Chapter 19
Chapter 19
tsawa tacemusu munafukai su saketa tazo da kanta. Haka hannah ta fara tafiya tana rirrike bango ta fita tazagaya bayan aji inda suke. Juwairiyya ta mikamata ledar da haisam ya bayar a bata suka ce''gashi inji saurayinki. Hannah tayi jugum tanamamaki can tace waye'' waye kuma saurayina?Salaha tace'' zaki sashi munafuka. Juwairiyya ta mika mata wata takarda tace'' ki kaiwa unclehaisam kice ina jiran amsa yanzu kice nace mikikarki sake ki dawo min babu amsa'' hannah ta faratafiya jiri yana daukarta ji take kamar ta fadi sabodayini cur a kwance babu ko dan tea a cikinta. Ta isaofishinsa ta kwankwasa yayi mamaki da yaji ana kwankwasa masa kofa yanzu, ya tashi ya bude saiga hannah a tsaye. Mamaki ya kamashi yace''hannah lafiya ? Keda baki da lafiya kika iyatahowa? Hannah ta cije baki gami da rike bangokamar zata fadi tace'' aikoni wajenka aka yi'' yace''aike kuma, waye ya aikoki? Ta mika masa wasika tace ''inji senior juwairiyya da senior salaha suncedole in taho musu da amsa kar inzo babu amsa yabata rai ya karbi wasikar ya bude ya karanta.Wasika ce irin ta kullum daga juwairiyya ya cecirayuwarta tana sonsa.Haisam ya cikuikuye ya wurgar ya ce'' sun bakimagungunanki'' tace''ah ina ji sune anan'' ya karbaya bubbude yana tsiyaya mata a murfi yana mikamata sai ta karba tasha. Sai da ya tabbatar ta shadukka sannan ya daure ledar ya mika mata ya ce tawuce daki ta kwanta gibe idan taga baza ta iya fitowa aji ba tayi kwanciyarta zai sanarwa da dutymaster. Daga karshe ya ce'' sai da safe allah ya bakilafiya hannah. Tace amin '' har ta juya zata tafi sai tatuna ta juyo tace masa'' me zan cewa seniorjuwairiyya ? Ya ce'' kice nace tazo ta karbi amsar dakanta. Hannah ta amsa da to sannan ta tafi. Daman su juwairiyya na zaune a wata baranda suna hangosu. Hannah tazo wucewa suka kirata tace musu takai masa ya ce amsar taje da kanta ta karba. Salahatace'' jeki to'' juwairiyya ta nisa tace'' kinga haisamko wallahi wulakanci yake shirin yimin tunda ya ceinje da kaina ni nasan ba wata maganar amincewa zaiyi min ba. Saboda ai nagani cukuikuye wasikartawa yayi ya yar a kasa, ya buge da bata magani aidole ma son hannah yake'' salaha tace'' ammakuwa sunan yarinyar na gawa don sai taci ubanta amakarantar nan , mu 'yan s.s.3 muce muna sonsayaki ya so junior mu ai bazai yuba. Jeki kiji abinda zai fada muki don muci uwarta da hujja'' juwairiyyata mike ta nufi ofishin haisam tana wani karkaderiga tana gyara fuska. Tayi sallama gami da turakofar zata shiga ya dakatar da ita da hannu yace''tsaya daga nan baranda kiji abunda zan fada miki.Don me kika sake yimin aiken wasika bayan nace kada wanda ya sake zomin da wasikarki. Kumawanne rashin tausayi ne da zaki taso yarinya mararlafiya ki aikota, duk daliban makarantar nan, saihannah ? Me yasa sai ita zaki aiko juwairiyya ?Juwairiyya ta tsuke fuska tace'' amma uncle haisamduk aiken dana keyi baka taba kirawoni kace meya sa nake aiko kawayena ba sai dai kacewayan aiken duk wacce ta sake zuwa zaka sabarmata. Meya sa baka fadawa yar aiken ba a wannankaron sai ni ka kira ? Haisam ya fusata ya dakamata tsawa yace'' ina tambayarki kina tambayata ?To kar kiji yauce rana ta karshe da zaki yimin haka. Ki rike darajarki da mutuncinki a matsayinki na yamace budurwa. Idan sai kinyi soyayya a makarantaba karatu ya kawo kiba to ga sauran malaman dasuke rubibin sonki amma ni bani da ra'ayinsoyayya, this is the last warninng bana son na sakeganin sako daga wajen ki sai anjima kije. Wani jiri jiri juwairiyya take ji