Chapter 36
Chapter 36
kowa saida yatashi, da sauri mai martaba yakira dr bukar akan yazo yadiba, Bada jima waba kuwa yakarsa gidan, yaje ya dubata, Bayan ya dubata ya tabbatar da musu dacewa tanada juna biyu, Bakaramin farin ciki sukayiba, Mubarak saida yayi hawayen farin ciki, akan dadi, Mai martaba yayiwa dr bukar kyauta ta musanman sannan yabar gidan, □□□□ □□□□ □□□□ *ABUJA* bikin Faisal da zarah saura kwana biyu, har an fara hidimar biki, domin har ansaka zarah a lalle, Yauma walimar mata ake, sun kira malamai mata dayawa sunzo sunyi nasiha sosai akan abinda yashafi zaman aure, Soyayyar faisal da zarah kuwa kullum kara yaduwa take acikin zukatansu, _Bayan kwana biyu_ A yaune aka daura auren faisal da zarah, bayan shafe fatiha, kowa fatan zaman lafiya yake musu, Babu yadda faisal baiba da Mubarak yabari rumaisa tazo aurensa amma yaki, acewarsa bayason ta wahala, saboda juna biyun dake jikinta, yace shidai zaizo ya wakilceta, Haka dindai akayi shiyazo bayan an gama daurin aure yakoma kogi, Da dare aka kai amarya zarah dakin angonta faisal, burinta yacika ta mallaki faisal, farin cikinta, muradinta, sannan kuma burinta, Abokanan ango suka kawo ango, sannan kuma kowa ya watse abarsu subiyu, daga ango sai amarya, Faisal ya umurceta data tashi suyi sallah, sukayi alwala atare suka dawo suka yi sallah, Sunkwararo adu'a sosai akan Allah yabasu zaman lafiya, Bayan sun gama suka tashi, zarah kam bawata kunya a gurin Faisal, duk abinda ya buka tabashi, kuma sun raya auren su cikin farin ciki da kaunar juna, □□□□ □□□□ □□□□ _*BAYAN SHEKARA HUDU*_ *KOGI* Rumaisa ce a tsaye tana gyarawa Mubarak saka hularsa, saida ta tabbatar da hular ta zauna A kansa daram, sannan ta janye hannunta tana murmushi, shima murmushin yakemata, sannan tace "amma fa kayi kyau" Ya lakuci hancinta yace "ai duk wannan kyau sanadinkine, domin badan keba da yanzu ina nan a matsayina na MAJNOON" suka kwashe dadariya suduka, rumaisa tace "uhh wayaga MAJNOON da Rumaisa" suka kara kwashewa dadariya, Rumaisa tadan tsayar da dariyarta sannan tace "tunjiya fa nake magana akan inaso naje naga su umma amma kayimun shiru, kusanfa shekara kenan banjeba, dan Allah kabarni naje sati daya zanyi indawo" Ajiyar zuciya Mubarak yayi yana kallonta tabashi tausayi yace "toh shikenan kishirya zuwa jibi saiki wuce, amma fa karki wuce sati dayan nan fa domin ayanzu ke wani bamgarece na jikina idan bakya a kusa dani, bana samun farin ciki" yakarasa maganar tare da kifta mata edo, Murmushi tayi masa tana kallonsa tace "toh MAJNOON dina" ta saka dariya, tana ja da baya, Mubarak ya nunata da dantsa cikin wasa yace "bazaki daina bako" Tana dariya tatoshe bakinta tace "to nadaina shikenan, bazan karaba rabin raina" Tana cikin dariya aka banko kofar dakin da karfi, aka shigo wani dan kyankywana yarone, kamannin sak dana MAJNOON wai Mubarak nakeson nace shiya yadauko, Da gudu yakarasa gurin rumaisa ya rungumeta yana dariya yana fadan "ammi kice karka grandma ta dakeni" Rumaisa tafitar dashi daga jikinta tana murmushi ta kallesa tace "AREEF meka mata ne, ai nasan bazata dakeka abanza ba" Yajuya yana kallon kofar kafin yace "nifa ba abinda namata da wasa nake mata, cije mata kunneta kawai nayi shine wai saita dakeni" Mubarak yayi murmushi yace "zonan areef" da gudu yakarasa gurin Mubarak, mubarak ya tallabesa sama yana masa wasa yace "karka kara cizarmun umma, idannkuwa kakara nima zan cije amminka" suduka suka kwashi dariya, areef yace "papa! Zaka kaini insha Ice cream yau" Mubarak yace "zan kaika yanzuma kuwa, je ammin ka tamaka wanka ta shiryaka kazo muje" yana kokarin saukesa kasa, Rumaisa tace "nima wlh bazaku barniba tare zamuje" Haka kuwa