Chapter 15
Chapter 15
ya hau cewa gaskiya tawace wannan.Wancan na cewa na rigaka. Kawayenta da yawasun kudiri niyyar suma sai sun tuburewa iyayensuan kaisu makarantar kwana irin ta hannah donsuma su goge suyi jawur haka. Kafin hanne takarasa gida labari ya kai cikin gidansu ance ga hanne nan zuwa ta zama fara kal kamar baturiya itada wata tsohuwa. Farin ciki ya rufe mahaifinta yaiwuf ya fito kofar gida ya tsaya yana murna yanajiran isowar hannensa(yar boko). Budar bakin iyaabu kuwa sai cewa tayi watakila ciki aka yi mata amakarantar tayi haske don hanne ba fara ba ce kal. Surutai dai na hassada da bakin ciki barkatai tadinga yi.Hanne na doso kofar gida ta hango mahaifintasai su duka murna ta lullubesu. Hannah ta karisa dasauri taje ta rungumeshi kamar yadda taga sunusaiba suna yima mahaifansu sai hawaye suke itada mahaifinta. Iya abu a tsakar gida ita da yayantababu wanda ya amsawa uwar biyu sallamarta da tayi, sai malam habu yace shigo kawai ai ba zasuamsa muki ba'' ya shiga daki ya dauko tabarma dasauri ya shimafida mata ta zauna a sanyaye cike damamaki irin wannan tsana da ake yiwa wannan yarkaramar yarinya wanda ma yake sonta an tsaneshi.Hannah taje gaban iya abu ta durkusa ta gaisheta ko ta amsa ta juya ta gaishe da yayyenta 'ya'yan iyaabu kenan suma suka kwata abunda mahaifiyarsutayi. uwar biyu ta rike baki tace ''oh ikon allah bayinallah me yayi zafi hannah nawa take ? Don allahkuyi mata yar fara'a mana ko taji dan sanyi yanzuko dokinta bakwa yi kusan wata biyu bata nan, aidarajar sabon idon ni bakuwa kwa raga mata harin tafi'' suka yo ca akan uwar biyu uwar biyu nayi yayan nayi, ta mike tsaye ta juya ta kalli hannahwacce ta kame a jikin katanga tana makyarkyatahawaye ne ke zuba daga idanuwanta tasan yauduka da zagi allah ne kadai yasan iyakarsa da zatasha. Hawaye ya kecewa uwar biyu tace'' hannah yihakuri wuya bata kisa ko anki ko anso gidan ubanki ne duk inda kika je sai kinzo gidan dole,''iya abu tace'' gidan uban nata ya gagareta zamaidan naso ba. Malam habu shima yayi jugum yakasa magana tashin hankali ya isheshi sabodayana tausayin hannah yasan wahala zasu ci gabada linka mata ganin allah ya rufa mata asiri tayi kyau, uwar biyu ta fita malam habu ya bita hannahma ta bisu da sauri, uwar biyu tasa gefen gyale tashare hawaye tace'' allah yana nan, malam ni yaraikece. Malam haisam malamin daya karbeta ahannunka din nan. Malam habu ya katseta yace ''ehna gane kiyi mana godiya da kyau da kyau na gode madalla. Tasa hannu a dan tofi ta dauko kudimai dan afki ta bawa malam habu'' inji malamhaisam ya ce a bashi nasa ne na kashin kansa banamakarantar hannah bane. Da zarar hutu ya kare itada kanta zata zo ta dauketa, malam habu yayi shiruyana sauraron uwar biyu sai girgiza kai yake kawai yana mamakin wannan tara ta arziki da haisamyake yi musu yana fadin ashe akwai masu halinsahabba a duniyar nan masu kyautar da dukiyarsuga mabukata irin malam haisam. Malam habu yadago ya kalli uwar biyu yace'' kema daya aikokikika rike amana allah ya saka miki da gidan aljannah dashi da yake mana hidima allah ya bashida mai yi masa haka munji dadi mun gode. Ni inanan wata rana na gaza barci ina tunanin ko yayayar baba, kome take ci a makarabntar na bartababu abinci? Ashe tana cam ta fini koshi, kalliyadda tayi bul bul ah alhamdulillah. Maigari ya aiko da garin kwaki kwano biyu da suga rabin kwanosai kudin motar zuwa kazaure ya ce in kai matamakaranta wallahi matar