Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shiga dukkan daliban ajin suka mike dongirmama malaminsu suka hada baki dukkansu''good morning sir'' haisam yayi murmushi yace''morning how are you ? Suka sake hada bakisuka ce'' we are fine sir'' yace thank you sit down ''kowacce ta zauna akan kujerarta. Haisam ya jawo hannah gaban aji yace'' ga wata sabuwar dalibakun samu'' rauda itace monita ta mike tace'' lah ,what is your name ? Hannah ta daga ido tanakallon haisam'' ya harareta ma'ana ta bada amsa ,hannah tace'' my name is hannah abubakar imam''kama yadda haisam yace ta dinga fada. Nusaiba wacce itace mataimakiyan monita tace'' emh, nicename you are welcome hannah'' haisam yayimurmushi ya ce'' kun fara iyayin naku ko ? To mazaku saka mata kujerarta a tsakiyar taku a gabakuma kunga itama yar kucila ce kamar ku'' cikinsauri rauda taje bayan aji ta dauko kujera ta kawo ta koma ta dauko tebur yazo ta dasa a tsakiyar su ajere. Dake duk ajin su duka ukun sune kanananajin sunfi kowa kankanta kasancewar akwaidingin dingin din yammata a ajin musammankabilun na wata sai ka rantse uwa ce amma yar ajidaya ce farin ciki ya lullube hannah da haisam musamman ma haisam yaga hannah ta samu shigaa wajen nusaiba da rauda wadanda su suka fi dukyan ajin kokari dan rauda a america tayi karatunnusery da primary dinta don haka tana bala'inkokari ga turanci daya kama bakinta hausa matana kokarin ta subuce mata.Kuma auwal abokin haisam ne na kuttan kaibabanta alhaji shitu abokin baban haisam nesannan ramla yayarta ita haisam zai aura don hakanema aka kawo rauda makarantar saboda haisamyana nan tazo akayi mata jarabawa taci shikenanaka dauketa, don haka nema take kiransa da yaya haisam sabanin uncle haisam da sauran dalibaisuke kiransa. Nusaiba ma wata tsadaddiyarmakaranta ta gama a abuja, ita yanzu hakaiyayenta suna abuja karatu ya kawota nan ammasu haifaffun garin gwambe ne fulani, rauda danusaiba sun zama kawaye tun ranan da suka hadu ranar da aka kawosu makaranta, ajinsu daya sukakuma ci sa.a dakinsu daya don haka ga gadonrauda ga na nusaiba kuma sun hada kayanakwatinsu. Haisam yace monita da mataimakiyartaku biyoni waje ina da magana daku rauda danusaiba suka mike suka bi haisam wajen ajin. Hannah na zaune babu abunda take sai kallonginin ajin da dalibai daya bayan daya taga kowaccesanye da uniform dinta tsaf tsaf, fararen takalmakambas da fararen safa kan kowacce kitso ne tar.Hannah tace a ranta ashe da na sha kunya da aceranar da baba ya kawo ni a haka na shigo ajin nan da na fita daban, kai wannan malami ya taimakeniallah yayi masa albarka. Taci gaba da kallon gininajin da irin zane zane da akayi a takarda duk anlillika a jikin bango ga fankoki a jikin silin sunatafitar da sansanyar iska suka , ginin bulo hannah tafada a fili ba tare data san a baiyane ta fada ba, bayan fitarsu haisam a bayan ajin suka tsaya yakalli rauda ya juya ya kalli nusaiba yace raudanusaiba su duka suka amsa yaci gaba da cewa gahannah nan , kamar rauda kike kawar nusaiba tohannah ta zama kawarki itama, sannan kamaryadda ke nusaiba kike kawar kawar rauda to ina son hannah ta zama kawarki duk da ku biyudakinku daya to hannah ma yar dakin kuce dakesafiyanu ya fada masa sunan dakin hannah yacedon haka ku uku dakinku daya ajinku daya. Kamaryadda a ko ina kuna tare a hall ne, a ajine a daki neto hannah ma ta zamana kuna tare itama kanwata ce kunji ko ? Su dukka suka amsa. Nusaiba tace''uncle haisam ko baka ce mu zama kawaye badaman zamu zama tana burgemu'' haisam yayidariya ya juya ya kalli rauda yace'' kanwata ke