Chapter 13
Chapter 13
yi. Nusaiba ta ruko hannunmahaifinta ta nufo wajen da malam haisam dahannah suke zaune su duka suka mike dongirmamawa. Nusaiba tace, ga class master mu danake baku labarinsa a wasika nace shi yake kula damu uncle haisam sunansa. Alh idris yayi dariyayace. Oh uncle haisam duk wasikun nusaiba sai tarubuto mana labarinka da kai da kawayentahannah da rauda. Haisam yayi murmushi yace allahsarki ai ga kawarta hannah , hannah ta duka tagaishe shi ya mikawa haisam hannu suka gaisa. Nusaiba tace'' baba daga wannan hutun unclehaisam ba zai dawo ba. Alhaji idris ya ce da haisam''ai dama teaching practice kake yi ananmakarantar ? Haisam yace ''eh bautar kasa(N.Y.S.C)nayi kuma mun gama. Alhaji idris yace badadi yara sun saba da kai gashi zaka tafi, mun gode allah ya saka da alheri. Haisam ya ce '' ba komai aikannena ne.nusaiba ta ciro takarda daga jakarta dabiro ta mikawa haisam tace ya rubuta mata lambarwayar sa. Ya karba ya rubuta mata. Ta karba tamikawa hannah tace '' hannah rubuta min lambarwayar ki a kasan ta uncle haisam'' hannah tayi turus ita bata taba taba wayar bama balle ta sanyadda ake amfani da ita har ta san wata lamba.Haisam yayi sauri ya ce a'a ke rubuta mata taki zatakiraki. Nusaiba ta rubuta lambar wayarta ta mikawahannah, hannah ta karba. Daga karshe hannah takamawa nusaiba jakarta suka nufi wajen mota. Alhaji idris ya bude but haisam ya kama ya saka.Nusaiba ta rungume hannah su duka sunahawaye. Nusaiba tace'' kina zuwa gida ki kirani awaya kuma kullum zamu dinga waya munagaisawa. Alhaji idris ya dafa kansu ya ce '' ku dainakuka hutu za kuje yana karewa zaku dawo ai baku rabu ba gaba daya. Nusaiba da mahaifinta sukashiga mita ya ja suka tafi hannah da haisam sunadaga musu hannu har suka kure sannan sukakoma inda suke zaune da suka zauna. Sai gacincirindon dalibai suka zo suka zagaye haisamkowacce na baiyana rashin jin dadinta game da barin makarantar da zai yi, haisam ya baiyana musucewa in allah ya yarda duk term zai dinga zuwayana ganin su. A haka suka dai suka dinga wasada dariya kamar yadda suka saba rauda ma takaraso wajen ta zauna a hirar da ita basu lura dasanda motar gidan su ta shigo ba, sai kawai suka hango auwal wan rauda ya tinkaro su. Rauda tamike da gudu taje ta rungume yayanta, yanakarasowa ya mikawa haisam hannu suka kashe yace'' malam ,malam haka kake sa daliban naka agaba kuna rera hira ? Haisam yayi murmushi ya ce''bankwana muke yi kasan daga yau shikenan bazan dawo ba'' auwal ya ce wai har kun gamabautar kasar haisam yace ''kwarai kuwa ba famanake da kai ba kazo ka dinga yi mana dan kwanabiyu ma kaki to gashi nima allah yayi min komawagida gaba daya mun zama daya. Ya ce'' lallaishekara kwana ce kamar yaune muka kawoka kamar kayi kuka baka san kauye. Haisam yatuntsire da dariya ya ce'' gashi kuwa na saba yanzuhar bana jin dadi zamu rabu da dalibaina, nan daiauwal ya sami kujera ya zauna shima dake gwaninwasa da dariya ne da mutane ya dinga hira dadaliban nan yana zolayarsu dakyar haisam ya banbaro shi daga wajen daliban nan, auwal dazolaya ya sami yara yana ta zolayarsu musammanhannah, duk da ma baisan yadda take da haisamba yana tayi mata wasa wai ita balarabiya ce takoya masa yarensu yana tambayarta me ake cewayaro da larabci? Tayi dariya tace ban sani va shi a tunaninsa taki fada be kawai baisan ita babalarabiya ba ce. Auwal ya mike ya ce da daliban to ragowar