Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Complete Hausa Novel 1,217 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da c.d din da ake kunna disco da bidiyoda talabijin din da ake kunnawa. A wannan dare anyarjewa dalibai su saka kayansu na gida{persinal}kowane iri ne kama daga leshi ko shadda riga daskit kai har jeans da tea shirt duk zasu iya tsukewa. Rauda sarkin rawa ita har tunanin wannan asabardin wacce irin rawa zanyi don har fili ake batakowa ya koma gefe yana kallonta rawa salo salohar wasu suke kiranta janet jacson wai kanwarmacheal jacson nusaiba kuwa ita da hannaah babuabinda suka fi so irin kallon bidiyo hausa fim masu kyau malam haisam yake samowa ko nigerian fims.Social night din wannan asabar din bata yiwahannah da nusaiba dadi ba saboda bidiyo talalacebabu kallo sai dai c.d aka kunna aka ware kida dukmai bukata yaje ya cashe wasu na rawa wasukuma na gefe suna kallo. Amma wasu suna kan barandar wajen hall din a zazzaune basa sha'awaryin rawa ko kallon masu rawa kungiya kunkiyakowanne da group dinsu suna waje suna zazzaunesuna hirar duniya. Hannah da nusaiba suna dayadaga cikin wadanda basu shiga cikin hall din bawajen kida suna zazzaune a can kan wata barandar ofishin malami suna hirar duniya, hirarma ma jifa jifa suke yi saboda duk rayukansu abace yake yau babu kallo kuma wani hadaddenamerican film mai suna''mr bones''uncle haisamyayi musu alkawarin zai saka musu. Nusaiba tayiajiyar zuciya tace anya kuwa yau zan iya bacci saboda bakin ciki na kudiri niyar danin firm dinnan,wallahi fim din akwai abin dariya muna dashi fa agidanmu. Hannah tace na last week ma yayi kyauga abin dariya osofia in london yaya haisam ya iyazabo man films masu kyau. Wata murya ce abayansu tace na kamaku kuna gulmata'' suka juya da sauri sai suka ga yaya haisam ne su duka sukatuntsire da dariya ya zagayo suka matsa masa yashiga tsakiyarsu ya zauna yayi murmushi ya cekuna gulma ta ko, dan ban kunna muku kallo bako ? Nusaiba cikin shagwaba tace'' yaya haisam harkwalla nayi fa wallahi yau duk ranmu a bace yake. Haisam yayi dariya yace'' kai haba harda kwalla ?Ke fa hannah kema kinyi kukan ? Tayi murmushitace a.a banyi ba uncle haisam. ''yaci gaba da jansuda hira yana zolayarsu kamar yadda ya saba wasada dariya da dukkanin daliban makarantarmusamman da wadannan ukun. Ya ce dasu '' ga rauda can a hall tana cashewa kuje ku tayata manako kuma kuyi mata liki. Suka danyi dariya suka ce ''mu bama rawa'' suka ci gaba da jugum , haisam yalura yau dai nusaiba da hannah babu kanta basason magana balle doguwar hira yace nusaiba,hannah yaya haka kowacce tayi zugum babu nishadi kamar yau ba ranar social night ba. Nusaibatace''yaya haisam tsabar bakin cikin rashin kallonnan ne yake damunmu.'' yace shi yasa baku fara'a?To yanzu daya bayan daya sai kun yimin waka darawa tunda yau social night dole kuyi murna'' cikinshagwaba nusaiba tace''yaya ni bana iya waka ba sai dai hannah ta fara tunda itace karama. Hannahtayi dariya tace to bari inyi muku wakan sarkingarinmu,'' hannah ta fara tafi ta fara rero waka.Haisam yace'' to tsaya tafi akeyi muma mu dingatayaki muna muki amshi ? Tace'' ai da kwarya akekida dan dai babu kwaryar ne. Yasa hannu a aljihunsa ya zaro wannan abun busar daya karba awajenta ya ce zai ajiye mata ya ce'' ga abun busarkima ki busa mana ki rero mana wakar kiwo'' cikinfarin ciki hannah ta karbi abun busarta ta haujujjuyashi tana cewa'' allah sarki abun busata nadade ban busa kaba,'' nusaiba tace '' lah busa muji yadda akeyi'' hannah ta kaikaice ta fara busa abunbusarta tana rera waka kamar haka. muyi kiwosamari. Kuyi kiwo yan mata kiwo baiwa ne. Wakabaiwa ce. Haka busa ma baiwa ce kuyi soyayyasamari. Kuyi soyayya 'yan