Chapter 16
Chapter 16
na hana karatun hanne ko bai fada miki ba ne ? Iwar biyutace '' shine mahaifinta shine kuma mai iko da'yarsa bake ba. Ni kuma akan kin barin yarinyarnan ta tafi zan iya cin dammara mu daku da kowakuma daga na har gaban mai gari zamu je dakeidan kika kwatanta hakan. Iya abu tayi shiru tasan idan aka kaita kara wajen maigari tasan bazai bibayanta ba kasancewar sun sha gogawa akan zatahana hanne karatu bata ci nasara va. Iya abu tanisa tace to kije dawan da kanki ki kirawo hanne'yata ba zata ba. Taja hannun 'yarta mahajana sukashige cikin gida.malam habu ya leka kofar gida ya kira musa dan makwabtansu ya ce yaje dawa yaceda hanne tazo yanzunnan ta koro kiwan su dawogida. Uwar biyu ta tabe baki gami dayin ajiyarzuciya tace'' rabon gado akayi da kayan hannetunda ranta ba'a jira ta mutu ba. Caraf iya abu ta fitoashe a labe take tace'' an raba kayan hannen ko hannen naga dama zan iya rabata balle kayanta.Duk gulmace gulmacen da kuke hadawa ya kare akanku babu wata makaranta da ake kai hanneyawon bariki kawai ake koyawa yarinya ta samoabin duniya'' uwar biyu tayi dariya shekeke tace''wannan yawon bariki na hanne don ke da yayanki take yi irin wannan bushasha da kayan yarinya. Dayake itama uwar biyu badaganan ba wajen iyamasifa da yaba magana suka yi tayi dakyar malamhabu ya hana uwar biyu magana ya ce ta yi shiru takyaleta, iya abu tayi fada tana shiga da fice bakinciki ya lullube mata zuciya kamar zata fashe ganin anzo za'a dauki hanne a tafi da ita wajen da takehutawa. hannah ta shigo a sanyaye tana fargaba tanatunanin me tayi kuma aka ce ta koro kiwo ta dawogida yanzu. Tana shigowa sai taga uwar biyu damahaifinta a zaure a zaune ta daka tsalle tarungume uwar biyu tana mai tsananin murna dafarin ciki tace. Iya daukata kika zo yi mu tafi'' uwar biyu tace'' yanzu kuwa shiga ki dauko kayanki mutafi. Hannah tayi kasake a tsaye murna ta koma cikitayi kamar zata fashe fa kuka. Uwar biyu ta kalletatace'' hannatu lafiya meya faru kuma kika zamahaka lokaci daya kamar mai shirin rushewa dakuka ? Uban yace da kika ce taje ta dauko kayanta shine jikinta yayi sanyi ai babu kayan duk sunkwashe. Harda litattafan makarantar sun yayyagasun siyarwa da mai kosai wasu'' uwar biyu takwada salati tana cewa'' harda manyan litattafankaratu masu tsada suka yayyaga mata ? Iya abutayi wuf ta fito tace da uwar biyu !! Ki kiyayeni don kin zake dawa, karfa ki kuskura ki cika min cikiba'aja dani an yayyaga littafin kyi abinda zakiyikuje ku saya mata wasu ta kawo na sakeyayyagawa muje duk inda zamu je aikin banza.Uwar biyu ta mike tsaye ta juya ta kalli malam habuwanda yayi tsuru abin duniya ya isheshi ya kasa magana tace '' malam na tafi da hanne allah yanabayan mai gaskiya kuma duk dan hakin da karaina shike tsone maka ido zakaran da allah yanufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi.Hanne mu tafi garin da ake kaunarki. ''iya abu tarako su har kofar gida tana zagi tasa hannu ta fallawa hanne duka a baya gami da angazata ta tafitaga taga zata fadi uwar biyu ta riketa tajahannunta suka tafi. Hanne ta rushe da kuka uwarbiyu fadi dake. Duk abinda zaki yiwa hannah bakiisa ki hanata numfashi a duniya ba tunda bake kikahalicceta ba'' suka kama hanya suka tafi, suna ji iya abu ta koma kan mahaifin hannah tana zazzagamasa masifa yayi shiru kamar bada shi take ba. A tasha uwar biyu ta siyawa hanna sabon silifasdomin na kafanta wari da wari ne, suna zaune amota uwar biyu take tambayar hanne abubuwanda ake yi