Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Majnoon Book 1 Complete Hausa Novel 1,194 words 0 views Progress saved
Download Book

lura da jinin dake fita a kafarsa, Tace "subhanallah, jin ciwo kayine" ya girgiza mata kai, Oh sorry" tafada tana kokarin taba masa kafa, da sauri ya janye yana kallonta yace "babu kyau macce tataba kafar daba ta mijintaba" Rumaisa ta kallesa tayi murmushin tajidadin maganar har cikin ranta tace "babu shamaki gaduk wadda zai tamakawa musulmi dan uwansa a duk lokacin da yake cikin neman taimako, dan haka idan har taimakonka zanyi babu laifi idan natabaka" Fahad yayi dariya yace "ok shikenan" ya miko mata kafar ta kama ta matse jinin daya taru a ciki sannan tamike taje toilet ta dibo ruwam zafi a heater tazo tana gasa masa kafarshi, tana dan kara yimasa bayanin akan addini, Haka dai harta kare, sannan tatashi taje tashirya musu breakfast, bayan sun gama suka dawo falo suka zaune tafara kowayar abubuwa, ranar tasaki jiki sosai dashi, A ranar babu inda yafita yana gidan har yamma tayi, kuma ya koyi abubuwa dadama daga gurin rumaisa, ****** ***** **** Allah sarki majnoon, Majnoon nagani a rakube a gefen tati yana kakkarwar sanyi, duk ya rame yakara fita hayyacinsa, Duk da babu hankali a tatare dashi amma dai yaji rashin zuwan rumaisa gurinsa, yashiga da muwa sosai amma babu wadda yadamu dashi balle yasan damuwa sa, yanzu yama soma daina yawan wasar nan da yara, burin shi kawai shidai yaga Rumaisa. .. ALLAH SARKI SOYAYYA... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:43 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 47 and 48 Via *OHW* _A love story_💝 *Bayan kwana biyu* Zarah ce zaune akan gado, tadafe kanta tana hawaye, edonta duk sun kumbura, tasha kukanta mai isarta, Turo kofar d'akin nata akayi akashigo da gudu, bata d'ago kantaba ballema tasan waye yashigo, illadai taji shigowar mutum, Yarinyace yar kemanin shekaru 10 tashigo d'akin tana murna, tafada kan gado inda zarah take, "anty zarah, kingafa abbanmu yasayimun game boy" tafada tana nunawa zarah game din, Zarah ta d'ago edota ta kalleta tace "Feena kije nagani banason damuwa" tafada a kasale Feena tana kallon zarah, tagane kuka take tadan bata fuska tace "anty zarah kuka kike, me akayi miki, mamace ta miki laifi ko Abby" Zarah ta share hawaye ta tadan langawabe kanta kadan tana kallon feena "basu bane, kidai nace kije kibari anjima zamuyi magana" "Faisal ne koh?" Feena tafada tana kallon zarah, zarah ta zare ido tana kallon feena cike da mamaki, tayadda akayi tasan faisal, saikuma ai bazatayi mamakiba domin tana yawan bata labarinshi, bata san lokacin da data girgiza mata kaiba, feena ta tsuke fuska "waishi faisal dinnan duk lokacin da kikaje gurinsa saiya sakaki kuka, ni gaskiya anty zarah kidaina zuwa gurinsa, kima rabu dash.." bata karasa maganar ba zarah ta toshe mata baki, tana girgiza mata kai a lokacin har hawaye sunzo mata ta dora kanta akan feena tana fadan "bazan iyaba feena, wlh bazan iya rabuwa dashi ba, kee bakisan MIYE SO ba, shiyasa kike fadan na rabu dashi, I lov him feena, I lov him...." takarasa maganar tana kuka, Feena ta tausaya mata sosai. tasa hannu ta share mata hawaye sannan tace "anty zarah malamin islamiyarmu yace duk abinda mutum keso toh yakai kukansa a gurin Allah insha Allah allah zai shere masa hawaye, anty zarah mezai hana kifadawa Allah damuwarki" Zarah tayi murmushin yake tace "ngode sister na, nagode sosai, tashi kije inason na kwanta" feena ta mike daga kan gado tanufi hanyar fita tana tana juyo tana kallon antynta, harta fita tabar dakin, zarah takara fashewa da kuka.... **** **** **** **** Kwanan umma biyu kenan a station tayi baki