Chapter 3
Chapter 3
Shigowar wata dalleliyarmota ce Jeeplaunin koriya (dark green) wacce ta tunkaro indasuke, ita ta katsewa Malam Habu surutun da yake yi. Ta zo dafda su tatsaya babu abinda yake tashi a cikinta sai sautinkida dasanyin A.C maza ne samari guda biyu suka fitodaga gani wa ne da kaninsa, kanin yana sanye da kayan bautarkasa ajikinsa wato (N.Y.S.C) Yayan kuwa wata tsadaddiyarshadda cefara sol a jikinsa sai kamshin wani tsadadden turarene yake tashi. Abunka da kauyawa sai kallo suke dukkauba da *yar,kanin ya bude but din baya ya dauko wata Jakarkaya, yamayar ya rufe ya ce da wansa "Yaya Habib, na godesai dai nace maka Allah Ya kiyaye hanya. Yaya Habib yayimurmushiya ce "To madalla. Allah Ya bada sa'a sai yaushekuma zaka zomana weekend? Ina fatan dai wannan karan zakayi kamar wata baka zo ba ko?Su duka biyun suka tuntsire da dariya, kanin yace "Ai Yayaranar juma'ar nan zaka ganni a gida ko ba'azodaukana ba mazanzo Kano, haba ai sai jini na ya hau zama a kauyein ba dole ba wa zai iya? Yayan yana dariya ya mikawakanin hannusuka gaisa ya ce "To Allah Ya taimaka, ina ganinranar juma'arda zaka zo may be baza mu hadu ba saboda dasassafe zan tashi zuwa america kai kuma nasan sai da yammazaka tahosai an tashi *yan makaranta ko? Kanin ya ce "Ehkuwa bazamu hadu ba Allah Ya kiyaye hanya Ya dawomana da kai lafiya, Yaya akwatinan auren da nawa da naka yazamo iridaya. Yaya Habib ya ce "Insha Allahu, Yaya Habibya shigamota har zai ja kofar motar ya rufe sai ya juyo yakalli Hanne da Babanta ya ce "Salamu alaikum" Malam Habu yaamsagami da daga hannu, Yaya Habib yaja motarsa yajuya ya nufikofar fita kanin na tsaye yana daga masa hannu.ayan da motar Yaya Habib ta kure, idanuwansuduka na kantasannan hankalin kowa ya dawo jikinsa. TunaninHanne yakoma ga kallon kyakkyawan ginin makarantarginin bulo da bulo,yaune rana ta farko da take tunanin take saran zatakwanta a dakin ginin bulo ba gidan kasa ba rufinazara. Ta cea ranta "Cafdijan yau kuwa zan iya bacci? Anyabazan ringa jin sanyi ba a wannan dogayen gininnikan. Bata sansanda tayimurmushi ba har hakoranta suka fito, sai tawayence ta kifakanta akan cinyarta kada Babanta ya ganemurmushin dadi take. Kyakkyawan saurayin nan ya tunkaro indasuke yanarataye da jakarsa a kafadarsa, ya yiwa Malam Habusallamagami da dan dukawa kadan, kana ya wuce su yajegindin wata bishiyar dake kusa da tasu ya daga wani benci yazauna yaajiye jakar kayansa a kusa dashi yaci gaba dakallon Hanne daMahaifinta. Can Malam Habu yaje ya same shi a indayake zaune ya ce "Dan Allah *yan samari kai maka'aikacine ananko kaima bako ne? Yayi murmushi ya ce "Yaya akayi Baba?Malam Habu ya ce "Yarinya na kawo makaranta tundazu banga kowa ba balle in tambayeshi hannun wa yakamata indankata? Saurayin nan ya gyara zama gami da cirehular dakekansa ya ce "Daliba, daliba ce wannan? Malam Habuya ce "Eh nan aka ce na kawota kuma gama takardar canbari ta mikogama korarmu akayi dazu da babu takardar, yakwalla kira yace "Hanne kawo takardar nan ta dazu.Cikin sauri Hanne tasa hannu a cikin bokiti dakegabanta tadauko takarda tazo ta mikawa Babanta da hannubiyu ta dukahar kasa. Babu abinda wannan saurayi yake saikallon Hanne sama da kasa kayan jikinta yake kallo da takalmindakekafarta wanda ta daure da leda saboda ya tsinkekudin naninma aiki ne, wata uwar danmara kai kace dambentsiya za'a kwasa, wuyan, hannu da kafa tsakiyoyi. Saurayinnan ya kulada lallai Hanne ita kanta tana jin kunyar shigar nantata ganinkallon da yake yi mata, sai yayi sauri ya fara dubatakardar da Malam Habu ya mika masa. Ya karance