Chapter 26
Chapter 26
ta shimfida musu sukazazzauna ta koma ta dauko musu ruwa a randacikin kwanan sha. Ta kawo ta durkusa kasa tagaishe su ta koma gefe ta zauna. Murna ce ta rufe malam habu yama rasa inda zaisa wadannanmanyan baki, yan gayu, ya lalubo kudi a aljihunsaya ce da hannah tayi maza taje bakin kasuwa tasuyo musu fura da nono, su haisam suka ce kaihaba ai su a koshe suke ya barshi kawai. Bayansun gaggaisa malam habu ya gama yi musu sannu da zuwab da tako kare sai safiyanu ya nisayace''baba munzo ne mu ba da hakuri akan dalilinda yasa ka hana hanna zuwa makaranta. Shinemuka zo da kammu mu roke ka baba duka dukasaura wata nawa ne yanzu hanna zata gamakaratunta ta dawo gida'' nan da nan malam habu ya canja fuskar fara'ar dayake ta gushe yace''wai me yasa kuke sani inamuku kin kyautatawa ne ? Bana so ku tambayeniabinda zan kasa baku na gama magana don allahdon annabi ku bar zancen karatun 'yar baba. Nayanke shawara ba zata koma ba. Haisam kokarin da yake yi allah ya saka maka hakan ma ya isa basai ta kara yin wasu watannin ba. Nace uwar biyuta yi maka godiya ka cika min alkawarin da kadauka wallahi ko bata karasa ba ai ka cika alkawariba laifinka bane. Alkawari da amana ai ba karaminaiki bane cika su amma cikin yardar allah ka cika dai dai ubangiji ya saka maka da gidan aljanna.Amma hanna ba zan bari ta koma ba. Haisam yayidan murmushi game da gyaran murya ya ce'' aminbaba, amma idan baka manta ba a ranar dana karbiamanar hanna nayi alkawarin hanna zata yi karatuto kai ma a lokacin kayi min alkawari,kaga alkawari girma ne de dashi baka cika ba, kayi min alkawarinzaka bar hanna tayi karatun don sai dama nasakayi alkawarin zaka dinga turo hanna makarantabaza ka hana ta ba wataran sannan nayi makaalkawarina. Malam habu yayi shiru zuwa wani danlokaci can ya nisa yace'' anyi haka yaro haka akayi nayi maka alkawari to ammma ai abinda yarinyarnan tace gargadi fa tayi min akan kada in kara tura'yata makarantar nan kaga ai kome tayi mata batada laifi nine ban ji ba kenan'' haisam ya katseshiyace'' kare lafiyar hanna da duk wani abinda zaicuce ta yana daga cikin amanar dana dauka in allah yaso babu mai yiwa hanna wani abu. Ramla kuwata fada ne kawai a cikin bacin rai amma babuabinda zata yiwa hanna, a ina ma zata ganta balletayi mata wani abu ? Ta dai fadi son ranta dontatsorataka kaga baba kuma abinda ta fada ba hakabane hanna karatu take haikan a makaranta, kanwa ce hanna a wajena ni ne mai tsawatar matama misali da ace tana soyayya da samari amakarantar . Baba mu canfa akwai doka babuyadda za'ayi malami yayi soyayya da daliba, babukuma yadda za'ayi wata ya shigo cikin makarantardauke da wata guba taje ta cuci dalibai don haka baba ka kwantar da hankalinka ni da kai duk mucika alkawuran da muka daukarwa allah''.Malam habu yace ''to shikenan allah ya taya mucikawa. Hanna dauko kayanki ku tafi allah yakiyaye hanya''suka duka suka ce amin''sai murnata dira a zukatansu. Cikin farin ciki da jin dadihanna ta shiga ta fara hado kayanta ,iya abu tayicaraf ta fito daga bayan kyauren da take labe ta hau malam habu da fada'' au yarda kayi dawannan dadin bakin da suka yi maka. Duk wannangaskiyar data baiyana yarinya iskanci suke amakarantar don yana aiko maka dana goro shinekaki fadar allah saboda abun duniya ? Kallo dayahaisam yayi mata yaga irin wadannan mutane ne masu abun haushi masu kama da aljanu munanamasu bakin hali yaji ya tsani iya abu har baya so yakara kallon fuskar shegiya. Hannah ta ratayajakarta ta fito ko kallon iya abu