Chapter 2
Chapter 2
ce "Ko dai waccan makarantar ceta gwamnatin jiha suka rasa suka shigo nan. Koda yake ko can dinma dakyar su kwashi wannan.Sannan na karshe ya ce "Ku dai ku tsaya babumamaki nan din taci abun ai na Allah ne, Malam inatakardar shaidar taci nan makarantar? Malam Habuya ce "Mu babu wata takardar shaidar cinmakaranta a tare damu, ni dai kansilan garinmu yazo har gida ya ce jarabawar da *yata tayi a birnita fito kuma duk karkararmu ita kadai taci, maigarinmu ma ya turo inje ya shaida min ya ce lallai-lallai nan taci in kawota, ya ce min makarantun'yan mata a Kazaure guda biyu ne data gwamnatintarayya data gwamnatin jiha, ta gwamnatin tarayya taci in kawota. Amma ni babu wanda yayi minzancen takarda. Suka sake kecewa da dariya. Dayaya ce "Malam sai kuyi waje don baza ku shiga bababu takardar shaida, ku koma ku sami kansila komaigarin naku su baku takardar shaida sai kuzo kununa sannan mu barku ku wuce. Yau gashi kusan wata daya ke nan da aka riga aka gamakawo yara har sunyi nisa da fara karatu, kai saiyanzu kake kawo 'yarka. Malam Habu ya ja 'yarsaa sanyaye suka yi waje, zuciyarsu cike damummunar damuwa.Hakika Nigeria muna cikin wani hali lokacin da yake ajiye kayan dake hannunsa a waje,yakamawa 'yarsa akwatin dake kanta suka saukekasa. Suka tsaya suka yi cirko- cirko suna kallon masu gadinnan,wadanda har yanzu basu daina yabo musubakakenmaganganu ba. Malam Habu ya nisa ya ce "AllahSarki rayuwa, Allah Ka fimu sanin halin da muke ciki kaizaka fitardamu, 'yar Baba zauna a gefen akwatinki kinjikafin mugayadda Allah zai yi damu. Isa kansila da maigarisuka ja mana wannan wulakancin. Ni nasan a rina, shi yasa dafarko nakifur da akace za'a kaiki birni daukar jarabawa,kuma kema daakayi kiranki me yasa ki amsa musu? Kika ce kinason karatun, ga irinta nan ai. Hanne ta zauna a hankali jikintayayi sanyi,wanda ko yatsanta wuyar dagawa yake yi mata.Zuciyarta cikeda damuwa, babu abin da take tunawa illakomawarta gida haduwarta da iya Abu kishiyar uwarta da'ya'yanta.Irin tsananin azabar da suke gallaza mata dabautar ta din daake tamkar baiwa alokacin cinikin bayi. Ta ce aranta "Da inamurna zanzo makaranta nabar gidan da banahutawa kuma ban taba hutawa ba sai yanzu. Gashi yanzumakarantar masun koro mu dole mu koma gida. Taci gaba da tunairintataburzar da aka sha da Mahaifinta kafin Iya Abutabar su suka fito daga gida zuwa makarantar nan. Wai itaidan Hanneta tafi babu mai yi mata aikace-aikace su sharawanke- wanke,debo ruwa a rafi ko tuka-tuka. Saboda haka nemataki fur wai baza a kawo Hanne makaranta ba. 'Ya'yantakuma garda-garda maza da mata suna zaune ko tsinke basadaukewa saiHanne wacce bata da uwa a gidan. Allah Sarkihawaye ne ya kecewa Hanne yayi ta zuba daga idanuwanta.Maganar dadaya daga cikin masu gadin keyi ita ta katse tadaga tunanindata dulmiya tana yi. Taji kamar daga sama yanacewa "Kai kauyawa ma da rashin tunani suke dan kawai ance'yarka tacimakaranta sai ka taho ka zabi makarantar data yimaka kawaika sako kai, dubi yarinyar daya kawo sai kace maizuwa tallar kalwa riga a cukurkude, zanin daga kasa ya nadekamar annade tabarma. Takalmin kafarta harda leda tadaure waye zaice daliba ce. Daya ya ce "Danmarar data ci kai kacedandali zata, ta daure kugu tamau. Ina jin ma basu san anadinkakayan makaranta ba (Uniform) balle takalmikambas da safa.Hanne tayi ajiyar zuciya ta hadiye yawun da ya cikamata bakinta tayi shiru, kanta a sunkuye a kasa.Tace a ranta "Lallai ko nafi maye kwakwa dole nahakura damakarantar nan harda kayan makaranta akedinkawa. Wayezai dinka min? Ta sake kallon kayan jikinta tace aranta "Kayan sallar tawa shine suke cewa duk a