bakice komai ba ke bata burgeki ? Rauda ta tabe bakitace'' yaya haisam rannan fa kace nice kadai kanwarka a makarantar nan yanzu kuma kace itace'' haisam ya kyalkyale da dariya ya dafa kantayace!! Rauda kenan, ai har yanzu kina nan amatsayinki na kanwata itama hannah yar uwata cekibga dole kanwatace, nusaiba ma kanwata ce donhaka karki damu. Gata nan duk abunda bata sani ba akan karatu ki koya mata. Haka kuma maganada turanci ku rika tunasar da ita koda ta manta tayihausa karku rubuta sunanta a masu yin hausa sai ahankali zata saba itama ta rinka yin turanci sosai.Haka a daki idan bata san yadda zata yi amfani dawani abu ba kamar man gashi in zata shafa a jiki ku nuna mata mata na gashi ne ba ku ringa yi matadariya ba kuna gayawa kawayenku kunji ?Musamman ke rauda kinga rose suna yawan kawomun kararki wai kina yi musu tsawa kar in sakenaji kina yiwa hannah kinji ko ? Rauda tace''yayaya za'ayi ta shafa man gashi a jiki sai kace bakauyiya'' haisam ya ce a,a wai a misalai nakenufi, koda ace zata manta ta dauko man gashin''tafiyar wani malami ce tasa duka hankalinsu yahuya baya don ganin mai tahowa, haisam yace'' toshikenan ku koma aji ga malam shaiya nan zaikaya muku maths an kada firs period,'' suka ruga a guje, malam shaiya ya mikawa haisam hannu sukagaisa sannan ya nufi s.s.3c yana da period yanakoya musu geograpykamar haisam yayi duba da yace idan ta daukoman gashi zata shafa a jiki haka kuwa aka yihannah babu abunda ta sani a kayan akwatintadaga ta dauko man wanke gashi [shamppoo] takwaba a jikinta sai ta dauko man shafawa ta makaa kanta makilin ma wani lokaci a tsagar kitso rauda tazo ta isketa tana sharbawa. Suyi ta dariya har sugodewa allah daga karshe dai suyi mata bayanidalla dalla , wannan ne na kaza wannan kuma awaje kaza ake shafawa. Babu laifi a sati biyuhannah ta waye ta gane duk kayayyakin amfani nazamani sannan ta koyi cin kayan gwangwani dana kwali, don da farko inda suka dama comflask damadara cokali daya zatayi sai ta fita a guje ta kelayaamai bata sanshi ba haka sardine da gesha kifingwangwani sai taki ci tace tsutsace amma dagabaya duk ta waye tana ci. Hannah tana farin cikimatuka da wannan sabuwar rayuwar data tsinci kanta. Abinci lafiyayye a akwatinta na makaranta ,gashi tana cikin yara sa'anninta suyi karatu taresuyi wasa tare musamman nusaiba tana bala'inkaunar hannah tafi rauda kirki don rauda ta cikanuna isa da nuna tafi kowa kuma duk girmanka saita riga daka tsawa.Ta fannin karatu kuwa. Ada hannah dumama kujera take yi kawai saboda tsantsar turanci ake yia makarantar amma sai nusaiba ta lura hannahbata fahimta don haka a koda yaushe bayanmalami ya gama darasinsa sai ta matso da kujerartahar kusa da ta hannah tayi mata bayani dalla dalla. Haka shima malam haisam kullum a prep dinyamma yana zuwa ya kira hannah ya koya mataabubuwa da dama. A wata daya hannah ta faragane turanci fiye da yadda kuke zato. Ranar wataasabar da daddare ranar ne ake warewa dalibai sushakata su hole rayuwarsu kamar a saka musu kidan disko su cashe wasu kuma su kada tebur dakansu suna waka wasu na rawa. Wasu kumatalabijin ake kunnawa da bidiyo suyi kallon kasetduk dai abunda ransu keso shi zasu yi. Daga 'yanj.s.s 1 har manyansu s.s.3 Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 GANGARJIKINSA NA AURA 1 Part 2 Posted by ANaM Dorayi on 02:02 PM, 30-Apr-15 Under: Gangarjikinsa ta Aura Wannan rana ita ake kirada '' social night'' uncle haisam kuma shine social master wato shine malamin da yake kula da dalibaiyake kula

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});