ta juya ta tafi tana kwafa.Salaha tazo ta tare ta a hanya tana cewa'' meyenake hangoki a baranda ofishinsa ma ya hanakishiga ? Juwairiyya tace'' ke dai muje in baki labarinyadda muka yi'' daman lokacin tashi daga prepyayi duka dalibai sun dungumo daga ajijuwansu sun doshi dakunansu. Don haka juwairiyya dasalaha nura sai suka nufi hostel a hanya ta zaiyanamata duk yadda suka yi da uncle mai kyau watohaisam. washegari talata da sassafe bakwai da rabia lokacin dalibai suke firfitowa daga dakunansuzuwa ajijuwansu domin daukar darussa. Uncle haisam a tsaye yake kem a bakin get din hostelyana kallon masu fitowa daga ciki, mamaki yakama dalibai ganin sabon al'amari meye unclehaisam yazo ya tsaya anan da sassafe haka bashine da duty ba, ba ranar inspection ba kuma.Kowacce idan ta ganshi sai ta duka ta mika gaisuwa ta wuce'' good morning sir'' can ya hangorauda da nusaiba da pamella suna tahowa daganesa ya dauka hannah ce sai da suka karaso yagababu hannah a cikinsu. Bayan sun gaisheshi ya ce''yau kuma ina hannah ko jikin ne ? Rauda ta waigagaba da baya taga babu kowa sai ta matso kusa dashi tace'' hannah ba lafiya tana clinic a kwanceacan ta kwana'' gabansa ya yanke ya fadi ya ce''zazzabin ne ya rufeta ? Nusaiba tace'' wannan yafizazzabi yaya'' rauda tace'' su senior juwairiyya nesuka yi mata duka da tsakar dare kusan dukkan s.s3 sai da kowacce ta doki hannah jiya ina ji a sume ta fadi da kyar matron suka zo suka hana su. Mumabamu san me tayi musu ba. Kuka mu ma mukakwana muna nan da nan haisam ya canja ido yakada yayi jawur gashin jikinsa ya mimmike kai kacemuku mukun sanyi ake amma duk da sanyin safiyazufa yake yi. . Ba tare daya ce tak ba ya juya ya nufi clinic inda hannah take a kwance ya same ta rikkicifbata sanma inda hayyacinta yake ba. Abinka dafarar fata sai sabun bulalan suka mata jawur a jiki ,har wuyanta da fuskarta shatin bulala ne lambar.Ya dade a tsaye yana kallonta kawai yasa hannu yacire mata wani ganyen maina daya makale mata a wuya a sanadiyar duka sai yaji jikinta zafi kaukamar wuta, yaja mayafin dake kan gadon yalullubeta. Babu kowa a clinic din nurse din ma batanan. Ya juya ya fita a fusace ya nufi ofishin principal.Ya shiga ofishin gami da yin sallama ya sami wajeya zauna bayan sun gaisa ta dubi haisam tace''haisam lafiya yau na ganka ranka a bace dukwannan fara'ar taka ? Ya ce''dole raina ya bacisaboda kusan kashe wata yarinya akayi a daren jiya a makarantar nan 'yan aji shida ne suka dakiwata yar aji hudu da tsakar dare kamar zasukasheta tana clinic a kwance'' principal ta zaburatace'' subhanallah'' ta danna kararrawa masinja yashigo tace maza yaje aji shida ya kira matajuwairiyya. Haisam da principal na zaune sunyi jugun kowa yana tunani a zuciyarsa. Can saigajuwairiyya ta karaso ita da wani malami mai sunasahabi tazo ta dutkusa a kasa ta gaishe daprincipal. Principal ko amsawa bata yiba ta rufejuwairiyya da fada tana cewa'' in har ba zaki iyahana a aikata laifi ba a makarantata banga amfaninki ba a matsayinki na shugabar dalibai''haisam yace'' madam ai itace ta gaiyato sauran yanaji shidan suka hadu sukayi dukan'' principal tace''oh har da ke head girl kuka hadu aka kusa kasheyarinya, kiyi kneel down yau sai kun yabawa ayazakinta'' uncle sahabi yayi carab ya ce'' madam tsaya kiji, juwairiyya ta fadamun duk abunda yafaru daman zamu taho wajenki muka hadu damasinja a hanya a gaskiya yarinyar ce bata dakunya wai cewa tayi zata yi dambe da head girlshine juwairiyya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31