Chapter 14
Chapter 14
motar bane ?Haisam ya leka cikin motar ya tsaya yana kallonhannah baice mata komai ba, ta sunkuyar da kaicikin sanyi jiki ta jawo jakar litattafanta (schoolbag)ta rataya ta juyo ta kalli rauda ta kalli auwaltace'' na tafi sai anjimanku'' rauda tace au har dake zaku shiga motar haya kin fasa zuwa kanon ne ?Hannah ta gyada kai kawai sannan ta fito. Yayaauwal yana yi mata wasa yana cewa, af ashe yarkauye ce ma, motar babura zaku hau ko? Hannahta fita ba tare da ta bashi amsa ba,. Haisam dahannah suma suka nufi cikin tasha dama uwar biyu da kwandasatan daya dauki jakar sun shiga tasha.Motar bus ce wacce baifi mutane hudu ba ta cikaba. Uwar biyu ta zauna a kujerar baya aka sakajakar hannah a but hannah ma taje kusa da uwarbiyu ta zauna, jikinya sanyi kalau kamar marar lakahankalinta a tashe yake kamar wacce za'a kaita lahira ba gidansu ba. Haisam ya zaga ta wundon dauwar biyu ke zaune ya danko kudi ya mika mata yace' ga wannan kuyi kudin mota dan karku mastu kibiya kudin kujerun bayan a barku ku kadai sannanki fito ki shiga aishalle super market kafin mota tacika ki siyowa hannah sabulun wanka, wanki man shafawa dana gashi. Biskit da alewoyi ta yiwa yangidansu tsaraba.?ya sake deno wasu kudi masuyawa yace wannan kuma ki ajiye da zarar hutu yakare ya rage kwana biyu kije ki taho da ita kikawota gidanki zanzo in kara yi mata siyayya namayar da ita makaranta. A cikin kudin ki bawa mahaifinta dan na kashewa ki gaya masa lallai lallaihutun kwana arba'in da biyu aka basu da zararhutu yana karewa zaki zo ki dauke ta inji ni zakice.Ki san dai kalaman da zaki gaya masa na kwantarda hankali kada ya hanata dawowa kinsantsofaffin nan namu, kice ke uwar dakin tace a wajenki take a makaranta na hadaku, kice inagaisheshi da kyau. Uwar biyu tayi godaya tashialbarka kamar ita aka bawa kudin ko jikarta. Yadauko wasu kudin ya mikawa uwar biyu yace'' kisayawa hannah sarka da dan kunne na jiyal maikyau ki bata'' uwar biyu tace'' kai kudin ai yayi yawa malam haisam duk a cikin wannan ya isa nayimata siyayyar'' ya ce ''ba komai na gode uwar biyuallah ya kiyaye hanya'' tace amin malam mune dagodiya'' ya zagayo jikin wundon da hannah kezaune tayi tagumi ta langwabar da kai a jikinwundon mota jawaye ne yake sulalowa daga idanuwanta daya bayan daya. Haisam ya kalletayayin da yaji kamar zuciyarsa zata fashe dontsananin tausayinta , yayi karfin hali yace'' hannahkukan meye kike don kawai anyi hutu zaki tafigida ? Ai hutu na karewa uwar biyu zata je tadaukoki kinji ko ? Zan zo inyi miki siyayya na mayar dake makaranta, yanxu idan kika je gida kinakuka baba zaice wahala kike sha a makarantar yace ba zaki dawo ba. Amma ki nunawa babamakarantar da dadi ga ladabi da biyayyar da akekoya muku ga karatu da abinci a wadace shi kansazaice ki dawo, kinji ko ? Hannah ta gyada kai ta fara share hawayen idonta. Yace gaba da cewa'' kiyihakuri da abun da iya abu take yi miki hutu nakarewa uwar biyu zata zo ta daukeki ta kawo kimakaranta. Sannan kullum ki rika zuwamakarantar islamiyya kina kuma duba litattafankina makarantar boko don karki manta karatu kinji. Allah ya kiyaye hanya hannah. Ya juya ya tafi,muryarta yaji ta rushe da kuka, ya juyo ya tsaya cakyana kallonta sai ya rasa me ma zai ce mata sai yajuya ya tafi da sauri. Yana mai tsananin damuwa datakaici.kukan zuci kawai yake. Ba tare da ya cewa suauwal komai ba, ya ja mota ya fara tukawa. Canrauda ta nisa tace'' yaya haisam daman hannahfulanin daura ne, ko ba daura zasu ba ? Haisam yayidan murmushi kawai. Auwal yace'' haisam ka cikashige shige ina ka samu