Chapter 1
Chapter 1
GANGARJIKINSA NA AURA 1 Part 1 Posted by ANaM Dorayi on 07:51 PM, 29-Apr-15 Under: Gangarjikinsa ta Aura GANGAR JIKINSA NA AURA JAMILA UMAR TANKO {JUT} ⃣Wata kwarababbiyar mota kirar bus mai kararfatattakekkiyar salansa ce ta tsaya a bakin get dinmakarantar 'yan mata ta gwamnatin tarayya dakegarin Kazaure, wato F.G.G.C. Kazaure. Tana tsayawakondastan motar ya ja kofar ya bude "Barararaa"saboda kwankwatsewar da kofar motar ta yi sakamakon cin ruwa da gafje-gafje da tsabar tsufa.Wani dattijo mai kimanin shekaru saba'in da doriyane ya fito, da wata *yar yarinya tana biye dashiwacce shekarunta basu wuce shekaru goma shadaya ba, Bayan sun furfito kondastan motar yazagaya baya wato but ya dauko wata katuwar akwatin karfe irin ta *yan makarantar wacce akadafka sunan mai akwatin garza-garza da fenti bakiHANNE HABU IMAMU. Ya ajiye gefe ya sake janyowata karamar katifa wacce take daure ya doraakan akwatin, sannan ya dauko wani bokitin karfesabo dal yana sheki shima an fenteshi da sunan mai bokitin wato HANNE HABU IMAMU. Daga karsheya mayar da kofar but din ya rufe ya juyo ya kallidattijon wato Malam Habu ya ce "Baba baka fa cikamana kudin motarmu bafa, gashi har kun sauka"Malam Habu ya sake marairaicewa ya ce "Dana daAllah fa nake hadaka kuyi hakuri kudin da yayi saura a aljihuna ko gida bazai mayar dani ba, sai nanemi ciko kayi hakuri dan Allah, dan haka nemanace ta zauna a maleji yanzu baza ka tausayawatsoho ba, karbi arba'in din?" Kondasta ya sakefusata ya ce "Dalla Baba kana bata mana lokaci gafasinjoji har sun fara tsaki sun kagu suma a kaisu inda zasu. Ka zauna kana mana magiya tun dazumuma fa ba'a bati muke shan man motar da mukejigilar nan bafa, da kasan kudin motar taka bai cikaba me yasa ka hau? Har zaka ce wai yarinyar amaleji ta zauna, maleji ba cikin mota bane? Bakasan har a sittin muke daukar na maleji ba daga inda muka dauko ku zuwa nan nayi maka ragi nace kakawo hamsin dinma gashi kaki biya sai wataarba'in ka bani, kai wallahi Baba saika ciko managomarmu kaji ko? Direban motar dake zaune awajen tuki wanda yake jin duk abinda suke yi, saiyanzu ya waigo inda suke yayi magana ya ce "K.b wai yane? K.b ya ce "Har yanzu wannan tsohon baidaina magiya ba wai shi ayi masa ragin goma kudinyarinyar nan data zauna a maleji, Hamsin nace yabiya, ya wani bani arba'in. Kuma ma dan raininhankali harda cewa kudin aljihunsa bazai mayardashi gida ba, wato yana da kudin, cikawa ne bazai yi ba.din aljihunsa bazai mayar dashi gida ba, watoyana da kudin, cikawa ne bazai yi ba. Malam Habuya danji dadi ganin direban yayi magana ko zaice abar masa amma sai yaji kalamansa sabanintunaninsa gara ma abinda kondastan ya fada masa,cewa yayi in har bazai biya ta dadin rai ba to zasu farka aljihunsa su dauki gomarsu, Malam Habu yarike baki don mamakin irin wannan rashinmutunci, can ya nisa ya ce "Allah Ya kyauta, bari nabaku kudinku abin duk bai kai ga haka ba, yasahannu a alhihunsa na dama ya dauko watacukurkudaddiyar naira biyar ya sake saka hannu a aljihunsa na bangaren hagu ya dauko gudar nairaashirin da kwandaloli guda biyar, ya hadakwandalolin nan guda biyar da cukurkudaddiyarnaira biyar din nan ya mikawa kondosta ya ce"Gashi dana Allah Ya kiyaye. Ba kunya ba tausayintsohon nan yasa hannu ya karbe yana gunani "Daman kana dashi ka tsaya kana bata mana lokaciduk fasinjoji sun kagu, direba ya juyo ya ce "YayaK.b ya baka, sun cika? K.b ya ce "Eh sun cika jamujeJ.J.C. Malam Habu da *yarsa Hanne suka bi motar dakallo har ta hau titi ta kure sannan hankalinsu yadawo