Chapter 4
Chapter 4
ya ce "Tsaya yaro karma ka kirawomin wadannan dubunnai. Ta faruta kare wai anyiwa mai dami daya sata, yaro nagode madallah, sai anjima. Malam Habu ya juya batare da ya jira amsa daga bakin saurayin nan ba yadoshi inda Hanne ke zaune da saurinsa kamar zaikifa cikin gaggawa, ya ce "*Yar Baba tashi maza mu tafi ga magariba ta kawo kai. Cikin sauri ta mike yaciccibi akwati ya dora mata akai ya sungumi bokitida katifa suka kama hanyar get din fita. Sunyi takudaya biyu sai sai suka ji magana kamar daga samaance "A'a Baba ina zaku kuma? Su duka suka juyadan ganin mai maganar sai suka ga wannan kyakkyawan saurayin ne ya taso yazo wajensu.Malam Habu ya ce "To yaro me zamu yi in ba tafiyaba, dubunnan kudi fa naji kana kira, kuma ka tsayacak ka kalleni dani da dubu daya ma waye ya ajiyewani? Daman kansilan garinmu ne da maigari sukasani dole na kawo *yar nan makaranta, suka ce za'a aiko da kudin, na tabbata har ga Allah basusan kudin yakai dubunnai ba da suma basu tankaba. Kuma kudin gwamnati ba'a bashi babu yaddaza'ayi nazo na ajiye yarinya a makaranta babukudin makaranta babu kayan makaranta na ce abimu bashi zamu kawo ba. "Wannan ba zai yiwuba, inji saurayin. Malam Habu ya ce "To ka gani cewasuka yi na zo na kawo ta za'a aiko da kudin kumayadda naji kalamansa shi kansilan a tunaninsakudin makarantar bai wuce dari uku ba, bai sandubunnai bane kuma koda shine yazo ya kawotaaka kira dubunnan nan cewa zaiyi ta fasa karatun. Don karamar hukuma baza ta biya wadannanmakudan kudin ba.Saurayin nan yayi murmushi ya girgiza kaiya ce "Amma Baba bai kamata daga kirandubunnan nan ka kwasheta haka da sauri kacezaku tafi ba. Malam Habu ya fara jin haushinsaurayin nan, ya ce a ransa "Wai shin wannan dukzancen nan da ake bai gane ba ne? Makaranta sai da kudi kuma babu kudin jiran me zanyi, ko shi baisan babu ba ne? Saurayin nan yaci gaba da cewa"Baba kuzo ku ajiye kayan nan bai kamata ka juyada yarinyar nan ba, ai bai kamata ba. Ta cimakaranta har kun shigo cikin makarantar sannanku kwasa ku tafi ka ce ka fasa, babu fa abin da Uba zai yiwa *yarsa a duniya in ba ya bata ilimi ba,yarinya kamar wannan ai kamata yayi tanamakaranta tunda bata isa aure ba, me zata yi agidan? Malam Habu ya sake jin haushin saurayinnan kamar ya doke bakin da yake masa wadannankalamai ya ajiye bokiti dake hannunsa ya ce "Yaro, wai shin a harshen Hausa idan akace babu me akenufi? Yayi murmushi ya ce "Baba kenan, na gameduk dalilan da kake nuna min yanzu, ni kuma abinda nake so na rokeka shine ka fasa tafiya da itatunda ka kawota har cikin makarantar ka kyaletatayi karatu. Abun da ya kamata ka tambayeni shine tayaya zata yi karatu tunda babu kayan makarantababu kudin makaranta? Malam Habu ya ce "toyanzu nasan ka gane babu,ta yaya zata yi karatubabu kudin makaranta babu kayan makaranta?Kyakkyawan saurayin nan ya ce "Yauwa Baba kayitambaya mai kyau, amsar tambayar ita ce in Allah Yaso Ya yarda Hanne zata yi karatu in har kaamince ka yarda zaka ringa turo ta makaranta dazarar hutu ya kare ba sai ta fara ba kace baza tadawo ba ka cire ta.Idan kayimin alkawarin haka kuzo ku ajiyekayan nan ka tafi ka barta. Malam Habu yayi jigumyana tunani, a ransa ya ce "Wannan yaron me yakenufi? Hanya zaiyi mana a dauki Hanne babu kudinmakaranta babu kayan makaranta ko kuma yayaza'ayi? Bana tunanin dai shi zai biya mata kudin makaranta harda dubunnan da ko karamarhukumar mu baza