Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 19

Chapter 19

Majnoon Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

da bayar da jini" murmushi kawai tamasa shima yamata sannan suka samu guri suka zauna suna jirana farkawar rumaisa, BAYAN AWA DAYA DA RABI Umma tana zaune kusa da rumaisa, rumaisa ta tafarka tana kallon dakin a hankali, Umma ta dubeta tace "sannu rumaisa ya jikin" bata iya cewa komaiba saikawai bin dakin take da kallo, A daidai lokacin abba da likita suka shigo dakin, abba yace "alhmdulillah ta farka" da sauri yakarasa gurinta ya fadan "ya jikin" suna hada edo da Abba rumaisa ta fashe da kuka mai sauti saida hankalin kowa a dakin yatashi, hajja luba takaraso ta rike mata hannuwa tana cewa "rumaisa kigaya mana menene damuwarki, meye matsalarki" Cikin kuka rumaisa tace "inna bazan iya sakaku kumin abinda baku soba, haka nima bazan iya hana zuciyata tunaniba, bazan taba samun salamar zuciba matukar bana tare da majnoon, ta dube abba sannan taci gaba dacewa "abba majnoon shine farin cikina shine kadai wadda nakeso Dan Allah abba kabarni naganshi koda saudayane...." takarasa maganar tana kuka sosai, Dakin yayi shiru nadan wani lokaci, Abba yashiga tunanin maganar rumaisa, tabbas 'yarsa ta susuce akan soyayya da majnoon Likita ya katse mata tunani dacewa " waye shi wannan majnoon din, daman tanada wadda takesone" abba yasauke a jiyar zuciya yace "eh tanada amma kuma ai mahaukacine, ni banga ribar auren mahaukaci ga mai hankaliba " Likita yace " idan har yana raye yakamata azo mata dashi, idan har kunason tasamu lafiya, yakamata ace kacece rayuwar 'yarka, ka ajiye maganar hauka gefe, domin hauka zata iya warkewa matukar ba mugun asiri akayi masaba, wasu iyayen suna bani mamaki, duk da sunsan matsalar yayansu kuma sunada maganinta amma saisu kafe da nuna iko da isa, wannan kwata2 bai daceba, nidai shawarata anan itace kanemawa 'yarka lafiya ka ajiye maganar hauka a gefe, ai ko mahaukaci mutumne" Abba yayi jim yana nazarin maganar sai cen yadube likita yace " yanzu kana ganin zai iya warkewa kuwa " likita yace " insha Allah zai warke, indai har ba asiri akayi masaba, kagama idan har kayi haka kasamu riba biyu kenan ga ribar taimako, kuma sannan kanemawa 'yarka wadda takeso" Abba yayi ajiyar xuciya yace "to shikenan zanje yanzu nazo dashi" yana gama fada yanufi hanyar fita Likita yiyi saurin cewa "yasan fuskar kane, domin kasan yadda suke, basa yadda da sabuwar fuska" Abba yadan tsaya kafin ya juyo ya dube likita sannan yace "eh yasan fuskana, domin nataba zuwa mukayi hatsaniya dashi sau daya" Likita yace "tare zamuje domin banason yaganka yafirgita " abba yace to shikenan muje, Tare suka fita Nan suka fita sukabar asibitin sukanufi unguwra da majnoon yake, Suna zuwa kuwa suka ganshi kwance yana bacci duk ya kara hargisewa, jikinsa har wani tsamin datti yake, likitan yatoshe hancinsa, sannan suka suka karasa gurinsa, Abban rumaisa yadan dakeshi kadan, ai kuwa da karfi yafarka, Cike da firgita suka hada edo da abban rumaisa, da karfi yatashi yana ja dabaya, Abban rumaisa yace "tsaya kaji munzone mutafi dakai asibiti" Majnoon yanajin zancen munzone mutafi dakai, ya zura da gudu, abban rumaisa da likita suka mara masa baya suna kiransa amma ko juyosu baiba, Kan titi yahaura babu ko duban motocin dake zuwa , ai kuwa yana kai tsakiyar titi, naji abba na fadan katsaya mota ga banka, kafin majnoon ya ankara kaji wani karrrrrrrrrrrr...... Note" Aslm, ina mai baku hkr akn gaskiya bazaku jini kwana biyu ba domin banada lfy kuma gobe zamu fara exam, nagode da nuna kaunarku akan novel dinnan" Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:46 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 