Chapter 17
Chapter 17
wadda yasaceni, akan yana sona" tana karasa fadan maganar ta sunkuye kai, Falomln gabaki daya kowa yacika da mamaki, hajja luba ranta a bace tace " wannan ai haukane mugun mutum kamar wannan yashigo gidan nan shine bazaki fadaba, meyasa baki gaya mana tun farko shi bane da basai asaka police sukamshiba" Abban rumaisa yayi saurin cewa "hajiya amma dai bakisan kowauye alhj sani babba bako, ai wannan dakike gani duk kasar nan babu wadda ya isa yakamashi, saidai kawai muyi hakuri tunda Allah yasa rumaisa tadawo lafiya lau, mugodewa Allah" hajja luba tayi ajiyar zuciya sannan tace "toh shikenan, sai kuma ta dube umma tadan tabe baki kafin tace " ke kuma wlh nasake jin wani tashin hankali yashiga tsakaninki da rumaisa to ina mai tabbatar miki dacewa zamanki a gidan nan yazo karshe" umma tadan share hawaye, domin yanzu nadamce karara a kan fuskarta tace "insha allah babu abinda zai sake faruwa" tana gama maganar tayi shiru, Hajja luba ta dube abba tace "kai ma ina kara fad'a maka cewa karka kara dukanta kuma karika mata abinda takeso, yarinya karama saiku nemi kusa mata hawan jini" Abba yayi yake yace "insha Allah hajiya babu wata takura dazata sake shiga tsakanina da rumaisa, yanzu haka sonake tafadamum wata keso, duk wadda takeso to shi zan aura mata, abba yadube rumaisa kafin yace " rumaisa wa kikeso?" Yana tambayar rumaisa, Gaban rumaisa ya fad'i, ta dago edon tana kallonsu, tanajin yadda zata fadamusu cewa majnoon takeso, jin tayi shiru yasa hajja luba tace " kifada mana wakikeso" Rumaisa tayi rau rau da edo kamar zatayi kuka, muryarta na rawa ta soma furta " majnoon, abba majnoon nakeso" tana karasa maganar tasoke kanta kasa, Tunda tafadi kalmar majnoon abba yashiga tashin hankali, yafara tunano abinda yafaru kwanakin baya, Hajja luba kuwa mamaki yacika kasa hakura tayi saida tayi magana "majnoon fa kikace, mahaukaci kenan" Abban yayi saurin cewa "eh hajiya wani mahaukacine takeso, nayi kokarin rabata dashi amma taki rabuwa dashi" hajja luba tamike tsaye cike da masifa tace " wannan ai haukane, niko a tarihi bantabajin mai hankali yaso mahaukaci ba, nima ban goyi bayan a aura miki mahaukaci ba domin wata rana zai iya illataki, meye abinso a cikin mahaukaci mtsw, ni wlh nayi tunanin kinada hankali ashe ke baki hankali ko kadan" takarasa maganar tare dajan tsaki, Abba ya girgiza kai yana kallon hajja luba yace "kemadai kya fada, meye abinso a gurin mahaukaci, amma babu yadda zanyi tunda kince abata wadda takeso, dan haka shi a aura mata kawai" Hajja luba tace "ai ko bayan raina bazata auresaba, ni wlh dama nasan akan mahaukaci kike wannna kurciyar da wlh bakisa nabaro sokoto nazo nanba" Tunda suka fara maganar rumaisa tasoma kuka, hajja luba taci gaba da zabga mata fada, kamar ta daketa, taga rashin hankalin na rumaisa yayi yawa, daga karshe tace "wannan duk kurciyace, dan haka idanma kinada wanda kikeso kifito dashi amma ba mahaukaci ba, idan kuwa bakida kijira zuwansa amma bazamu aurar dake ga mahaukaci ba" tana gama maganar ta dube abba tace "tashi muje kamaidani sokoto, domin ni bazan zauna ina sauraron wannan tatsuniyarba, sanna tasake duban rumaisa tace "ke kuwa idan kika tanace akan cewa sai mahaukaci, to bani bake, karki kara daukata a matsayin kakarki" takarasa maganar tana huci tanufi kofar fita, rumaisa tayi saurin mikewa cike da tashin hankali tashiga gabanta ta durkusa a gabanta tana kuka ta rike mata hijjab " inna dan Allah kiyi hakuri akan abinda nafada, wlh na hakura dashi, zan iya barinsa amma ke bazan iya jurar ganin fushinkiba, saidai inna dan Allah kitayani da adu'a