Mutane sai kara taruwa suke, Abba yashiga cikin gida yafito da kabir ango, domin lokacin daure aure yakusa, Su daddy kawai ake jira, Rumaisa kuwa bayan fitowarta daga wanka, kawayenta suka fara shiryata, suka tsara mata kwalliya mai kyaun gaske, Sannan akaje ga sutura ananfa akasha rigima domin ko wacce aka dauko sai rumaisa tace ita bata yimata ba, itadai tafison a yau dinnan tafi kyau fiye da kowace rana, Da kyar dai aka samu tazabo kala daya, sannan tasaka, tabbas tayi kyau sosai kamar ba itaba, leemart tayi dariya tace " amarya ansha kamshi, kinyi kyau abinki" murmushi kawai rumaisa tayi, suka kwashe dadari, maryam tace " nimadai baza'a barni a bayaba, saina tsokano magana, amarya bakya laifi kokin kashe dan masu gida" su duka suka kwashi dariya harda rumaisa, haka dai sukaci gaba da zolayarta ita kuwa sai faman murmushi take musu.. (amaryar Majnoon😜 ) □□□□ □□□□ □□□□ Motar daddy ta ja parking a bakin kofar gidan abba, tun a lokacin adnan yakejin gabansa na faduwa, Daddy da faisal suka fito suka barshi a cikin motar yana tunani, harsun fara tafiya faisal yaduba yaga babu adnan da sauri yadawo bakin motar ya leka, yaganshi zaune yayi jugum, faisal yace "fito muje mana" Saida adnan ya dan zabura yace "to...to" sannan yafito suka nufi kofar shiga gidan, a lokacin har daddy yashige ciki, gaban adnan sai faduwa yake, Suka tura kofar gidan suka shigo, nan suka tarar da mutane zazzaune, sukayi tsaye suna kallonsu, faisal ya dube adnan yasauke murya yace "cab di jan, to yanzu taya za'ayi mufita da shi" Adnan yayi ajiyar zuciya yace " hmm nima ina nasani, niko ganinsama banyiba" Faisal yashiga leka taron yana fadin " bari na duboshi" nan ya d'aga yashiga neman Majnoon, yabar adnan tsaye a gurin, zuciyarsa sai saka masa take taya zai kashe majnoon batare da faisal yasaniba, haka dai yayita sake-sake.. yana neman mafita □□□□ □□□□□ □□□□ Kabir yana zaune akan kujera, kwata- Kwata yau bayajin nishadi, baisan komeye dalilin hakan ba, jin anfara adu'ar daurin aurensa, yasa yaji kansa yafara sarawa, nan take edonsa suka chanza launi zuwa ja, duk jikinsa yadau gumi, tashi yayi dasaurin yana kokarin komawa cikin gida, A daidai lokacin faisal ya hangesa, da sauri ya kad'a hannu yace " yes!! Nagansa" sannu yafada, sannan yakarasa gurinsa, Assslamu alaikum" ya tsayar da kabir tare da mika masa hannu sukayi masubaha, sannan kabir ya amsa masa, Yana murmushi yace " sunana faisal, amm munzo ne nida abokina domin mutayaka murnan aurenka, mubakine daga kogi state" Da karfi kabir ya zare edo, kwakwalwarsa tarika juyawa kamar zai iya tuna sunan, kamar yasan sunan, amma sai kuma yakasa tuna komai, Faisal yariko hannunsa yace" muje koh, Kabir yabishi da kallo, suka nufi kofar fita, Adnan dake tsaye a bakin kofa, tun daga nesa yake hangosu, Kallo daya yamasa yazare edo, duk jikinsa yadau rawa tabbas yaya Mubarak yana raye, mummunan tashin hankali ya ziyarci zuciyarsa, duk ya fita hayyacinsa, gumi yasoma karyo masa, Tafiya suke suna Magana ammashi bayajin abinda suke fada, tun daga nesa Faisal ya nunawa kabir, gurin da adnan yake yace " ga abokinan ce sunansa adnan" Da karfi kabir ya dago kansa ya dube gurin da faisal ke nuna masa , Tunda edon kabir suka fada kan adnan, yaji