Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 30

Chapter 30

Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ke tsaye sai tasa gyale tarufe fuskarta. Ya karaso inda take a tsaye yayi matasallama ta make murya ta amsa. Yace wacece? Hanna ta sake make murya tace bakuwa ce''haisam ya hada girar sama data kasa yace'' wai kewacece in ba zaki fada ba zan koma ina da abunyi''hanna ta yaye mayafin a hankali ta bude fuskarta.Wai, kamar wanii hasken walkiya ne ya haskewahaisam ido da yaga fuskar hanna ,cikin fara'a da mamaki haisam yace hanna! hanna! Kece!! Tayilallausan murmushi tace'' yaya haisam nice'' taduka ta gaisheshi. Taga haisam ya caba ado dawata babbar riga mai aiki a wata tsadaddiyarshadda fara sol yasa bakin takalmi da bakar hulayayi matukar kyau. Tayi dariya tace''yaya haisam yau kaine da babbar riga ? Har kafi kyau haka'.Yace haba? Tace allah'' yace yaya su baba. Dasauran yan gidanku? Tace sunanan lafiya sunce nagaisheku. Yace to zaki shiga cikin gida ku gaisadasu hajiya'' hanna ta dan yatsune fuska tace'' kaisai dai watarab bi kunya nake ji kuma sauri nake sai dai idan na dawo. Yace daman ba nan kikazobane? Hanna tace ''ni kuwa wa gareni a kanoidan ba kai ba? Gurinka nazo baba ya aikonihaisam yace to gani fada min aiken. Zumudin yajiabunda aka aiko ta ya kama haisam. Tayi shiru tahau rufe fuska. Cikin zumudi haisam yace'' haba hanna ki fada mun mana kunyar me kike ji ne?Tace'' baba ne yace inzo in fada maka cewar kazoka nemi aurena ta bakani. Tu kafin ta karasa saitaga haisam ya fara dariya da alama farin ciki yacika zuciyarsa. Ya kurawa hannah ido na wani danlokaci yqce'' abunda kika kasa fada daman? Ya sake yin dariya ya tsaya kallan hanna wacce takerufe idanuwanta saboda kunya ga tsananin farinciki.Haisam ya nisa yace''yanzu baba da kansa yacekizo ki cemun ya bani ke! Hanna ta amsa da''eh''yace yanzu ya bani ke kacokan a matsayinmatata? Yanzu baba ya yarda ki zama uwar yayanamun zama daya dangina sun zama danginki,iyayena sun zama iyayenki? Yanzu baba ya yarda na zama abokin rayuwarki na dindindan har abada? Yanzuhanna kin amince zaki zama abokiyar zamana harabada? Hanna cike da fara.a da murmushi takeamsawa haisam tambayoyinsa da ''eh'' haisam yayimurmushi ya sunkuyar da kai na dan wani lokacican ya dago ya kurawa hanna ido yayin da kowannensu yake sakarwa dan uwansa murmushida wasu masun kauna da suke firfitowa dagaidanuwan kowannensu suna yiwa junansu wanikallo mai kunshe da so, kauna muradi ganin juna.Haisam yayi ajiyar zuciya ya nisa ya ce alhamdulillahhanna na daukarwa allah alkawari ba xika , sannan na cika burina dana kudira akanki na ingakin kammala karatunki. Kuma yanzu na dawo gidazan cika wani tsohon alkawari dana dauka. Nan danan hanna ta kurawa haisam ido ta dainamurmushin da take alamar bata gane abundahaisam yake cewa ba. Haisam ya ce'' hanna na gode madalla , ki yimun godiya a wajen mahaifinki .Good bye, good bye hanna. Ya fara jada baya yanadaga mata hannu yana yi mata murmushi . Bakintaya hau rawa tana so tayi magana ta kasa . Gabadaya jikinta ya hau karkarwa inda jakar dakerataye a kafadrta ta sulmiyo wasu marokane suka wayar mata dakai akan abunda haisam yake nufisuna cewa'' ango haisam kasha kamshi fari maifarar aniya kagaa ango na ramla, yan boko bayinnasara a daura aure lafiya akai maka amarya gidalafiya. Wani abokinsa ne ya taho da sauri yace dahaisam ''ana ta yin waya daga wajen daurin aure ance waje ya cika kai ango kawai ake jira.muje ka shiga nota mu tafi mana. Haisam daabokansa suka shiga tsala tsalan motocinsu sukazo suka wuce hannah anan a tsaye tana