79 and 80 Via *OHW* _A love story_💝 Abba yadan zabura kadan dominshi harya shiga duniyar tunani, gyaran murya yayi sannna yafara dacewa "bansan yadda zakaji maganarba, amma yazama dole ingayamaka ita, soboda koda ban sanar dakai ita yauba to tabbas gobe ko jibi zan sanar dakai komai, wannan daka tambayeni waye shi, nikaina bansan waye shiba, kaddarace ta had'ashi da rumaisa, kuma shi mahaukaci ne, tayi mugun kamuwa da sonsa, nayi kokarin naraba dashi amma nakarasa yin haka, sanadin hakan yasa kaga komai yana faruwa ba daidaiba, kamar yadda nasanar dakai a waya cewa muna asibiti, jiyane bayan faisal yabar gidana, rumaisa tashigo gidan a hasgitse, ina zaune a falo naga shigowarta, nake tambayarsa meya faru amma tagagara mun magana, abin ya tsoratani, shine nabi bayansta tana karasa dakinta tafadi kasa a cikin dakin nan fa saita fara aman jini... abba yayi shiru yana kokarin goge wasu gajerun hawaye dake kokarin saukowa kan kuma tunsa, Daddy yayi saurin cewa "subhanallah" sai kuma yayi shiru Abba yayi ajiyar zuciya sannan yaci gaba dacewa "to shine muka kawota asibiti, bayan mun kawota asibiti, likita yake sanar damu cewa tana daf da kuma da cutar hawan jini matukar bamu nema mata abinda take soba domin tunani da damuwa sun mata yawa, shine bayan ta farka aka tambayeta meye matsalarta anan take sanar damu cewa ita mahaukacin nan takeso, naso nadauki maganar tata a shirme amma Likita yace bai dace nakasa ceton rayuwar 'yataba akan wani banza kudiri nawa, Likitan ne yabada tabbacin cewa zai iya warkar da mahaukaci matukar ba asiri akayi masa ba, nikuwa shine nabi shawararsa mukaje aka daukosa, a garin daukosa kuma mota takara kadesa, yanzu haka likita yasanar dani cewa bayan cutar hauka dake jikinsa, kwakwalwarsa tayi losing wasu abubuwa wadanda koda yasamo lafiya bazai iya tunawaba, abba yadan shiru yana share hawayen dake zubo masa, jikin daddy duk yayi sanyi tausayin majnoon yaji sosai aransa, bayan abba yashare hawayensa yaci gaba dacewa "alhj kayi hakuri, kuma kabawa yaronka hakuri akan maganar aurensa da rumaisa, domin bazan zamo mai sonkaiba akan abinda 'yata kesoba, ni a yanzu farin cikinta kawai nake nema" Daddy yayi yasauke nunfashi edonsa sunyi ja sosai, shima shirin yin hawayen yake, sai dai yadanne aransa, domin tunba yauba yaso faisal yadaina zancen auren rumaisa amma yaki, to yanzu dai komai yazo karshe, daddy yace "alhj bazan taba kamaka da laifi ko cin amanaba domin wannan hukuncin daka yanke ko nine hakan zanyi, fiyema da hakan zan iyayi domin kawai in nemawa yarona farin ciki, amma wannan shawarar daka yanke itace mafita mai kyau, mukanmu munsan dacewa rumaisa batason faisal, saidai munyi amfani da ikon mune na zama iyayenta zamu aura mata shi a dole, gaskiya bazanga laifin kaba, kuma najidadi sosai daka taimakawa yaron nan Allah yasaka maka da khairan" Murya a sanyaye abba yace "ameen" Sai kuma sukanyi shiru, kamar kurame saicen daddy yace "saidai wani hanzari ba guduba, abba yayi saurin dago kansa yana kallonsa "menene " Daddy yace "sai dai akwai matsala daya, matsalar kuwa itace manta komai dayayi, domin zai iya tunawa da komai aduk lokacin dayaga abinda yataba faruwa dashi abaya, to idan yatuna ya kake ganin kenan zakayi idan yakasa amincewa da auren rumaisa, kokuwa yagudu yabarku" Abba yadanyi shiru kamar bazaiyi magana, sai cen kuma yace "idan ma hakan zata faru tosaidai a bayan auren su, domin ana sallamarmu a asitibin nan zan fara shirye 2 aurensu, kaga kenan idan daga baya yatuna zuwa lokacin zai iya kasancewa sun samu haihuwa ita dashi, kaga kuwa bazai iya guduwaba yabar iyalansaba" Daddy ya girgiza kai yace "

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37