dukta kode, tasha wuya sosai, Yanzu dai kam abba yagane ba umma bace ta sace rumaisa, domin da ace ita tasaceta data fito da ita kodan wahalar datasha, Abba duk ya fita hayyacinsa, 'yarsa k'waya daya tilo tabata, anyi nema har an gaji, dole akaje aka bawa malamai adu'a akan sutayasu da adu'a ko Allah zaisa aganta, tafito a duk inda take , Abba kullum yana station idan baya station to yana gida amma kwata2 yadaina aikin komai, komai nasa yatsata cak, tashin hankali yashiga sosai, zuciyarsa cike da danasanin abinda yayiwa rumaisa, Yauma Yana zaune a station yana tunani2 Zunbur ya mike kamar wadda aka tsigala, dasauri yafita yabar office din, yashiga motarsa, ya kunna yahau hanya gudu yake sosai, harya karasa unguwar da ya saba ganin rumaisa.... wace unguwaceee... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:44 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 49 and 50 Via *OHW* _A love story_💝 Unguwar da majnoon yake zaune, daidai gurin daya zo yasami rumaisa ranar anan yaja birki, yana tsaya yana kallon unguwar, yana jan nunfashi, A gefen wani gida ya hangi majnoon a rakube, yayi wani irin zama kalar tausayu.. Dasauri abba yafito daga cikin motar yanufi gurinsa, yana karasawa ya gurkusa yazauna kusa dashi edon abba sunyi ja sosai, yadube majnoon sai kuma yasaukar da kansa, yanayinsa yabashi tausayi cikn sanyi murya yace " ina rumaisa" majnoon yayi saurin dago kansa yana kallon abba, saikuma ya mike tsaye yana kokarin barin gurin, abba yayi saurin shiga gabansa " magana nake maka ina rumaisa" majnoon ya ture abba daga gabansa yacigaba da tafiyarsa, ran abba yasoma baci kara shiga gaba majnoon ya runtumo kwalar rigarsa yadaga murya sosai yace "kai inaima magana ka kashareni, ina kakaimun rumaisata, wallahi saika fito mun da ita saboda komai yafaru da rumaisa kaine sila, abba yakara jinjiga kwalar rigar majnoon yana fadan " ina rumaisa..." yafada yana hawaye, nan take mutane suka taru a gurin suna kokarin babbare majnoon daga hannun abba, shidai majnoon uffa baiceba, sai mazurai yake da edo, abin tausayi duk ya rama, Abba yana kuka yake fadan " karku barshi yatafi wlh 'yata yasacemun, 'yata tana wurinsa kuce masa yabani 'yata" mutane suka rirrike abba, wasu kuma wasu kuma suka rike majnoon.. daya daga cikin mutanen yace " haba Alhj yazakace mahaukace yasacemaka yarinya, meyasani waddama koshi kansa baisaniba ballema harwata 'yarka, kaidai kaje kanemi wadda yasacema 'yarka amma ba wannanba" nan kaji mutane gurin sunce "gaskiyane wannan bazai iya sace maka 'yaba " wani matashi yana rike da majnoon yace " wannan mahaukacin yau kwanansa biyu kenan ko wasa yadainyi da yara, kullun yana rakube a gefen titi ko agefen unguwa, gaskiya wannan bashi yasace maka 'yarka ba, kaje cen kanemi wadda yasace maka 'ya" Abba yace "wlh shine.. wannan ne " yanuna majnoon, mutane suka ce a fa bashi bane, abba kuwa yayi juyin duniya suka koki bashi gaskiya, mutane suka rikesa suka kaisa har bakin motarsa suka sakashi, sannan ya kunna motar yabar unguwar yana kuka, soyayyar 'ya da mahaifi kenan.... **** *** ***** Faisal kuwa duk ya rame abincima kadan yakeci bai wuce a yuni yaci abinci saudayaba, koshi dandai momy na matsa masa ne, ammashi kwata kwata bayajin dadin abinci, Faisal yana zaune a falo yana kallo bayan dawo daga gurin aikinsa dagashi sai singlet da 3cutr yadora kafarsa kan dani table dake tsakiyar dakin ya jingina jikinsa a jikin kujera, kallo yake amma hankalinsa kwata2 baya gurin yana gurin tunanin rumaisa, gaggar jikinsa ce kawai zaune a gurin amma zuciyarsa bata tare dashi, Momy ce tafito

Table of Contents

Chapters

37 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37