kwakida kanzo na tafi tunda kun zama yan kwantai ba'azo daukar ku ba. Ya kallo hannah ya ce'' ke yaryemen jirgin kasarku baizo ba kema mun tafi munbarki sai kinfi kowa kwantai saboda ke ba yar kasaba ce. Hannah ta kyalkyale da dariya sauran dalibai suka ce'' mu bama cin kwaki bamu san ma yaddakanzo yake ba allahnya sawake kuma mumayanxun nan za'a zo daukar mu. Haka wasa dadariya aka dinga yi da auwal da su hannah haisamna gefe yana kallon yana dariya yace'' da hannahkema dauko jakarki kizo mu tafi na riga na muki signing ke da rauda mu tafi kawai. Auwal ya ce dahannah ''ah ke da nace sai kinfi kowa kwantai ashetare zamu tafi dake ko a filin jirgi zamu ajiyeki ne akano ? hannah tayi dariya tace ''oho ni dai banyikwantai ba'' haisam ya dauki jakar rayda cimaksaboda nauyi ba zata iya dauka va ya kai ya saka a mota.Auwal ya ce da hannah'' kawo kema in taya kitunda vaki da karfi don nasan a garinku bakwa cintuwo sai yar gurasa da zuma ko ? Hannah daimurna take kawai da ba gida za'a kaita ba kanozasu wuce da yaya haisam. Rauda da hannah sukaje suka shiga mota a gidan baya suka zauna, yaya haisam da auwal suma suka shiga motar yayahaisam ne yake yukawa auwal yana zaune a gefe,suka nufi get din fita. Dalibai na daga musu hannuhar suka tafi.rabon rauda da ta yiwa hannah magana tunjiya yau ko magana bata yi mata ba saboda tsabankishi da ita wai saboda yaya haisam yana ji da itaitama yace kanwarsa ce, yanzu taga yan uwantakarta tabbata gata a motarsu yaya haisam zai wuce daita gidansu ma. Ta kalli hannah ta yamutse fuska tace'' kema kano zamu dake kenan, daman a kanokike baki taba gaya mana garinku ba ! Hannah tayishiru ta rasa amsar da zata bata. Haisam ya ce ''ehrauda da ita zamu kano a gidanku ma zata zaunakinga sai ku dinga karatu tare ko ? Rauda tace'' saikace basu da da gida ai a gidansu a nemeta. Cikin rada hannah tace'' babu wanda zai nemeni, ni bazani gida ba. Ta mudubi haisam na kallonta yayimurmushi kawai. Haisam ya nufi cikin garinkazaure auwal ya dubi haisam yace a'a haisam inazamuje mu da zamu kama hanyar kano. Haisam yace'' cikin garin zani akwai wacce zamu dauko. Basu tsaya a ko ina ba sai kofar gidan uwar biyu damana shirye take suna aika yaro yayi sallama ya ce injimalam haisam sai ta fito da gyalanta daman a shiryetake tsaf ta fito. Bayan sun gaisa haisam yace da surauda su matsa mata ta zauna, suka matsa ta shigata zauna a kujera baya sannan suka gaisheta dukkaninsu. Haisam yaja mota suka tafi bai tsaya ako ina ba sai a babbar tashar kazaure ya tsaya yajuya ya kalli uwar biyu da hannah yace'' to ananzaku hau mota ko ? Uwar biyu tace'' eh akwai motahar babban mutum a nan'' uwar biyu ta yunkurazata fita ta juya ta kalli hannah wacce bata da niyyar fita bata ma san da ita za'a fita ba a tunaninta uwarbiyu ce kawai zata sauka ita kuma su kara gaba sutafi kano sai taji uwar biyu tace'' to hannatu fito mutafi ko ? Cikin rudani hannah ta juya ta kalli haisamdon jin abinda zaice sai ya rasa me zai ce matakawai ya sunkuyar da kansa kasa ya kasa magana, ya fito daga motar ya bude but ya dauko jakarhannah. Nan da nan kwandastocin mota suka zosuna cewa'' babura zaku ne. Ko daura ? Uwar biyu''motar babura zamu hau sai mu sauka a babbanmutum. Haisam ya mikawa kwandasata da zasubabbam mutum jakar hannah, uwar biyu tace '' af har yanxu hannah bata fito daga
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31