karkarwaido da ido suke hadawa da haisam har suka wucesuka tafi. Ta juya tabi motar da kallo har suka hautiti suka kure. Sai hanna ta tsugunna a wajen ta rushe da wana azababben kuka mai radadin fita.Dakyar buzu mai gadin nan ya dinga bata hakuri tadauki jakarta dankwalinta a hannu sai gyalenta tayafa a kai ta tafi. Acaba ta hau har tashar yan kurawannan karon ma taci sa.a tana shiga mota ta cika .Kallo daya zaka yiwa hanna kasan hankalinta a tashe yake matuka don kwandasta sai da yayimagana sau uku yana cewa ta bada kudin motartabata jiba, hankalinta yana can tana tunanin damanhaisam ba sonta take ba. Ramla yake so shine ita damahaifinta suke yaudarar kansu . Yaya haisam meyasa kayi min haka me yasa baka fahimci son dana ke yi maka ba ? Ta nisa tace'' ko da yake bashi dalaifi bai yaudare ni ba, ya taimakkamin ne sabodaallah ni na dorawa rai sonsa. Bai san ina yi bakuma, amma na rabu da farin cikin rayuwa na rasamutum na farko dana taba hi inaso a rayuwata,gashi tun bayan gama makarantarmu ko bacci ma neman gagarata yake na kwallafa raina datunaninsa da tsananin sonsa'' sai da wata mata takusa da ita ta tattabta sannan hannah ta farfadodaga tunaninda take yi. Kwandasta yace kudinmota nake tambayarki kinyi shiru kina tunani''sannan hanna ta zabura ta dauko kudin mota ta mika. Mota ta bar cikin kano ta kama hanya fetal saibabban mutum. suna isa babban mutum tun dagatasha hanna ta dinga jin faduwar gaba kafartakamar bazata iya daukar ta ba dakyar take jefakafar burinta kawai ta isa gida taje ta fada jikinmahaifinta ta sharbi kukanta son ranta tunda duk duniya shine kadai ya rage mata gaba dabaya.kamar yadda data shiga kano taga mutanengarin suna ta kallonta har da waiwaye yanzu ma agarinsu haka ta gani sai kallonta ake tana tafiya harda masu nunata kamar basu santa daba, hanna tayimamakin irin wannan kallo da ake yi mat tace a ranta'' to ko sun san son maso wani nake ? Wandanake so yayi aurensa da wacce yake so'' kallon nandai da ake yi mata ya daure mata kai. Haka daihanna taci gaba da tafiya tana sauri ta karasa wajenmahaifinta shine kadai mai lallashinta, mai gayamata kalaman da zata ji dan sanyi a ranta. Ta kusa kofar gidansu, kwatsam taga wata kungiyar mazadauke da gawa sun yi gabas ana hailala. Tajigabanta ya fadi ta dubi kofar gidansu sai taga taronwadansu maza da yara a zazzaune ana jan carbitace a ranta'' ba dai gawar babana bace waccan?Sai ta zubar da takalmanta da jakarta ta shiga gida da gudu don ta duba zaure shinfidar babanta yananan kuwa. Tana shiga sai taga shimfidar wayambaya na ga silifas dinsa da butarsa a gefe babandaki ya zaga ba. Ga wannan furarsa gefesauran wacce ta dama masa yasha ya rage. Nan danan taga su iya salmai sun fito daga cikin gida suna rusa kuka idonsu yayi jawur suna riketa suna cewasannu hanna wannan ke aka yiwa mutuwa allah yajikan mahaifinki da sunanki a bakinsa har ya mutu.sai wani jiri ta kwashi hanna ta fada kanshimfidarsa ta rirrike filonsa ta kudindine ta runtseido ji take dama kasa ta bude ta fada da ita bakin cikin rayuwa ya isheta. Ta kwalla kara tana karacewa'' innalillahi waina ilaihi raju'un allah kanasane dani, allah ka san halin dana ke ciki. Allahbaka tsaneniba, baka kuma manta dani ba. Bani dakowa a duniya, babu wanda ya ragemin kumaallah kaine gatana kai ka halicceni, ka halicci mahaifina kuma ka halicci haisam. Ka hadani dasumuka saba kuma kai ka raba ni dasu allah. Allahkaine abun godiya. Allah na gode maka. Allahkaine jagorana, allah kar ka barni na dauwama acikin bakin ciki. Allahu akbar sai

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});