Allah yasa kar ciwon zuciya ya illatani" Tausayi tabawa hajja luba sosai, duk yadda taso tayi fushi da rumaisa bazata iyaba, idanhar tatuna irin hallacci da mahaifiyarta tamata, hajja luba tasa hannu ta dagota suna facing din juna sannan tace "na hakura rumaisa, kuma insha Allah ciwon zuciya bazai illatakiba, zaki dawo sumul kamar kowa zaki manta dashi a rawuyawaki" rumaisa tana kuka ta rungume hajja luba, hajja luba tarika suka wuce daki, akabar daga umma sai abba a falo, Abban yadube ya tsuke fuska yace "kitashi kigirka mana abinci" Umma ta girgiza kai kawai ta wuce kicin... ***** ***** *** Abban fahad kuwa tun a mota yaci fadansa mai isarsa, har suka karasa gida a faloma yakara dora wani fadan yana cewa "bazan barka a kasar nan ba, akan macce dukkabi ka susutaminkai, yau zamubar kasar nan tare dakai, yadube umman fahad yace " tashi maza ki had'o masa kayasan muwuce dashi" Umma tace " hakan ma yafi muje dashi cen yana gabanmu" haka kuwa akayi umma taje tahada masa kayansa, suka fita suka nufi airport, Fahad banda kuka babu abinda yake, duk yarasama mezai musu, duk da dai shima yanason tafiyar, domin yanason yamanta da rumaisa a yanzu, matukar yana ganinta bazai taba daina sontaba, Hakadai suka shiga jirgi sukabar 9ja, suka lula zuwa American... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:46 PM] +234 905 395 7618: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 71 and 72 Via *OHW* _A love story_💝 Ummanta nazaune a falon taga ta fad'I cike da firgita ta karaso gurinta, tana jinjigata, tana kiran sunanta amma taji shiru, daman umma likitace, da sauri ta dube feena, wacca tuni tafara tana fadan wayoo anty zarah tamutu, umma tadaka mata tsawa tace "jeki daukomin ruwa a firij" Dasauri feena ta mike jikinta na rawa, taje tadauko ruwa tadawo, umma ta karba ta kwara mata, Firgit tafarka tana kuka, ta kakkame umma, umma tace "lafiya kuwa meyake faruwa ne" Zarah kuka take sosai da kyar da iya fadan "ammi dan Allah achanzamun gurin aiki, wlh matukar ina gurin aikin nan bazan taba samun kwanciyar hankaliba, zuciyata zata iya fashewa" Ammi ta sauke nunfashi tace "toh shikenan daman tun shekarar jiya da damukayi magana dake nakira abbanki na sanar dashi komai, kuma yace insha Allah za'a nema miki wani gun, ki kwantar da hankalinki, tashi muje nakaiki dakin ki kwanta" Nan zarah tamike ammi tarika sukabar falon suka nufi dakin zarah, a dakinta ammi takaita saman gado ta ajiyeta sannan tafice tabar dakin, Bayan fitar ammi kuka sosai zarah tayi, tare da yiwa zuciyarta alkawari cewa koda son faisal zai kasheta to dole zataja baya2 da lamarinsa domin yanzu yasamu wadda yakeso, bazataso shi ya shiga irin halin da ita take ciki ba'ayanzu, Haka dai taci kukanta mai isarta, hadisin annabi Muhammad S A W ta tuna inda yake cewa "kugusar da damuwarku dayin sadaka, Allah subhanahu wata'ala zai yaye muku damuwarku kuma ya doraku akan makiyanku" wannan ta ajiye aranta, takira feena tazo tabata kudi tace taje masallacin bakin layi takai musu tace sadakace, haka kuwa akayi feena taje takai kudin ta dawo..... A hankali tasoma samun natsuwar zuci, harda bacci yayi awon gaba da ita, *Bayan kwana biyu* Rumaisa tadan warware amma haryanzu takasa sakin jiki, akoda yaushe tunanin majnoon take, tama daina fitowa falo, kulum tana cikin daki saikace wata amaryar kulle, Batada aiki sai tunina sai kuma kuka idan taga babu kowa a kusa da ita, Yauma kamar kullum tana cikin daki zaune, abbanta yashigo, yana murmushi yazauna kusa da ita ya dube yace "rumaisa!!" Ya kira sunanta tadago kanta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37