Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Complete Hausa Novel 1,213 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

santsin gaskebaki wullik mai tsawo sosai wanda yake taba doron bayanta. Amma me ? Yayi datti. Kura, amosalikai kace dambe tayi aka tumurmusa kan a cikinyashi . Sai wani kitso tuma tuma guda biyu dagagani ita tayi da kanta. Uwar biyu tace'' la la hannehaka kanki yake ? Amma kinyi wasa a yashi ko ?Gaki da gashi tubar kalla baki san yan mata yanzu ido rufe suke neman gashi ba. Da kudinsu ma siyasuke su kara yaya kika bar kanki haka babugyara ? Hanne tayi shiru kanta a sunkuye a kasatana kokarin daura dan kwalinta. Haisam wandayake zaune yayi shiru sai girgiza kai alamantausayi. Can ya nisa yace'' uwar biyu yanzu dai abunda za.a yi ga wannan wasu kudi ne ya sakecunkusowa daga aljihunsa ya mika mata tace'' nameye wannan kuma? Ya ce'' ina ganin hanne nabukatar abubuwa da yawa a kwana biyu da zatayigidanki . Ki tsaya a aishalle super market kitattambayi masu wajen irin man wanke gashi, dana kitso da sabulun wanka, wanki, abun goge kafa kisiya mata silifas. Ki duba kan idan akwaikwarkwata ki sayi shaltos duk a fesa su mutu. Kozaki taho aiki gobe to ki sami wata ki biya ta waccezata gyara mata kannan tayi mata kitso. Kai harmawanka kuyi mata da kanku ai bata wuce ayi mata wankan bama'' uwar biyu tace'' in allah yaso yaudin nan kafin mu kwanta da kaina zan gyaratagobe kuma ko zan taho aiki da diyata halima tananan auren ya mutu tana gida sai in barta da ita.Kuma ta iya kitso kala kala sana'arta kenan ki agarin da tayi aure'' haisam yace to nima gobe wajen karfe biyu idan an tashi a makaranta akwai tela dazamu je dashi can gidan naki ya auno ta zai dinkamata kayan makaranta(uniform)sai ki kwatantamin gidanki don naje. A kanti kike ko cikin gari ?Uwar biyu tace'' ah a cikin gari nake. Idan kajefada, kofar gidan sarki daga hannunkan a dama zaka ga titi ya mike to kabi shi kace a nuna makagidan dalhatun kazaure alhaji hamisu to lyngun mudaya ko a gidan kace gidan uwar biyu kake nemayaro karami zai nuna maka dan mu muke yi mususurfe, katangar gidanmu daya'' haisam yace'' toshike nan yanzu k dauki wannan kayan ku kai store din kicin ki ajiye su sai nan da kwana biyuidan anyo siyayya sai a dauko a zuba, sannankuma abinda nake so dake bana son ki gayawasauran abokan aikin ki ga dalilin da yasa zata jegidanki da sauransu. Ko a cikin gari ma kiyi gum dabakinki kinsan jama.a da surutu za.a yi ta cewa an kawo yar kauye makaranta babu komai sai dauwar biyu takai gidanta wani malami ne yayi matasiyayya da dai sauransu. Ba wai nace kin cikasurutu ba ko gulma a'a ko mutum daya yaji saidubu sunji. Kuma ai akwai matan kicin da yawa damuke gaisawa amma dana ga alamun suna da yawan magana ai ban kira su na basu amana bako ? To yadda tasa nace ta kira uwar biyu'' uwarbiyu ta kyalkyale da dariya dadi ya lullubeta '' tacehakane malam haisam ni dana ke cikinsu yangulma ko sun tambayeni ni nasan me zn fadamusu'' haisam yace'' yauwa ku dauki akwati da bokiti da katifar kamar yadda nace akai store aajiye, sai da safe'' suka ce allah ya kaimu''uwar biyuta kama akwati ta dora akan hanne ta dauki bokiti,da katifa a daya hannun suka doshi store din kicininda suma suke boye shirginsu . Malam haisamkuma ya rataya jakarsa ya nufi gidajen malamai (staff qurters). Zuciyarsa cike da tausayin yaddarayuwar hanne take. Kuma da burin canza matanan gaba* * * * HAISAM ABDULHAMID ZAKAR Sunanmahaifinsa ne abdulhamid zakar. Mahaifiyarsakuma sunanta NANA HAUWA'U Wacce a yanzu akafi saninta da hajiya nana ko kuma barista nana kasancewarta kwararriyar lauya ce. Mahaifinhaisam haifaffun unguwar kwalli ne a kano. Kumasun fito daga tushe daya yar kanwace aka