Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 28

Chapter 28

Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Complete Hausa Novel 1,222 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da hannah take rusawa shine ya dabartar da haisam ya rasaabunda zai ce shima ji yayi kwalla ta cika masa idotaf sai kawai ya juya ya tafi ya ce'' allah ya kiyayehanya, sai anjima'' wani kululun bakin cikin neyazo ya tokaresu dukkansu a wuya tsananin bakincikin rabuwa da juna. Gagarumin tashin hankali ya mamaye zukatansu kowanne na fidda ran sakeganin dan uwansa kuma. To tayaya hanna zata zokano tace tazo ta gaishe da malaminta bayan ramlana nan na nemanta zata halakata idon ta idon tatace sai taga bayanta. Shi kuma yaya za'ayi haisamyaje garinsu hanna bayan duk gari ya dauka sharrin da ramla tayi, iya abu na yadawa hanna bakaratu take yi ba soyayya take yi da wanimalaminta. Hanna tayi zugum a zaune a mota ji takeduk duniyar babu dadi. Yanzu zaman dindindinzata je suyi da iya abu tasan ba karamin bakin cikizata hadu dashi ba a gidan. Ga tsananin bakin cikin rabuwa da yaya haisam saboda sun saba sosai dontafi jin bakin cikin rabuwa dashi akan nusaibawacce suke kwana tare su tashi komai tare hattabacci baya rabasu. Uwar biyu ma sai duk jikintayayi sanyi shi kenan idan ta kai hanna gida baza tadawo ta dauketa ba kuma. Suka isa gidan su hannah, hannah ta shiga gida da sauri tana murnazata ga babanta. A shimfidarsa a zaure ta ganshikwance sharkab babu lafiya ashe watansa wajenhudu a haka. Ciwo kullum gaba yake sake yi saiakwantar a tayar. Hannah ta gigice har tana nemanrasa hankalinta yayin da taga mahaifinta ya zama kashi a kwance kurket dashi kaninsa ne uwa dayauba daya yazo yana jinyarsa . Dan ta iya abu cewatayi ya mutu mana tace ta gaji da zaman jinya tundayaki warkewa tayi na allah 'yan uwansa kuma suzosuci gaba da kula dashi ita ta huta. Hannah tasakuka taje ta tsugunna a gabansa tace'' sannu baba'' yace'' yauwa sannu 'yar baba ashe da rabonkizo muyi magana ban mutu ba nace aje a kirawomin ke a makarantar kizo kiga gawar mahaifinkibasu je ba'' cikin sheshshekar kuka hanna tace''baza ka mutu ba baba daina fada ma'' uwar biyuma ta matso kusa dashi tace'' sannu malam habu ya jikin ''yace'' jiki dai gashinan uwar biyu sai dai kuyimin addu'a idan na mutu, allah ya saka miki daalheri ke da haisam da gidan aljannah abundakuka yiwa hanne na gode''uwar biyu ma hawayetake yi. Hanna tayi kuka kamar ranta zai fita. Ananuwar biyu ta yini sai da la'asar tace zata tafi suka yi sallama da malam habu dake radai yana maganatashi tsaye ne baya iya yi. Hannah ta rakata hartasha.A hanya Uwar biyutakebawa Hannah shawara ta ce "Tun da ke mai ilimice kiyiamfani da iliminki, ki kai Mahaifinki asibitin Baburatunda kudin da Haisam ya bawa Mahaifinki dawandaya baki mai tsokane zai isheku. Da abarshi a gidaanamasa jike-jike duk wata cuta ake kara masa.Mutum akwance har wata hudu ya kare sai kashi da fata. Atashar Uwar biyu ta sami mai mota aka yi tsadazata jegida a dauko marar lafiya a kaishi asibiti. HannahdaUwar biyu suka shiga mota, dake itama Uwar biyudaman motar Babura zata shiga daga Babura zatahauta Gumel. Sai kawai su duk su tafi tare. Motar tajeharkofar gidan, direban da kwandasta da kanin MalamHabu suka ciccibeshi suka sashi a mota sukashigasuma da *yan kayayyakinsu suka nufi asibitinBabura.Iya Abu nata yiwa Hannah surutu tana cewa gatananUwar iya yi wai har tayi kilin din da zata daukiMahaifinta ta kai asibiti wai har asibitin Babura tazama *yar boko. Sai da Uwar biyu tayi wata gudacur aGumel sannan ta dawo Kazaure tana zuwa tananiyyarta shaidawa Haisam halin da Mahaifin Hannah kecikisai aka ce mata ai bayan tafiyar su Hannah da satibiyushima ya