Chapter 23
Chapter 23
bata bataabincin da suke dafawa ba. Ita kuwa hannahdaman tafi sin haka domin ita yanxu ta saba da cinmai maiko a makaranta tuwon dawa miyar kukasai su iya abu. Madara da biskit ne abincinta , alufge a jakarta a dakinta. Sabulan wanki dana wanka masu kamshi take amfani daus ita damahaifinta. Ta bashi yayi wanka ta wanke masakayansa. Malam habu yana jin dadi sosai dawannan abu da hannah take yi masa. Yasan doleidan hannah ta zo zata kawo masa kudi da abunduniya. Ga dinkuna da take kawo masa tace inji yaya haisam. Silifas dan madina dana gayu yanzumalam habu yake sawa. Tsaf tsaf dashi na kashewaya daina gagararsa. hannah ta zama tamkar wata tauraruwa mai haskea cikin taurari a makarantarsy. Akwai kungiyoyi{club} a makarantar da yawa, tun hannah tana ajidaya ta shiga kungiyoyi daban daban. Kuma dukwasannin kwaikwayo da za a yi a kowaccekungiya sai an saka hannah ko tana so ko bata so saboda kyawunta. Tun ana sata a matsayin yarinyahar aka zo ake saka ta a matsayin budurwa. Donhaka hannah ta kware sosai wajen iya wasankwaikwayo suna fita suje makarantu daban dabana fadin kasarnan, kamar su f.g.g.c azare,f.g.g.cbauchi, f.g.g.c. Kano,f,g,g,c, bakori da dai sauransu. Saboda kyawun hannah da iya acting dinta yajawowa.f.g.g. C kazaure suna da farin jini a wajendaliban sauran makarantu. Kowa ya budi baki saiyace kai a f.g.g.c. Kazaure da suka zomakarantarmu akwai wata mai kyau hannahabubakar ta iya wasa. A yau da yamma su hannah ne suke gwaji{rahazal}din wani wasan kwaikwayoda zasu he unity gwaram suyi sati mai zuwa.Kungiyar yan hausa fulani ne suke yi, malamhaisam shine shugaban 'yan hausa club, shinemalamin kungiyar{club master}don kawai yafarfado da al'adun hausawa a makarantar, ya kuma hada kan musulmai yara da manya ya zamana sunhadu a waje daya yare daya sunyi raye raye fawake wake da wasannin kwaikwayo tare. Hannah abubakar itace a mastayin yarinya maisuna talatu cikin wasan kwaikwayo, maryam tijjaniitace a matsayin saurayin ciki mai suna abdul.Haisam ne ya rubuta labarin wasan kwaikwayon. Ayadda wasan kwaikwayon yake maryam tijjani{abdul}saurayin ciki shine ai yi tafiya kasar libiya karatu sai yayi shekaru hudu acan sannan zaidawo. Ga budurwarsa hannah wato talatu a cikinwasan sunyi alkawarin zasu yi aure daman saitafiya ta taso masa yazo zai tafi ya barta. Damanhaisam ya gutsuro takarda ya rubutawa kowacceabinda zata ce a wahen sai ta rike tana karantowa harta rike da ka, kafin ranar da zasu yi ba sai datakarda ba. A yau kusan yan aji shida kakaf sunazaune a hall din nan wajen da ake gwaji{rahazal}din nan da wasu da yawa daga cikin yan aji biyar,hudu da uku yan kungiyar. Maryam tijjani {abdul}itace ta taho da jakar kaya katuwa a rataye a kafadarta tazo wucewa suka hadu da hannah{talatu} dauke da kwarya a kanta zata je kogi deboruwa. Abdul ya sakarwa talatu wani lallausanmurmushi na so da kauna cikin sassanyar muryahannah(talatu) tace''abdul ba dai tafiya ba'' ya ce''tafiya zanyi talatu nazo ne daman inyi miki sallama'' sai kawai kwaryar dake kan talatu ta fado kasa dangigicewa. Ta rushe da kuka. Abdul ya gigice yaajiye jakar dake hannunsa, hannah ta fara karantotakardar da haisam ya rubuta musu tace'' abdulkayi min alkawari ba zaka yi aure ba a cam har saika dawo ka aureni karka je can ka sami yar larabawa ka aura ni ka manta dani'' haisam yasatafi sai duk aka dau tafi a hall din. Haisam yacekunyi kokari wajen yayi kyau kema maryam tijjaniki dage ki bata amsa dan allah banda dariyar nanda kika saba'' maryam tijjani tace to bazan yi dariyaba'' ta daga ido ta kalli hannah(talatu) wani kallom