cukurkude? Niina ganinnayi ado kowa a garinmu da muka zo wucewayana cewaHanne yau kuma ina zaki kika ci ado haka? Su anankazan- kazan suke ganina ashe, dole mu koma gida asheban rabu dawahalar Iya Abu ba. Kuka ya sake kece mata hardashessheka. Malam Habu ya kalleta fuskarsa cike dadamuwa ya ce "Yi shiru 'yar Baba bari zamu san yadda zamuyi mukoma gida. Ni yanzu ke nake ji gashi kudin da yarage mun aaljihuna saura Naira ashirin kacal. Da niyyatainnakai ki makarantar in zan koma gida sai in hau mota daganan zuwatashar Kazaure daga can kuma sai in kama hanyada kafa harBabban- mutum (garinsu) idan dare yayi mun insami waje in kwanta washe gari na tashi naci gaba. Har dai inkarasa kokwana nawa zanyi a hanya. To yanzu ba zai yuwuba tundagaki, sai dai kawai mu shiga mota muje tasharKazauren, ko a bakin tashar sai in siyar da akwatin nan ko katifarkoma dukamu samu muyi kudin motar komawa gida. Hanne tazabura tace "Ka siyar da akwati da katifa fa kace? Kansila aisai yasa a kamaka, cewa yayi fa gwamnati ce ta siya ta bani.MalamHabu yayi kasake yana tunani na wani lokaci maitsawo can yace "To laifin waye? Shi kansila da maigari basu sanda kudi za'a zo makarantar ba, babu wanda ya bamu kosisinsa,kansila kullum yana min alkawarin zai je ya karbokudin da zaayi miki siyayya da kayan makaranta da komai dakomai, har cewa yayi motar gwamnati ce zata zo ta kawoki..Daga karshe ya zo ya fara hanya tun dagagwangwarmarakwatin nan da katifa da bokiti babu abunda yakara kawowa.Bansan wacce shawara suka yi da maigari ba kumadaga karshe suka ce inzo in kawoki haka za'a aiko mikikayayyakindaga baya. To yanzu gashi takardar makarantar cebabu aka yimana korar kare ina ga idan muka shiga ciki aka cemu kawo kudi, muka ce babu ai sai a rakomu da duka. CikinsauriHanne ta ce "Lah Baba na tuna jiya maigari ya aikoda watatakarda da yamma ya ce ta makaranta tace, bakanan. Na karba nasa a akwatina ko itace suke tambaya?Malam Habucike da mamaki da zumudin dauko takardar ya ce"Haba 'yarBaba kina 'yar karamarki kike mantuwa, tun dazufa ake maganar takardar duk baki tuna ba. Yi maza kidaukotakardar in nuna musu ko itace takardar. Hanne tadagaakwatin da sauri ta bude, babu komai a ciki saikayan sawarta kala biyu a cukurkude suke kamar anyi sukuwardoki a kansu.Ta binciko can kasan akwatin ta dauko watadoguwar takardafara ta mikawa Babanta. Malam Habu ya karba dasauri ya doshi wajen masu gadin nan yana cewa "Ga daiwata takarda a cikinakwatinta saiyanzu ta tuna ashe mai gari ya aiko da ita jiya kudai ku duba ku gani ko ita ce. A yatsune daya daga cikinsu yakarba yaduba yana dubawa kuwa yaga takardar shaidar andaukiHanne Habu Imamu a F.G.G.C Kazaure ce wato(Admission letter) Sun sha mamaki kwarai da ganin nanmakarantar kuwataci ba batan kai suka yi ba. Cikin sakin fuska sukayi musuizinin su kwaso kayansu suzo su wuce. Cikinmurna Hanne da Mahaifinta suka kwashi kayansu suka wuce izuwacikinmakaranta. Basu tsaya a ko'ina ba sai a bakin wanibabbangini wanda ya kunshi doguwar baranda da ofishinMalamai.Babu kowa a wajen hatta leburori masu share-share da goge-goge duk basa nan, wajen tsit kamar babubil'adama. Sukasami gindin wata bishiya suka sauke kayansu.Hanne ta hau kan akwatinta ta zauna Malam Habu ya ce "To fawannanshine ko in kula, yanzu kuma ina zamu dosa kokuma wazamu tambaya? Ni wallahi abun nan na makarantarbokon nan ya ishe ni daga nan sai can ana tsattsare ka datambayakamar a lahira mun gama da masu gadi yanzukuma Allah nekadai Ya san wa zamu hadu dashi, kai Allah Yakyauta, wannan shine ake cewa ba shiga ba fita wai anbawamahaukaci gadin kofa.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31