bar koyarwar ya kwashe kayansa yakomaKano. Ta nemi Safiyanu shima aka ce mata ai shitundayayi aure a Kaduna ya tare da sabuwar amaryarsaacan ya sami aiki, sai Uwar biyu ta hakura dasanarwaHaisam don ita bata taba zuwa Kano bama balleta tafinemansa. Su Hannah kuwa sai da suka shafe wataguda da kwana shida sannan aka sallamesu dagaasibiti. Kanin Mahaifinta ne a wajensa amma itamatakan je tayi kwana biyu uku acan har dai sukadawogida gaba daya. Jiki da sauki tunda yana zama dakansa ba sai an tallafo shi ba. Sai dai kudadenhannunHannah sun kare kakat saboda siyan magungunanasibiti.Nan fa balokokon Iya Abu ya tashi akan tagaHannahbata da kudin da zata sayi dan biskit da madarardatake sha idan tazo hutu da, dole ta ci tuwan gidan.Hannah ce shara, wanke-wanke da dafa abincitukatuwan bakar dawa da miyar kuka a murhun kasa.Kwanci tashi su Hannah sunyi wata biyar da gamamakaranta. Hannah har ta fara zuwa makarantarbokongarinsu tana koyarwa. Duk da dai ba'a dauketa amatsayin Malama ba don Jarabawarta bata fitoba.Amma a karshen wata ana bata dan na batarwa.Ranarasabar babu makaranta. Da sassafe bayan Hannahtagama wanke-wanke tana kokarin daura tukunyartuwon burabuskon gero miyar kuka na rana saikawaiIya Abu tazo ta kashe wutar da ruwan tuwon. Tace tacanja ra'ayi yau an fasa yin abincin ranar sabodaunguwa zata ita da jikokinta don haka meyeamfanintuwon. Ta dauke garin tuwon da kukar kadin tasaadaki ta datse ta yafa mayafinta zata fice. RanHannahya baci ta ce "To Baba fa, me zai ci shi da bashidalafiya? Yau jikin nasa a rikice yake tunda sassafeamaiyake. Iya Abu ta ce "Sai yaci hakuri ko ki kwasheamanda yayi ki dumama masa. Cikin fushi Hannah ta ce"Inaraye a duniya Mahaifina ba zaici amai ba inshaAllah"Mari tas Iya Abu ta sakar ma Hannah akanlallasusankuncin nan nata ta ce "Ke kin isa ina fada kinafadalalle wuyanki ya isa yanka. Malam Habu da yakekwance sai jikinsa ya dau kakkarwa tashin hankaliyadira a zuciyarsa yaji marin da aka sakarwa Hannesaiya hau hawaye yana kira "Yar Baba yi hakuri zonanwajena ki zauna. Hannah tana hawaye ta je gefenshinfidarsa ta zauna Iya Abu tana tsaye akansutana tabalokokonta tayi har ta gaji ta kama hannunjikokintasuka fice, da taji ba'a kulata ba. Zuwa can wanilokacimai dan tsawo Hannah da Mahaifinta sunyi zugumsuna tunani sai ta jiyo mai tallar fura da nono tazotazo wucewa, da sauran *ayan canji a jakarta tatashita leka ta kirawota, ta dauko kwanon sha ta saya.Tadama ta tashi Mahaifinta zaune ta bashi yasha yakoshisannan ta gyara masa kwanciyar ya kwanta takomagefensa ta zauna tayi lamo zuciyarta cike datakaici gayunwa tana addabar cikinta. Can Malam Habu yace"Yar Baba, ta ce "Na'am Baba. Ya ce "Allah Yayimikialbarka ya baki miji na gari mai sonki kamarHaisam,sai Hannah tayi shiru tana tunani da mamaki yaakayiMahaifinta yake hada mijinta da Haisam.Malam Habu ya ce "Ya ba ki amsa ba? Ta ce"Babakamar Haisam kuma? Ya ce "Eh kamar yadda yakekuladake yake nuna miki kauna. Tayi murmushi ta ce"Mutunci ne dashi da tausayi amma ba soyayyabace.Malam Habu yayi dan tari ya ce "*yar Baba matsokusadani kiji. Hannah ta matso kusa dashi. Ya ce "YarBabababu mai sonki a duniyar nan kamar Haisam, babumairikeki tsakani da Allah irin Haisam, babu mai rikekiamana ko bayan raina wanda ko dar bana yi saishi*yar Baba. Haisam yana matukar sonki. Hannah tace"Meka gani kake cewa haka? Ba sona yake ba kokadanmutunci ne ai bai taba gaya mun ba. Malam Habuyanisa ya ce "Yanzu tashi kije ki nemi gidansu aKanokice na amince masa ya zo zan bashi ke ya aureki.Hannah ta zabura ta ce "A'a Baba ya za'ayi injekawaiince masa ka yarda yazo ya aure ni bayan bai cezaiaureni ba. Malam Habu ya ce bakya

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});