soyayya da hannah take, tayi wani narai narai daidanuwanta kai sai kace a gaban saurayinta nagaske take. Sai dariya ta kwacewa maryam tijjanisai kowa yasa dariya. Haisam yace ''maryamgaskiya kina bata mana lokaci kullum muka zodariya kawai kike yi saura kwana uku fa mu fita excusion idan kinsan ba zaki iya ba nasawata''maryam tace''uncle allah hannah ce take sanidariya baka ga kallon fa take yimin bafa kamar tasami saurayinta da gaske sai kashe idotake''haisam yayi dariya yace''tsabar tafiki iyaacting kenan. Shi daman wasan kwaikwayo ana son duk abunda aka baka kayi kokari ka nunakamar da gaske ne. wajen kuka kayi kuka, wajen murnakayi murna . Kema kiyi mata kallo kamar kecesaurayin kin hadu da budurwar da kika fi so a duniya. Wannan yana nuna kenan hannah ta iyaacting sosai kamar da gaske. Kowa ya hau dariyaana yiwa maryam tsiya ''kema ki yi mata kallonsoyayyar mana ko baki iya bane? Haisam ya tashi yaje ya karbi takardar hannunmaryam ya ce''koma gefe ki dinga kallon yaddazamu yi sosai don ki koya'' ya ce da hannah''tokara karanto naki''babu kunya hannah ta narkarda idanuwanta ta kashe murya lallausa ta dubihaisam kallo ido cikin ido''abdul kayi min alkawarin ba zaka yi aure ba a can har sai ka dawo ka aurenikar kaje can ka sami yar larabawa ka aura ni kamanta dani anan'' haisam ma ya narairaice ido yakurawa hannah ido kawai wannan kallo da haisamyake yiwa hannah ya sosa mata wani waje axuciyarta, ya ce''talatu ba zan yi aure ba, kuma ba zan manta dake ba. Ko a ina nake, ko da gangarjikina bata tare dake ruhina yana tare da ke.,soyayya baiwa ce, hannah kina raina a kodayaushe . Ina sonki hanna'' taji gabanta ya fadi donjin yaune rana ta farko da hannah tasan ma'anarwakar nan da take yi tayi shiru tana tunani tana kallon yaya haisam ta san tabbas wannan wajen acikin wakar nan da take yi masa ya dauko kamardaga sama taji yaya haisam ya ci gaba da cewa''inasonki ina sonki hannah! Ba zan manta dake bakina raina har abada'' wannan karon bakarantowa ya ke a takarda ba kuma ba talati yace ba, hannah sai ta fara ja da baya taba tafiya ahankali tasa hannu ta rufe idanuwanta tanamurmushi. Kunya ta ka mata gaba daya yan kallonsun zubo mata ido suna kallon sarautar allah, domin kowa ya san wannan kallon kadai da sukeyiwa junan su yafi karfin gwaji balle kalaman da yake fita daga bakin haisam ba a jikin takardaryake ba. Sai yaja wani dogon numfashi ya juya yakalli sauran dalibai yace'' kuje ma karasa gwajin dadaddare'' ya fita ya nufi gidansa. Dalibai su ka firfitosuna gulmammaki'' wannan anya hannah da unclehaisam ba soyayya suke yi ba, ke kinga kallon da suke yiwa junansu uncle haisam kamar yarungumeta fa. Haka suka shiga dakunansukowacce ta nufi bangaranta. Rauda ta sami hannah a kwance akan gadonta tadora filo a kanta babu abinda take tunanowa saiidanuwan yaya haisam sai kuma tsananin mamakinyadda ya rike baitukan wakar nan da take yi masatun tana aji daya. Tace a ranta ashe ma'anar wakarkenan banda yarinta nake kai kaicewa nake rera masa ko da gangar jikina bata tare dakai ruhinayana tare da kai. Har nusaiba take cewa hannahmeye ruhi nace ina jin larabcine ashe ni ban sanhausa ba ce tsaba a lokacin . Ruhina , ruhina'' tsakitaji anyi a kanta ta bude ido sai taga raudaamurtuke. Tayi furgigit ta tashi zaune tace'' rauda har kun dawo? Rauda ta kaste ta tace''haka zaki cemana har mun dawo da acan zamu kwana? Komuma son maso wani muke yi da zamu bishigidansa? Yaya haisam dai yana da wacce yake sokuma an gama magana gara kowacce ta komakauyenta ta sami wani bakauyen ta aura
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31