mata. Hannah ta zaiyana mata tsaf tacekusan kullum sai an lakada mata duka an kwacekayan sawarta da jakunkunanta, sabulan ma da mayukan shafawa ko sau daya ba'a barta tayiwanka da suba. Tana dai barinta taje makarantarislamiyya kullum shima saboda tana tsoron maigarine. Hanne ta sake dagulewa kamar ba itace tayikyau din na ba das da ita gwanin sha'awa, yanzu tadawo furtutunta, yagulallun kaya uwar biyu tace'' yanzu har kayan makarantar taki(uniform)duksakawa suke ? Tace eh ta rarrabawa jikokintawasu, wasu kuwa ta sayarwa 'yan jagorar makafi.Bani da sauran kaya sai wannan na jikina, uwarbiyu ta nisa tace allah ya saka miki, kuma wannanyaro haisam shima an sake ja masa sabon aiki'' zugum suka yi su duka kowacce tana tunani harsuka isa tashr kazaure babu wacce ta sake yinmagana suna isa gida uwar biyu ta shirgowahanna abinci mai yawa da mamakinta hanna tatashi dashi tasha ruwa. Bayan sun huta uwar biyutasa 'yarta halima ta wanke mata cukurkudeden gashinta , hannah ta sallah wanka. Kafin magarubahar an gama rangadawa hannah kitso,Sai suka ji ana rangada sallama uwar biyu tacehanne ta leka zaure taga waye yake sallama . Tanalekawa sai taga safiyanu ne abokin yaya haisam,rike da wata katuwar jakar bacco babbar ta karshea girma. Hannah tayi dariya '' tace lala yaya safiyanusannu da zuwa . Ya ce yauwa har kinzo ,hutu ya kare ko ? Hannah tace'' eh ka shigo mana'' dakyaryake jan buhun a kasa saboda a shake yake damda kaya. Suka iske uwar biyu a tsakar gida. Lalemar haban, uwar biyu take cewa hannah tayi saurita shimfida tabarma ya zauna. Bayan sun gaisa da uwar biyu ya fara zazzagekayan dake cikin wannan katuwar jaka siyayyarhannah ce ta makaranta (provision) kaya ne abunbaya lissafuwa komai akwai kai kace kanti za,abude uwar biyu ta rike baki kawai tana kallon ikonallah, tace '' safiyanu wannan kaya ai ya yiwa hannah yawa. Safiyanu yayi murmushi ya ce aikudin da haisam ya bani ne masu yawa ne ya ceduk ayi mata siyayya a wadace. Nima da kainanaga ya dace na bar siyayyar nan haka ba donkudin sun kare ba . Uwar biyu tace ai gara da karago kudin don sai an sake siyan sababbin uniform da litattafai. Safiyanu ya ce ina nata nada , ko dukterm ake sake wa ? Uwar biyu ta gyara zama ta farabawa safiyanu labari duk abunda ya faru da kayanhannah tun daga biri har wutsiya. Safiyanu yatausayawa rayuwar hannah duk da yake damahaisam ya gaya masa kadab daga ciki. Ya nisa ya ce'' abun babba ne kudin da yawa musamman nasayan litattafan karatun(text book)masu tsada negashi haisam din bama ya kasar. Uwar biyu tacebaya kasar ina yaje ? Nifa tun ranan hutu ban sakesashi a idona ba. Safiyanu ya ce'' ai kuwa bai dadeda tafiya ba shi da mahaifiyarsa suka tafi london kinsan shirye shiryen bikinsa ake yi shi da yayansawatakila nan da wata uku za'ayi don haka damanzaiyi wuya haisam ya sake dawowa kazaure tundabautar kasa daman yazo kuma sun kare. Nima dayake daman a kano na sanshi a can muke haduwa.A can kuma ya ce zai dinga kawo min kudin siyayyar hanna. Yanzu dai abunda za'yi duk abindaya tashi na game da makarantar hannah a gayamin zanyi ko nawa ne zan ranta masa nasan zaibiya ni don haka daga yau zuwa gobe zanyi kokarina saisayo mata uniform din da takalmi da kumalitattafan. Zuwa gibe telan daya dinka mata wancan zai dinka mata da wuri . Jibi dai zasu komamakarantar kafinnan insha allahu komai yakammala. Uwar biyu tayi murna dajin bayanansafiyanu tayi ta godiya. Amma hanna ta fita
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31