kan kayansu. Malam Habu ya kalli *yarsa Hanne wacce hawaye ya gauraye idanuwanta dakumatunta, abin ya bashi mamaki ganin Hanne nakuka alhali kuma ita take son karatu take murna dazasu taho, ya sake juyowa sosai ya kalleta yagahawaye ne ke zubowa daga idanuwanta dayanabin daya, ya ce "*Yar Baba, kukan me kike yi? Karki cemin yanzu bakya son makaranta bayan keaka kira fadar mai gari aka tambayeki kika ce kinaso. Ba'a son raina ba nima na kawo ki makarantarnan ke kika amsa musu. Shine kuma yanzu kikekuka? Idan kinsan bakya so to ni a wajena tafinono fari sai mu juya kafin mu shiga ciki. Kansila da mai gari su suka tilastamin in kawo ki amma badanhaka ba nima bazan rabu dake ba na kawo ki nanuwa duniya, babu wanda kika sani. Hanne tagirgiza kai cikin shesshekar kuka ta ce "Baba bamakarantar bace bana so, rashin kunyar da masumotar can suke yi maka shine ya sani kuka. Malam Habu yaji hawaye ya cika masa ido amma sai yajure yayi murmushin karfin hali ya ce "Allah Sarki*yar Baba, babu komai duniya ce. Duk wanda yagagirman tsohon wani, za'a ga girman nasa. Hakakuma duk wanda ya raina tsohon wani sai an rainanasa, zamani ne ya canja babu sanin girman Allah, ko an hada mutum da Allah kamar an hadashi dasa'ansa, wani cewa zaiyi daina hadani da Allahkarka cuceni Wa'iyazubillah. Ya ci gaba da cewa"goge hawayenki 'yar Baba kizo in dora mikiakwatin mu shiga ciki kada dare yayi min kinga harla'asar tayi. Tasa gefen gyalen da taci damara dashi ta goge idanuwanta kana ta matso ya ciccibiakwatin karfen nan ya dora mata a kai shi kuma yadauki bokiti da katifa a daya hannun sa'annansuka juya suka doshi cikin babbar kofar shigamakarantar, yaci gaba da yi mata nasihohi masuratsa jiki yana nuna mata wannan abin da aka yi masa a gabanta ya zama darasi a wajenta duklalacewar tsoho koma ba tsoho bane na gaba da itakada tayi masa fitsara. Ta zamana ko a ina takekuma kome ta zama ta girmama na gaba da ita.Ta zama mai taimakawa mabukata, kasancewartasan talauci ta kuma dandanashi tana kandandanashi. Masu gadi uku suka iske a bakin kofarshiga cikin makarantar, suna zazzaune, MalamHabu yayi musu sallama gami da mimmika musuhannu, Hanne ma ta duka ta gaishesu, bayan sun amsa, Malam Habu ya ce "Yarinya na kawomakarantar nan, ta ina zanbi mu shiga ciki? Dayadaga cikinsu ya ce "Mikewa zakuyi sosai zaku tararda ofishin Malamai dana shugaban makarantar.Malam Habu yayi godiya suka wuce, har sun danyonisa suka ji masu gadin nan sun kwalla musu kira bayan sun dawo, sai daya daga cikinsu ya kallesusama da kasa ya ce "Dan Allah Malam muna datambaya sai bayan da ku ka wuce tambayar ta fadomana. Malam Habu ya gyara kayan dake hannunsagami da yin murmushi ya ce "To Allah Yasa na sani.Ya ce "Wai shin me kake tambaya ne? *Yar makaranta ka kawo daliba ko kuma mai aiki kakawo gidan Malamai a nuna maka gidan Malamai(staff quaters)? Malam Habu ya ce "A'a daliba nakawo 'yar makaranta ce. Su duka suka kyalkyaleda dariya suna tafawa wani harda buga kafa akasa. Abun ya daurewa Hanne da Mahaifinta kai. Menene abun dariya?Konan ba ita bacemakarantar 'yan mata ta gwamnatin tarayya dakeKazaure? Malam Habu ya tambaya suka ce "Nan cemakarantar daka ambata amma watakila kayibatan kai ko baka ji dai-daiba. Malam Habu ya ce"Batan kai kamar yaya? Daya ya ce "Nan makaranta ce ta 'ya'yan masu hannu da shuni,'yan birnimasu kokari, ba haka kawai dan ance 'yarka tacimakaranta ba kaje ka suyo akwati da katifa kazoka zabi makarantar da ranka yake so ka shiga kacega daliba. Daya ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31