wani irin zirr kwakwalwarsa ta dauka; daga hannu yayi yadafe kansa saboda mummunan cewon dayake masa, yana kokarin nuna adnan, jiri yasoma dibarsa saboda zafin da kwakwalwarsa take masa, kad'an yayi ihu, a hanakali yake sulalewa kasa yafadi wanwar, Daddy dake zaune acikin taro, yana kallon duk abinda suke, amma shi bai lura da adnan ba,sulalewar Kabir kawai yagani, da karfi yace " innalillahi wa inna ilaihin raju un" nanfa kaga kallon kowa yadawo kansa ana tambayarsa lafiya, dasauri yamike yanufi gurin su kabir, mutane suka bishi da kallo, kabir yana kwance a kasa a some, faisal ya durkusa kusa dashi, yana girgiza shi, duk ya tsorata, yarasa meke faruwa, Daddy ya karasa kusa da faisal, Ganin halin da ake ciki yasa mutane suka yo kansu, sai salati ake, hakalin kowa yatashi, Cike da firgita adnan ya juya da gudu yafita yabar gidan, domin yasan dacewa yanzu kam komai yachabe, duk ya fita hayyacinsa, yana fita yayi daidai da wani mai napep yashigo layin da sauri yataresa , tare da umurtarsa daya kaisa airport, ba musu mai napep din ya tada napep suka wuce airport □□□□ □□□□ □□□□ Koda faisal yajuyo gefe adnan yaga wayam, babu adnan babu labarin, abin yakara daure masa kai, waishin meke faruwane, kodai hakan yana nufin cewa wannan shine yayan adnan, kansa yake tambaya, Daddy yasa aka kwashi Kabir akayi asibiti dashi, □□□□ □□□□ □□□□ Rumaisa tana cikin daki ita dasu leemart, suna tsokanarta, umma tazo tasanar da ita mummunan labari, bakaramar firgita tayiba, taso taje asibitin amma umma ta hanata domin tasan idan taje bayan kuka babu abinda zata musu, haka ta hakura tazauna gida... □□□□ □□□□ □□□□ Bayan ankarasa dashi asibiti likitoci suka karbesa suka bashi taimakon gaggawa, Cikin kakkanen lokaci suka gano matsalarsa, sun gano cewa babu abinda ke damunsa, sock ne kawai yadibesa, nan bada jimawaba insha Allah zai farka... □□□□ □□□□ □□□□ Yana karasa airport cike da firgita ya sallami mai napep ko chanji bai tsaya karb'a ba, yakara shiga jirgi, yakoman kogi, tun suna cikin jirgin yake kuka duk ya tsorata, Yau kam asirinsa ya tono, ya matsu bai karasa kogi ba yasanar da ummansa cewa tabbas Mubarak yana raye bada jimawaba kuwa suka karasa kogi.... Waya ganemun edon umma taji lbrn Mubarak yana raye😜 https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr [10/20, 10:52 PM] +234 905 395 7618: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 105 and 106 Via *OHW* _A love story_💝 Ana ajiyesa filin jirgi, Bai tsaya akazo daukar saba, taxi yashiga yakaraso gidan da shigowarsa cikin gidan yanufi sashen haj zainab cike da tashin hankali, Tun bai karasaba yake kiran sunanta, dasauri tafito daga dakinta tana murna a tunaninta sunyi nasarane akan Mubarak, Sunacin karo dashi taga yana kuka cike da firgita tace "adnan lafiya kuwa" Adnan yakara fashewa da kuka, yana fadan "umma yau zamu mutu, wlh yaya Mubarak yana raye kuma yana ganina yaganeni" Haj zainab ta toshe baki nta tana kokarin yin kuka tace "nashiga ukku" taja hannun adnan suka karasa cikin daki, tazaunar dashi kan gado, "kafadamun meke faruwane, garin yaya hakan tafaru" haj zainab tafada, takarasa maganar cikin hargowa Adnan yana kuka yafara labarta mata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37