akayi suka shirya suduka suka fita sayen ice cream, haka rayuwar gidan yarima Mubarak take kasancewa cike da farin ciki da kaunar juna, Sai kusan azahar suka dawo Bayan sundawo suka tarar da mai martaba ba lafiya, Dasauri suka isa sashensa, suna shiga suka gansa kwance kan gado, umman Mubarak tana zaune a kusa dashi, areef yaje ya fada jikinta, Tayi murmushi tace "bamunyi fadaba" Areef yace "toh kiyi hakuri bazan sakeba" murmushi kawai tamasa, sannan Mubarak yace "umma wai meke damu abba ne" Umma tace "ai kasani ciwon sane yatashi, kuna fita, wannan ciwon yaki sakinsa, kusan shekara biyu kenan, kullum saiya kwata, sai.kuma ya kara tashi" takarasa maganar cike da nuna damuwa, A daidai lokacin mai martaba yadago hannusa ya kira Mubarak, yaje zauna kusa dashi, mai marta ya rike hannusa yace "Mubarak nifa tsufa yazomin, babu yadda zanyi dole saina sauka kan mulkinnan, bazan iya jira saina mutuba, domin inason insamu farin ciki kafin hakan, dan haka zanyi murabus kai kahau kujerar" Gaban Mubarak ya fadi, harga Allah shidai bayason mulkin nan, domin bayason abinda zai tauyesa ya hanashi farin ciki da iyalinsa, amma babu yadda zaiyi, domin shine magajinsa, Cikin rawar murya yace "nikuma" Mai martaba yace "eh kaidin, kuma banason nadin sarautarnan ya wuce nan da sati biyu, dan haka kaje kishirya duk abinda zaka shirya kafin zuwan wannan lokaci" Ba'a son ransaba ya amsa tayin mai martaba, akan sai karbi sarautar kogi, sannan yabar dakin, Rumaisa kam dadi taji har cikin zuciyata, zata zamo matar sarki, arika kiranta da princess rumaisa □□□□ □□□□ □□□□ Jibi aka hadawa Rumaisa kayanta ita da areef suka wuce abuja, Bayan sunkarasa abuja, umma tayi matukar farin cikin ganinsu, haj luba ma tana gidan, domin abba yahanata komawa sokoto, ba a son rantaba tazauna abuja, Sunyi farin ciki sosai da ganin jinikansu ya girma yayi wayo, yaro mai kyau da shiga rai, Yau kwanan su biyu a abuja, areef ya aza masifa akan shi ala dole sai ankaisa yasai ice cream, Rumaisa ta shiryashi sannan suka fita tare, bayan sun karasa gurin mai ice cream, suka siyo sannan suka juya suka nufi gurin mota, Tana kokarin bude kofar motar, tajiyo sautin wata murya a kusa da ita ana fadan "Aina gaya miki zan dawo, bazaki taba gujemunba"... dam, dam gabanta yafadi, domin tasoma gane mai muryar, a hankali take dago kanta, caraf sukayi edo hudu da FAHAD.... https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr [10/20, 10:55 PM] +234 905 395 7618: _Title:-_ *MAJNOON*😴 _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES*😃 *Last episode* Via *OHW* _A love story_💝 Firgita karara ta bayyana a fuskar Rumaisa saida taja da baya saboda tsoro, ya kura mata edo, kamar ya cinyeta, Da kyardai tasamu tayi controling kanta ta dago kanta ta dube cike da bacin rai ta tsuke fuska tace "karka kara mun magana, ni matar aure ce.... " bata karasa maganarba taga wata yar karamar yarinya ta nufi inda suke da gudu tana fadan "daddyyy" rumaisa ta tsureta da kallo, Yarinyar ta zuwa ta fada jikin fahad cikin shagwaba tace "daddy shine kazonan koh, nida momy munacen muna jiranka" Fahad yayi murmushi ya tallabo yarinyar sannan yace "sorry my little RUMY, ina nan gurin mamanki" Rumy tace " wacece mamana,? Momy fa tana cikin mota" Fahad ya nuna rumaisa yace "gatanan" Rumy ta juyo ta dube rumaisa tace "daddy wacece kuma wannan" Fahad yayi murmushi yace "sunanku daya keda ita, ta sanadiyarta kika samu wannan" Rumaisa duk mamaki yacikata, a hankali tana murmushi ta dube fahad tace " kayi aurene?" Fahad ya ajiye rumy kasa, yana jiyeta tazura da gudu tana fadan "bari naje nakira momy" Sannan Fahad
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37