tsaf, sannanya dagoya ce "Hanne Habu Imamu ko? Tace "Eh, ya ce "ToBaba saikun dan jira don nima nan Malamin nake jira gashitakamaimai ma ni bansani ba ko yana makarantar kobayanan don nima shigowata kenan. Malam HabuyayiHamma gami da yin dan siririn tsaki ya ce "Yaroyanzu bayadda za'ayi ka karbi yarinyar nan, dole sai waccan din ya zo? Saurayin ya ce "Ni Malami ne amma kuma bapermanentteacher ba bautar kasa (service) nazo yi, a ka'idarwannanmakarantar kuma senior master ne ya kamata ya karbetamusamman ma kasancewarta sabuwar daliba ce.Gashi yau lahadi, dama litinin ce ko sauranranakun aiki lokacin principal tana nan, da sauranpamanent teachers duk sai su karbeta koda seniormaster baya nan, amma yanzu ku jira kadan idannan da minti talatin bai dawo ba, zan tashi nima nashiga staff quaters din na gani ko yana ma cikin makarantar dan nima shi nake so na gani zan karbimukullan gidana. Malam Habu ya ce "To Allah Yakawoshi lafiya bari nayi sallar la'asar, nasan biyartayi ko sallar la'asar bamu yi ba. Yaro ina buta? Yanuna masa wani fanfo can kusa dashi kuma dazagayeyyen waje nan ne Masallaci. Malam Habu ya ce "To madalla. Ya kalli Hanne wacce ke tsaye agefe har yanzu ya ce "*Yar Baba koma kanakwatinki ki zauna zanje nayi sallah kinji. Cikinsanyin murya ta ce "To, ta juya ta doshi wajenakwatin. Malam Habu ya bita da kallo zuciyarta cikeda tausayinta ganin yininsu guda babu abun da suka ci tun dan kokon safe da suka dan kukkurbaa tsattsaye bala'in Iya Abu ya hanasu su zauna susha sosai. Malam Habu ya girgiza kai alamartausayawa kansu da kansu ya ce "Allah Sarki *yarBaba hakuri dai za ki yi, ki kuma ci gaba dayi.Sannan ya juya ya nufi wajen fanfo. Kyakkyawan saurayin nan na zaune yana kallonsu zuciyarsacike da alamomin tambaya da tsananin tausayi. Canya nisa yayi ajiyar zuciya ya zaro gilashin dakealjihunsa ya saka a idonsa gami da cusa hular dakehannunsa a cikin aljihunsa na wando yasahannunsa ya dafe habarsa yaci gaba da kallon Hanne dake zaune kan akwatinta tayi lamo tanatunani ba tare da tasan wani na nan gefenta ta cikingilas yana kallonta ba. Ya ce a ransa "Wadannandaga wanne kauye suke?Sun kuwa karanta takardar dake hannunsusunsan me ya kamata su tanada suzo dashi? Kaibasu san dokar da aka rubuta ba a jikin joininginstruction din nan ba. Lallai kuwa da sun san meaka rubuta da baza taci uwar danmarar nan ba tashigo makarantar nan haka ba. Bayan kamar tafiyar Malam Habu da minti ashirin sai gashi yadawo. Ya zo ya wuce ta gaban saurayin ya ce"Sannun ka da hutawa, ya katse tunanin da yakeya ce "Yauwa Baba. Malam Habu ya kara da cewa"Har yanzu dai kaga shiru baizo ba ga rana nan nashirin faduwa yau kuwa anya mai karbar yaran nan zai dawo? Yayi murmushi ya ce "Ina ganin kakawo duk abubuwan da aka ce ta siya da kudinmakaranta zan yi kasada na karbeta yanzu in yasoranar litinin wato gobe idan mutum yazo ya rubutarisitai yanzu sai nayi magana da masu gadin get dinHostel su kirawo prefect din.... Malam Habu ya matso kusa dashi ya ce "Yaro fadamin da Hausasosai na gane me kake cewa? Har da wani abu dazan kawo nan gaba? Ya ce "Eh Baba, ai a rubuce ajikin takardar aka rubuta za'a dinka mata kayanmakaranta har kala hudu, wanda zata sa idan zasuaji da wanda zata saka a dakunansu, dana wasanni (sport) duk an rubuta kuma lallai-lallai sai da kayanmakaranta za'a karbeta ba zata ta saka kayan gidaba, sannan daga karshe aka rubuta zata zo dakudin makaranta (school fees) shi kuma dakesabuwar zuwace sai kun biya sama da dubu.....Malam Habu ya katse shi da sauri
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31