bata yi ba balle tayimata sallama. Ta duka ta yiwa babanta godiya tayimasa sallama ta wuce cikin mota. Haisam ya danko kudo mai yawa ya ajiye a gaban malam habu.Safiyanu ma haka ya debo kudi ta ajiye masa sukayi masa sallama dukkaninsu yana godiya sunagodiya suka shiga mota suka tafi. Ba safiyanu bahar haisam yaji ya sake tausaya rayuwar hannasaboda ganin yadda gidansu yake. Gidan kasa ne anyi masa katanga da kara rufin azara abin dai abintausayi talauci dai tsagwaransa. Babu abinda zakadaga a gidan ka sayar dashi dari biyar komai ragaraga kaico!hannah na komawa makaranta tasalittafinta a gaba tahau karatu. Sune yanzu masushirin zana s.s.c.e don haka babu wasa sai karatu. kwance tashi su hannah sun fara jarabawarsu takarshe [s.s.c.e} saboda daman tuni sun gamatsarge karatu. Sai suka ga cin tuwo yafi jarabawarwuya sai kawai suka hau fede ta. Geography dinmalam haisam itace wacce suka yi ta karshe damisalin karfe hudu na yamma suka gama daman jakunkunansu su suna baki hall din da sukejarabawar suna fitowa sai kowacce ta dauki jakartasai tafiya daman kowacce ta kagu taje gida taga'yan gidansu basu taba irin wannna dadewa amakarantar ba har watanni bakwai a makaranta.Hatta hanna da bata so ayi hutu itama yanzu so taje gidq taga mahaifinta sai mafarkinsa take kullum takwanta barci. Hanna da kawayenta sun sha kukanrabuwa musamman ita da nusaiba sun saba sosaigashi zasu rabu. Gashi kuma babu waya a garinsuhanna balle su dinga gaisawa a waya. Rauda ma tarungume hanna tana kuka taji duk babu dadi yanzu da zasu rabu kuka wiwi juniors suke yi narabuwa da seniors dinsu zasu tafi su barsumusamman hanna basu ji dadin rabuwa da ita basaboda tayi musu mutunci samun shugabar dalibaiirin hanna sai an bincika. Ta koya musu abubuwana cikin kungiyoyinsu {club}na makarantar. A haka kowacce ta tafi gida kuka wiwi. Safiyanu ne yazo yadauki hanna ya kaita gidan uwar biyu. Yau haisamtun kafin su shiga jarabawa yazo yayi musu sallamaya koma gidansa ya rufe kansa kansa ko wajen daake bankwana bai zo ba saboda tsananin bakincikin rabuwa da yan ajinsa da yake matukar so. Gidan uwar biyu ma sai washe gari yaje ya samuhanna a can. Bayan sun gaisa ya ce da hannah''yau zaki tafi gida ko sai kin sake hutawa kamar satidaya anan sannan ki tafi ? Hannah tayi caraf tace''yaya haisam yau zan tafi na dade banga babanaba'' haisam yayi dariya ya ce'' wato ke yanzu kin bar kazaure kenan zaman kazaure sai mu ? Tayidariya tace'' sai ku ai mun daku wannan hutun harna daina sha'awar garin allah yaya haisam'' haisamya mike ya ce'' to ki shirya zanje nan makwabtasafiyanu yana ciki wajen abokansa ana wankemasa motar ana gamawa sai ku fito zan aiko yaro yayi kiranku sai mu kaiku tasha ku tafi. Da har cangarin zamu kaiku inyiwa baba godiya ince masagaki na dawo masa dake lafiya na cika alkawarishima ya cika to sai safiyanu ya ce kano zai tafi dakakarsa in anjima'' hanna tayi dariya tace'' kai yaahaisam ai babu komai yana gani na yasan lafiya na dawo lallai kuwa ka cika alkawari'' ya juyo yakalleta yace ''ko? Tayi murmushi tace'' E'' sannan yafita yana murmushi. Bayan fitarsa da dadewa sosaiyaro ya shigo ya ce wai uwar biyu da hanna su fitoinji su safiyanu suna kofar gidan dallatu'' daman ashirye suke tsaf sai hannah ta dorawa yaron jifgegiyar jakar kayanta. Jakunkuna uku ne. Yakaiya dawo ya dauki ta biyu sannan yazo ya dauki takarshe sannan suka fito uwar biyu ma da buhuntaa kanta, suka shiga mota sai tashar kazaure.Hannah
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31