wannan buzuwar har da kakarta kuma? Haisam yacce'' wai shige shige ni dakai za'a san me shige shige naga daga zuwa harkasan su naja'at suleman ko banga sanda takebaka adiredhinta ba balle ni dana shekara amakarantar'' auwal yace to ya isa ga wannanzabiyar a baya ta bude kunnuwa tana daukar rahoto'' haka dai har suka isa kano jifa jifa haisamyake magana babu abunda yake tunawa sai halinda hannah zata kasance a gidansu. Zuciyarsa cikeda tausayinta kulle kullen yaya zaiyi yaci gaba dataimakonta yake gashi kuma ya bar makarantar,har suka isa kano . A nasarawa g.r,a suleman cresent gidan su haisam yake, suka shiga cikinkatafaren get din gidan . Bayan auwal da rauda sunshiga sun gaisa da hajiyar haisam sai suka yi mususallama suka nufi suma nasu gidan da yake lamidocresent basu da nisa sosai. Alhaji shitu mukhtar sunan mahaifinsu rauda,mahaifiyarsu kuma hajiya jamila sunanta alh. Shitumuktar haifafen garin kano ne, dan unguwankabara ne tare sukayi firamare da sakandire damahaifin haisam abokaine tun suna yara. Haj.Jamila kuwa mahaifiyar su rauda mutumiyar chadi ce ya aureta. Allah ya albarkacesu da 'ya'ya uku,yaya auwal shine wanda ya kammala karatunlikitansa a america yanzu cikakken likita ne. Sai antiramla wanda ta gama sakandirenta a wannanshekaran tana jiran sakamakon jarabawarta tawuce jami'a bayan an cancara bikinta da angonta haisam, saita fara karatu a gidanta, sai yar autarsurauda wacce yanxu take ajin farko a sakandire.Tsantsar yan boko ne yaya uku sun ishesurayuwar duniya suna basu cikakkiyar kulawa datsantsarso da kauna. Allaha yayi musu arziki maiyawa don haka a daula suke ta ko ina hutu, ba su fi shekara biyu da dawowa nijeriya ba kasancewaralh. Shitu muktar yana aiki a embassy, shinejakadan nigeria a america {ambassador} don hakaduk a can suka yi karatunsu har mahaifiyarsu haj.Jamila acan tayi digirinta.al'amarin hannah da uwar biyu kuwa, bayan tafiyar haisam uwar biyu tayi sauri ta sauka daga motartaje ta yiwa hannah siyayyar kamar yadda malamhaisam ya umarceta da tayi. Ta dawo cikin mota dasauri ta iske motar dai bata cikaba , bayan mota tacika suka kama hanyar tafiya. A hanya uwar biyu taci gaba da lallashin hannah tana bata baki dakyar tayi shiru da kukan da take yi. Ta dade daman tanaso taji labarin hannah da dangantakarta da malamhaisam, saboda tsananin kulawar data ga yana yimata, cikin wayo da dubara irin na manya uwarbiyu ta dinga bugun cikin hannah tana son tajilabarina. Abunka da yarinya kuma mai neman agaji da take yi ta ko ina hannah ta fayya cewa uwarbiyu komai daga biri har wutsiya. Uwar biyu tatausaya hannah ta sake jinjinawa malam haisambisa jihadin da yayi saboda allah na taimakonhannah. A garin babban mutum suka sauka aka saukemusu jakarsu . Tun daga sauka hannah ta farafaduwar gaba tazo garin da bawa ya fita jin dadi.Uwar biyu ta lura da hakan sai tayi ta bata baki tanakwantar mata da hankalinta. Kawayen hannahmaza da mata yan garin suka baibayeta suna kallonta wasu kuma suna shishshige mata harrububin yi mata magana su ke. Masu daukar matajaka suka dauka suka dunguma zuwa gidan suhannah. Samarin garin sai kallon hannah suke ganisuke kamar ba hannar da bace da suka sani. Tayijawur da ita tsaf tsaf. Babban mamakin kambas din da ta dana a kafarta suke kallo wasu na cewatakalmin yan ball tasa, wasu na cewa na faretinsojoji ne. Mamaki ya ishesu yadda akayi hannah tazama haka kamar baturiya a wata guda nan danan, kyau na zuba duka cikar garin da batsewarsababu mai kyawun hanne da gogewarta. Nanfa samari kowa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31