nan tawa data ga garinnan da kudin mota sai ta sulalo ina bacci ta sacekudin motar ta tilla ledar garin ya dinga tsiyayewa akasa, da naje na shaidawa mai gari ba kiga cin mutuncin da suka yimin ba wai daman talauci yaisheni na sami kayan gwamnati ina wadaka dashi,su babu ruwansu ya dai ya ta ce in barta yunwar takasheta. Nayi kuka da hawaye nazo na zauna nahakura sai addu'a na dinga aikamata daga na allahya hadata da mai bata. Allah ya amsa addu.ata gashi bamu girbe amfanin gona ba shine yasa kotaro nakan tashi babu a aljihuna. Uwar biyu tace,kaico haka kake rayuwa ta malam ? To ni daishawarar dazan baka dan allah dan annabi(S.A.W)duk runtsi duk wuya ka toshe kunnankakome za'ace game da karatun hannah karka cire ta daga makaranta. Babu sisinka. Ba kai zaka dauketaba. Bakai zaka mayar da ita va nice zan dingakawota ina zuwa ina daukarta sai dai ka bata izinikarka hanata saboda karatu ne kawai zai farfadoda hannah ta sami yancinta da jin dadin rayuwartaanan gaba, amma azabar tayi yawa. Malam habu ya ce da gudu kuwa zan barta, aini badan za'ace nasiyar da yata ba, ko ace na kaita birni tana iskancida ko hutu ma sai ince ta dinga yi a gidanki ammayanzu kowa yaji a rediyo an yiwa 'yan makarantahutu ba aga hannah ba za'a fara titsiyeni datambaya a fada. Uwar biyu tace allah ya kyauta ni zan koma, ga sabulai can a jakanta da mayukanshafawa malama haisam ce don allah a dinga bartatana wanka da wanki da kitso ba kamar yadda akakawota ba, kazan kazan ina amfanin kazanta ?Uwar biyu ta fara tafiya bayan sunyi sallama damalam habu yana ta godiya, hannah ta rushe da kuka ta bi uwar biyu da gudu ta rungumeta suduka kuka suke rusawa hannah tace''uwar biyu karki tafi ki barni wuya bake sha ni zanbiki gidanki in zauna a can. Daya daga cikin 'yayaniya abu musbahu shine ya fito daga cikin gidan aguje uwarsa ta turo shi yazo ya dauko mata hannah aka dake suna labe a zaure suna jin dukmaganganun da suke yi. Ya dauko ta aka ya mikata cikin gida ya rufo kofar zaure sai kukan hannahne yake tashi ya cika unguwar kai kace rai ake zaremata saboda irin karar kukan daga ji ba karaminbudu ake yi mata ba, malam habu nata kokarin bude kofar yana bugun kofar kamar zai balla yanaso yaje ya ceci 'yarsa uwar biyu ta juya ta tafi tanarusa kuka kamar ranta zai fita, tsananin bakin cikida tausayin hannah ne ya cika mata zuciya. Tana jinsamarin dake zazzaune akan benci suna jiyo kukanhannah suke cewa''to baiwar iya abu tazo har an fara nada mata dukar kai wannan yarinya allah daiya rayata kar itama wuya ta kasheta kamar uwarta.Haka hannah tayi ta zama cikin wahala da kuncida azabtarwan iya abu har hutun makaranta yakare. Ana saura kwana biyu a koma sai ga uwarbiyu tazo daukan hanne. Tunda iya abu ta ganka tahau fada ta inda take shiga ba ta nan take fita ba,anan ne malam habu yake fada mata , kinsan cewa tayi indai da ranta hanne ta daina karatu tundawata gulma aka hada na kaita gidan yan gayubabu wata makaranta. Wuf iya abu tayi tayo wajedaga cikin daki tazo ta tsaya a dokin kofa tanagirgiza ta kama kugu tana kallon uwar biyu ayatsune. Babu abunda uwar biyu take sai kallon wuyan iya abu galleliyar sarkar jiyal din da tasiyawa hanne ce a wuyanta. Muhajana 'yarta kuwariga da siket 'yar kanti ta hanne ce a jikinta, saigamusbahu shima yazo ya wuce da jakar hanne arataye a bayansa (school bag)wai daga kasuwayake. Iya abu tace'' bai gaya miki ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31