Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Complete Hausa Novel 1,231 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

baki da komai,ba ki san kowa ba, Ya juya ya tafi. Hanne na tsayehawaye yana zuba daga idanuwanta tana kallonMahaifinta yana tafiya yana waiwayenta.Taji wani kululun bakin ciki marar misali akirjinta da mummunan tashin hankalin rabuwa daMahaifinta, yaune ranar da ta taba rabuwa daMahaifinta daidai da rana daya basu taba rabuwaba. Gashi a yau ya kawota inda bata san kowa baya juya ya tafi ya barta. Hawaye ne mai radadi yake zubo mata har sai da ta daina hango fararenkayansa ya kure, sannan ta yi ajiyar zuciya tasagefen mayafinta ta goge idanuwanta ta juya tadawo kan akwatinta ta zauna. Haisam na zauneakan benci yana kallonsu zuciyarsa cike datsananin tausayi ji yake wani abu yana yawo a cikin kansa, saboda wani abu guda daya daya bashimamaki ya bashi al'ajabi, shine ganin yadda Hannetake da Mahaifinta suna cikin tsananin talauci ammasuna da wadatar zuci. Haisam yaci gaba da kallonHanne wacce take zaune akan akwati a gabansa tasunkuyar da kanta kasa tayi shiru kamar mai tunani, amma hawaye na digowa daga ganintahankalinta a tashe yake tana cikin damuwa. Yagyara zama gami da zare farin gilashin da yakefuskarsa. Ya ce "Hanne, kukan mai kike yi ne?Bakya so ki zauna a makaranta kiyi karatu kamarsauran yara, kin fi so ki koma gida ki zauna da Baba? Hanne ta girgiza kai alamar a'a, ya ce "Tomeye kike kuka? In kinsan bakya son makarantarnan yanzu nayi sauri na tsayar da Babanki kafinyayi nisa sai ku koma gida. Hanne tayi sauri ta ce"A'a bana so na koma gida, ya ce "To ai kuka kikemeyasa kike kukan tunda kina son makarantar? Bakya son ki koma gida inda zaki yi wasa kuyiwake-wake da kawayenki a dandali? Hanne tayidan murmushi ta sunkuyar da kai. Haisam ya cigaba da cewa "Ni kuwa na dauka danmarar nan dakika ci ta zuwa wake dandali ce. Hanne tayi narai-narai da ido kamar zata yi kuka ta ce "Ni ba'a barina naje dandali wasa. Kullum aiki nake yi sai daiinzo in wuce su in zani debo ruwa. Haisam ya sakegyara zama ya ce "Ban gane ba sai dai ki zo ki wucesu in zaki debo ruwa? Ke kullum a debo ruwa kikebakya zuwa wasa? Hanne ta ce "Eh, sai dai suSaude Yayyena da kanne na ne suke fita wasa.Haisam ya ce "Ina Mahaifiyarki take? Hanne tasake saka gefen gyalenta ta share hawaye ta ce"Tun ina shekara biyu ta rasu. Yaji gabansa yayanke ya fadi ras, saboda yanzu ya gane Hanne agidansu tana cikin halin wahala kasancewarMahaifiyarta ta rasu da alama kishiyar Uwa tana wahalar da ita. Allah Sarki Hanne ya fada a ransayayin daya kura mata ido. Hanne ta bashi tausayida, a yanzu kuma ta sake kara bashi tausayi akantausayi wanda badan ya daure ba da zai iyarushewa da kuka. Can bayan sun dauki wani lokacimai dan tsawo babu wanda ya sake cewa komai. Dukkaninsu kansu a sunkuye a kasa suna tunani,Haisam ya rike kai da hannuwansa guda biyu canya dago ya kalli Hanne ya ce "Yanzu dai a gidankuke kadai Babarki ta haifa kenan baki da Yayye ko?Hanne ta ce "Eh. Ya ce "Shine kuma ake saki deboruwa kullum. Hanne ta ce "Ba debo ruwa kawai ba kullum ni nake wanke-wanke, shara, wankinsu, dakai dabbobi kiwo daga can nayo musu ciyawa.Haisam ya buga kafa a kasa ya ce "Kai wannanwanne rashin imani ne haka? To ya akai kike zuwamakaranta? Hanne ta ce "Sai wajen sha dayan ranakoma wataran bana zuwa, tun ana min dukan makaranta har suka daina su Malamai. Shine waniMalami ya je ya sami mai gari ya ce a yiwa Babanamagana a dinga turoni makaranta da wuri tundaina da kokari, Haisam ya ce "Sai da maigari ya kiraBabanki ya fada masa sannan ake turakimakarantar da wuri? Hanne ta ce "Cafdijan shima Baban ya isa? Ya ce "Kamar yaya bai isa ba.Ta ce "Shima tsoron Iya Abu yake, matar tasazaginsa take,*ya*yanta suyi masa, sai dai in ana dukana inakuka shima yadinga yi. Hawaye ya sake kece mata, shima ya jikwalla ta cika masa ido, ya dauko wani hankici fari kal a aljihunsaya gogeidanunsa ya mika mata, ya ce "Yi shiru Hanne dainakukagoge hawayenki. Ta karba ta goge. Haisam ya ce"Bari na danyi miki tambayoyi naji kina kokari? What is yourname?Hanne ta ce "My name is Hanne Habu,Ya ce "Howold areyou? Ta ce "I'm eleben years old. Wich school areyou? Ta ce "I'm in Babban-mutum special primary school.Haisam yayidariya ya ce "Hanne Habu haka kike da kokari? Toke da bakyazuwa makarantar sosai ya aka yi kika koyi dukwannan? Hanne tayi murmushi ta ce "Ai daga baya maigariyasa akakirawo ita iya Abu da kanta taje fada ya sakashaidu ya ce"Duk ranar data hanani zuwa makaranta ko namakara sai ya kaita kara local goverment. Sannan take barina natafimakaranta da wuri sai dai idan na dawo tayi tadukana tanacewa ga wanke-wankenta nan harya bushe natsaya a hanya ina wasa. Haisam yayi tsaki ya girgiza kai alamartausayawa.Yayi gyaran murya ya ce "Hanne ina so kiyi minalkawarin zakidage kiyi karatu duk rintsi duk wuya. Kar ki zo kifara ayi hutu ki koma gida kiga kawayenki da yayyanki sunagida basa zuwamakaranta kema kiki dawowa. Hanne ta ce"Kwarankwatsazan dawo.(hahah. Inkikayimata dariya bazancigabarmikiba,'Eh' dake nake Zee ) Haisam ya kece da dariya (subhanallahi, tinda shima yayi to kema danyi amma kadan),ya ce"Kwarankwatsabarantsuwa bace wallahi Allah za ki ce. Hanne tayidariya ta ce"Mantawa nayi Malamin makarantar Islamiyya yahana mu cewa kwarankwatsa. Haisam ya ce "Kina zuwaIslamiyyakenan? Ta ce "Eh, ada makarantar allo muke zuwadaga bayaaka bude makarantar Islamiyya da yamma dakuma dare duka ina zuwa. Haisam ya ce dakyau Hanne yanzuidan anyihutu kin koma gida sai kici gaba da zuwa taIslamiyya karkifasa zuwafa kinji? Hanne ta ce "To. Haisam ya cigaba da kallonta har sai da Hanne ta fara jin kunyar kallonda yakemata sannan yayi murmushi ya ce "Hanne dukwannankwalliya ce kika yi a fuskarki, ta zuwa makarantace? Hanne tayi murmushi ta sunkuyar da kai kasa tana rurrufefuska dahannu ta ce "A'a ba kwalliya bace. Ya ce "Gashi nankinrambada kwalli kinja wata doguwar jagira kinyifashin goshi da kwalli kinyi digo-digo duk fuskarki kice bakwalliya bace. Gawannan tsakiyoyi da kika jifga a wuya da hannuhar kafarkima kin daura, Yana dubanta yana dariya. Hannan tace "Eh sarkar salla tace Baba ya siya mun. Ya ce "Kingananmakarantar an hana sawa idan Malamai suka ganizasu kwacesu tsittsinka miki, ciro su ki bani in ajiye miki saianyi hutu in zaki tafi gida na baki. Cikin sauri taji zancentsittsinkawa taciro ta bashi, yadda take bala'in kaunar sarkokinnan natabata son abun da zaisa ta rasa su. Haisam ya karbayana jujjuyasu yaga wasu irin tsohon wuri ne aka jera sucikin liloaka daura ya ce a ransa "*Yan kauye suna gayu.Yayi murmushi ya jawo jakar kayansa ya budewanikaramin zip ya zuba ya mayar ya rufe. Ya juya yakalli Hanneya ce "Kuma a cikin akwatin naki bude in gani kokinzo da wani abunda dokar makaranta ta hana. Hanne tatashi dagakan akwatin ta bude ya karkato ya leka akwatinbabu abundaya hango sai tsummokarai, cikin sauri ya ce "Hanneme wancan nake hangowa kamar miciji a cikinakwatinki? Hannetasa hannu ta zaro wani dan siririn gyale baki yakanannadeya kudindine ta ce "Gyale ne ba miciji bane. Haisamya kyalkyale da dariya ya ce "Na dauka kofi kika yiminna miciji.Hanne ma tayi dariya ta ce "Gyale na ne dan bansaruwa

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});