ta iya biya mata ba yaddazamanin nan ya canja masu kudi basa taimako,babu yadda za'ayi yaron nan ya zare makudankudi ya baiwa yarinyar da bai santa ba bai tabaganin ta ba bazan bar *yar Baba a makarantar nan ba in tafi ta wulakanta ba, wacce bata san hanyarda zata bi ta koma gida ba idan an korota. Yanzuakan Naira goma masu mota suke kokarin sudanneni su dauka ina ga dubunnan kudade gakayan makaranta har kala hudu waye zai dinkomata? Saurayin nan ya katse Malam Habu daga tunanin da yake yi ya ce "Baba tunanin me kake yine? Karka yi kokonto ba zaka yi dana sanin barinHanne a makarantar nan ba in Allah Ya yarda babuabin da zai sami Hanne sai alheri da kwanciyarhankali ka tsarkake zuciyarka ka danka Hanne gaAllah wanda a koda yaushe Yana kallon halin da bayinsa suke ciki na kunci kona farin ciki, sannanka danka Hanne amana ce a wajena. Ni kuma namaka alkawarin zan karbi amana na rike. Cikinsanyin zuciya da gamsuwa da kalaman saurayinnan Malam Habu ya juya ya kalle shi ya ce "AllahSarki duniya wani ya munana maka wani kuma ya dadada maka. Yaro tunda ka ce Allah na yadda kakuma ambaci amana, amana kalmace mai girmamai wuyar rikewa kace zaka rike tsakaninka daAllah, na gode yaro, Allah Yayi maka albarka Yabiya maka bukatunka. Abin da kayi min UbangijiAllah Yayi maka fiye da haka, *yar Baba muje mu ajiye kayan. Suka juya harda saurayin wajen bencinda yake, Malam Habu ya kama akwatin dake kanHanne ya sauke mata ya juyo ya kalli saurayin nandake zaune akan benci ya ce "Yaro bazan gaji da yimaka godiya ba.Madalla Allah Ya yi maka albarka zan tafi nabarku lafiya, af kaga ko sunanka ban tambaya ba.Saurayin nan yayi murmushi ya ce "Sunana Haisam,Baba. Malam Habu ya ce "To madalla. Ya juya yakalli Hanne wacce ke tsaye idonta ya ciko da kwallaya ce "*Yar Baba zan tafi na barki ga Allah na barki ga wannan bawan Allah. Sai ta rushe da kuka takoma kan akwatinta ta zauna ta kifa kai a gwiwatana kuka. Hawaye ya kecewa Malam Habu ya ce"Nima ba'a san raina zan tafi na barki ba Allah Yakaddara saduwarmu. Ya juya ya kalli Haisam ya ce"Yaro mai wuyar suna har na manta sunan(fatan Yayarmu ma Zee zata iya rike sunan, kodayake ita 'yar birnice, loz) na tafi, sai wata rana. Haisam ya ce "To Baba Allah Yakiyaye. Malam Habu ya juya ya fara tafiya yana facemajina yana goge hawaye da gefen babbar rigarsa,sai yaji muryar Hanne ta ce "Baba ya juyo ya ce"*Yar Baba. Ta taso da gudu ta karaso inda yake takama gefen zaninta ta kwance sai ta dauko wasu cukurkudaddun *yan Naira ashirin guda hudu tace "Baba karka tafi da kafa gashi ka hau mota.Haisam dake zaune har yanzu akan benci yanakallonsu sai da yaji kwalla ta cika masa ido dontausayin Uba da *yarsa. Malam Habu ya ce "AllahuAkbar, *yar Baba Allah Yayi miki albarka. Allah Ya baki ilimi mai amfani, kinji? Waye ya baki harmurtala hudu? Hanne ta ce "Dana shiga makwabtanayi musu sallama suka babbani wasu, saurankuma kudina ne da nake tarawa tun na yawonsalla. Malam Habu ya ce "Kya bani duka ingomurtala biyu ni na dauki murtala biyu, kema ki rika siyan *yar gyada kya zauna haka kina ganin yarasuna siye-siye ke bakya siyan komai? Hanne ta ce"A'a Baba murtala biyu baza ta kai ka gida ba, banaso ka shiga mota kudinka bai cika ba, kana rokonayi maka ragi irin na dazu. Malam Habu ya sakekecewa da kuka ya ce "To *yar Baba na gode na tafi na barki ga Allah baki da kowa,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31