mata ke 'yar budurwaina naki gwanin ? Ni nawa gwanin baya nan. Yayi tafiya amma koda bana tare da gangar jikinsa.Ruhinsa yana tare dani. Haisam yace '' hannahtsaya meye koda gangar jikinsa bata tare daniruhinsa yana tare dani ''? Tayi shiru can tace ohonima haka ya mun wakar nusaiba tace meye ''ruhi ? Hannah tace '' nima ban sani ba, ina jin larabci ne , haisam yayi dariya ya ce '' yarinta mai dadi. Kwanci tashi yau kwanan hanna arba'in amakaranta har an kafe musu tine table dinjarabawa wato end of 1st teem examinationkasancewar daman dalibai sai da suka yi kimaninwata guda da dawowa makaranta sannan akakawi hannah babu abunda yaya haisam yake yi sai nasihohi da yake yiwa yan ajinsa wato j.s.s 1a dakowacce ta cire wasa tasa littafin karatu a gabantadon suci jarabawa. Haka kuma wasu lokuta ya kankira kannansa rauda, nusaiba da hannah yanakara musu fada dasu dage sufi kowa cin jarabawaya sake xewa'' hannah bana jin fargabar su rauda kamar ke don haka ki dage duk abunda ba ki saniba ki tambayi nusaiba ko rauda idan sun sani sukoya muki, idan kuwa basu sani ba to kuzo kutambayeni. Haisam yayi musu rantsuwa da allah acikin su ukun nan duk wanda ta fadi jarabawartasai yayi mata bulala kuma daga ranar data fadi jarabawa babu ruwansa da ita ya cireta a cikinkannansa gaban hanna ya fadi rasa dajin bayaninyaya haisam tace a ranta tace idan yaya haisa yacebabu ruwansa dani aina shiga uku tunda babu maiyimun siyayyar makaranta karshenta ma karshenkaratuna yazo. Ta kudiri aniyar daga yau babu ita babu cikakken bacci zata dage da karatu don tacijarabawa kada haisam yayi fushi da ita. a sati dayasu hannah suka gama jarabawarsu,jarabawabibiyu suke a rana daya. Don haka babu hutu badare ba rana kowacce ta dukufa da karatu,musamman hannah sallah ce da cin abinci tashinta daga kan littafin karatunta, haka kuma ta zanajarabawar cikin sauki ma'ana da an bata questionpaper sai taga tasan amsoshin gaba daya, hakatake amsasu cikin sauki saboda tsaban ta gamakarance litattafanta, hannah tasan yaya haisamzayyi murna da sakamakon jarabawarta tunda tayi karatu yadda ya kamata. Hutu kuma sai juma.a donhaka dukka wadannan ranakun babu abinda sukeyi sai wasanni da raye raye da wasanninkwaikwayo na kungiyoyi (club)din makarantarkasancewar akwai kungiyoyi daban daban amakarantar kaar english club, hausa club, jet club. Che,ical club, geography club. Yoroba da igbo dadai sauransu, kuma kowacce daliba daga yar ajidaya zuwa shida tana da damar da zata shigakowanne club a makarantar. Su kuwa malamaicikin satin nan suka dukufa da aikin makinjarabawar dalibai, don ganin kafin ranar hutu sun bawa kowacce daliba sakamakon jarabawarta tatafi dashi gida iyayenta su gani. Ranar alhamis anagobe hutu haisam ya tara 'yan ajinsa a bakinbabban dakin taron dake makaranatar wato halldon ya bawa kowacce sakamakon jarabawarta(report card) 'yan ajin malam haisam suna da dimbun yawa don dalibai saba'in da shida ne a ajinhausawa da yarbawa,igbo,musulmai da kiristocisma da talatin ba hausawa bane kuma ba kiristocibane, wata ko zo bata sani ba da hausa, tundadaga kudu suke babu abunda suka sa a gaba saikaratun littafinsu don shine abunda ya kawosu tun daga uwa duniya zuwa nan arewa. Don haka babukoma baya a ciki kowacce tayi iya kokarintamatuka a wannan jarabawa. haisam ya kallifuskokinsu daya bayan daya sannan ya kyalkyaleda dariya. Abun mamaki babu wacce ta taya shidariya kamar yadda suke wasa da dariya a aji yau kowacce fargaban jin sakamakonta takemasamman ma hanna. Tunanin maganar da yayahaisam ya fada yayi musu ranstuwa yace dukwacce ta fadi jarabawa sai yayi mata bulala kumababu ruwansa da ita. Hakika bata fargabar

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});