hadasuaure a lokacin alhaji abdulhamid ya gama karatumdigiri dinsa a london yana da shekaru ashirin dabakwai ita kuma hajiya nana ta gama karatun sakandire tana da shekara goma sha shida.Dukkaninsu iyayensu suna da matukar arziki. Donhaka an sakar musu kudi yadda ya kamata antafka musu kerarren gida, motoci an kuma bawaalhaji abdulhamid jari mai tsoka yana juyawa itakuma hajiya nana ta fara karatunta na law a jami'a bayero ta kano. Allah ya albarkacesu da ya'yahudu, uku maza mace daya itace autar. Wacce ahalin yanxu ko yaye ta ba ayi ba karama ce.Babban shine yaya habib yanzu yana da shekaratalatin , mai binsa shine abdulhamid ake kiransa dahaisam yanzu yana shekararsa ashirin da shida mai binsa iziddeen shekarunsa ashirin da uku. Sai daiziddeen ya gama sakandire ya shiga jama'asannan aka yi masa kanwa mai shekara daya anakiranta da amratu.Girma yazowa alhaji abdulhamid da matarsaamma kumakarfi ya tasamma ya'yansa zasu iya kula da dimbindukiyarsada kamfanoninsa yaya habib ya kammala digirinsaa jamia'ar a.b.u ya karanta business admin a yanzu yana aikia kamfaninbabansa shine kuma mai zurga zurga zuwakasashe dabandaban na shige da fice da kayan kamfanonin.Haisam wanda a shekarar nan ya kammala karatun jami'a yakaranta bscgeography yanzu yana bautar kasa a f.g.g.ckazaure da zararya gama kujerarsa ta aiki nanan na jiransa a dayadaga cikin kamfanonin mahaifinsa. Na uku wato izziddenyana shekara tauku (level 3)a jami'ar bayero ta kano yana karatunlaw don yagaji mahaifiyarsa wato barista nana wacce itacebabbar lauyar kamfanonin . Tana kuma farin cikin ganin dayadaga cikin'ya'yanta ya taso gadan gadan da karatun lawwanda a cikin'yan shekaru kalilan zai gama ya zama cikakkenlauya ya canjeta alhaji abdulhamid ya dankawa yaya habibragamaraiki ya koma gida ya zauna yana hutawa sai daiyajekamfanonin fisha yaga yadda aiki yake tafiya yakoma gida.Dan lelen abba da umma wato haisam shine yafikowashagwaba a gidansu ko kuma nace shi akafishagwabawa tunyana kankani. Amma ai izidden ne yakamata yayishagwaba kasancewarsa ya dade yana auta kafin ayi masakanwa ammashi yana gefe tun suna yara haisam ne a kancinyarsabodatsananin biyayya, ladabi , tausayi da jinkai irin nahaisam shine ya kara masa fada a wajen mahaifansa sunfisha'awarsu zauna suyi hira da haisam sau dubu da suyi fayayansahabib tun suna yara saboda haisam yake magana acikin nutsuwa yake kalamansa masu muhimmanci akoda yaushefuskarsa cike da annuri(fara'a),wasa da dariya damanya dayara. Bashi da raini ga hakuri , baya ga zunzurutunkokari da allah ya bashi a bangaren karatunsa dukka akur'ani da bokonyasan alkur'ani kamar me a kansa duk gidansubabu maiiliminsa. Hatta mahaifinsa yakan yi masa tambayoyiakan duk wata matsalarsu ta addini ko ta zamani, yana datsananinhakuri sau tari ana masa abu da yawa yayi hakuri.Ammakuma duk gidansu babu mai zuciya kamarsa idanaka kureshi, idan yayi fushi abin babu kyau mai hakuri bai iyabacin rai ba.Da farko a enugu state aka turashi bautar kasa(n.y.s.c) kasancewar shakuwa da sabon da mahaifinsasuka yi dashi basa so yayi musu nisa don haka alhaji abdulhamidyasa adawo dashi kurkusa saboda yasan manya manyakasar nandaga yan boko har rukakkun yan kasuwa. Ammaduk da haka haisam yana korafi shifa kazaure yayi nisa da kanoa dawodashi cikin kano inda kullum zaina kwana gida, dakyar dai akalallasheshi yayi hakuri duka duka bazai yi shekaradaya ba zai gama ya dawo gida gaba daya. Don haka dukjuma'a yaketafiya gida wani lokaci ma a kanon yake yin sallarjuma'a sailahadi da yamma ake dawo wa dashi. Gashi yanzuma baifi saura wata uku ba ya kare bautar kasa kwatakwata ma yakoma daya ke muradi.Bayan tafiyar hanne gidan uwar

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});