Chapter 25
Chapter 25
fada maka ka jawa yarkahanna kunne ta kiyayi mijina idan ba haka ba nizan zamo ajalinta domin zan iya kashe duk yarinyarda zata rabani da haisam abun sona. Kuma ka cireyarka daga makarantar nan domin idan bata bar makarantar va haisam ba zai bar makarantar ba yarabu da ita. Muddin hanna ta sake komawamakarantar to kuwa har makarantar zan bita inzartar da abun da na yi niyya. Ba tana takama itakyakykyawa bace to zan kwara mata wani abuafuskarta {acid}fuskar ta sale ta kwakwkwabe har makarantar zan tarar da ita in yaso sai inga fuskarda zai sota. Don soyayya hannah take yi da mijinava karatu ba. Har sakamakon jarabawar kanwatayake dauka ya bata tazo ta daya a ajinsu. To na gajiwannan shine lokaci na karshe dana bawa hannahidan taki ji ta koma makarantar to wallahi ta kuka da kanta'' malam habu ya sharbe hawaye yaci gabada cewa'' da wata kanwarta yar makaranta tanasanye da kayan makaranta irin naki yar baba itamatana taya ta suka yimin tas, iya abu na ihu tanadariya tana cewa daman ta sani ba tun yau bahanne karuwanci aka kaita tayi ba makaranta ba yanzu gari duk ya dauka maganar ake yi don agaban mutane aka yi haka. Tace hannah taci sa'ada bam sameta ba da sai ta faffalla miki mari sannansuka shiga mota suka tafi. Hannah bata iya cewakomai ba sai ta sunkuyar da kai kasa tana kukamalam habu ma kukan yake uwar biyu ta matse hawaye tace'' kuyi shiru, ku daina kuka wannanduk abune na shirme da karya ita wannan yarinyardata zo ina tunanin matar da malam haisam zai aurace take ganin son hanna yake alhali kowa yasanhaisam a matsayin yaya koma ince uba yake awajen hanna tun tana karama fa inah, ai zancen so ma bai taso ba. Hannah karatu take a makarantababu wata soyayya daga wannan hutun ma bazasu sake dawowa har sai sun gama makarantar makwata kwata saura wata bakwai su gama. malam habu ya zabura yace'' wacce komawa aihanne tazo kenan baza ta koma ba ina wanizancen saura wata bakwai hanne ta gama aikosaura kwana bakwai ne hanne ta gama karatuntabayan a gaban mutane aka ce ba karatu take yi amakarantar soyayya take yi sannan in bar yata ta koma ai sai a dinga cewa tana can tana iskanci harwata bakwai ba ta komo gida hutu ba, ni daiabunda zance muku uwar biyu ke da wannan yarohaisam allah yayi muku albarka amma hanna bazata sake koma wa ba karatun ya isa haka dukkawayenta harma da kannanta duk sunyi aure gara itama in hadata da wani a dangi tayi aurentabaki alaikum kafin a kone mata fuska. Damanabunda muke ji a redio gaskiya ne ace an fesawawani ko wata wani ruwa a fuska ya kwakwkwabogaske ne to ba zai faru akan hanne ba. Karatun datayi na baya ya isa nagode madalla'' cikin rudewa uwar biyu tace'' haba malam habu yaya zaka yimana haka ? Baka kyauta masa ba yarinyar nanduk zance take haisam ba zai barta taje gurinhanna ba balle tayi mata wani abu. Bama a barinkowa yaga dalibai in ba ranar bisitin ba dokarmakarantar ce'' malam habu ya mike ya shiga gida yana cewa'' nifa na gama maganata uwar biyu kiyihakuri ki bar maganan komawar hannemakaranta. Ai ko karan hauka ya cije ni ba zan baryata taje inda za'a halakata ba ina hanne ina kishida wadannan gogaggun yan burnin masu kudi.Tunda tana ganin mijinta son hanne yake ai sai a hakura da taimakon na baya ma allah ya saka'' yashige ya bar hannah tana matse hawayen dakeidanuwanta da wani farin hankici dake hannuntatace uwar biyu'' kyale shi ya tsorata ne kafin hutuya kare zai yadda idan na wayar masa dakai ahankali na lallabashi sai dai idan hutu ya rage sati guda kizo don muji mai zai ce in yaki yadda sai daiyaya haisam yazo ko kuma ya turo principal idankuma yaki yarda na shiga uku karshen karatunaya zo. Hannah ta rushe da kuka, uwar biyu tace ''yadda za'ayi shine haisam zan turo yazo garin nanmahaifinki ya kalli kwayar idonsa ya ce ya hanaki ki koma makaranta, haisam zaizo da kansa. A hakahannah da uwar biyu suka yi sallama. Hanna tayitayi da uwar biyu ta shigo cikin gida ta huta sannanta tafi uwar biyu tace baza ta shigo ba ina zata iyashigowa wajen iya abu masifaffiyar matar da zataiya kashe mutum ma don rashin imani. Hannah ta raka ta har tasha ta shiga mota sannan hanna tadawo gida. Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 GANGARJIKINSA NA AURA 1 Part 4 Posted by ANaM Dorayi on 02:25 PM, 30-Apr-15 Under: Gangarjikinsa ta Aura A zaure malam habu ya shimfida tabarmar kaba dawani yagulallen filo da zanin gado irin na da da dadinnan shekara aru aru da suka shude. Nan neshimfidarsa da yake kwana nan ne dakinsa danduk dare duk sanyi da damuna a nan yake sabodaiya abu ta mamaye dakunan gidan. Dakinsa din ya barwa hanna data girma ya dawo zaure don da datana yarinya tare suke kwana a dakin. Ko dayaushe hannah zaka ganta a zaune a gefenbabanta tana lallashinsa tana wayar masa dakaigame da makarantarsu. Tana nuna masamuhimmancin karatu da kuma irin bacin ran da haisam zaiji idan bata koma ba.Ta kwashe labarun abubuwan da suka faru tuntana aji daya har tazo aji shida yadda haisam yakekula da ita da irin tataburzar da aka sha yi akantada dalibai da malamai har ya kwatar mata yancintababu mai dukanta ko zaginta yanzu, kuma yayialkawari zai iya kashe ko waye yake son ya takura mata. Malam habu ya gamsu sosai da bayananhanna ya kuma san haisam ba zai yadda a cuce taba. Hutu ya rage sati guda sai ga uwar biyu ta dira agarin su hanna ta iske hanna da mahaifinta a zaurea zaune zance daya dai suke ta nanatawa kullumshine zancen ya barta ta koma makaranta. Bayansun gaisa da uwarbiyu ta fadi abunda ke tafe da itacewar tazo ne ta tafi da hanna hutu ya kare sai malam habu ya kekashe idanuwansa ya ce shifababu inda hanna zata je. Hanna tayi mamaki da tajiya fadi haka yanzu bayan da ya yarda da tayi masabayani sai kawai hanna ta rushe da kuka, magiyarduniyar nan uwar biyu ta dinga yiwa malam habuamma yaki yarda daga karshe uwar biyu tayi musu sallama ta tafi. Tana isa kazaure ta wuce gidan susafiyanu abokin haisam bata sameshiba ance yanakano sai ta koma gida ta zuba ido ko allah zai jehomata haisam ko safiyanu idan zasu kawo sayayyarhanna ta makaranta tunda sunsan hutu ya karezasu kawo. Har ana gobe a koma makaranta uwar biyu bata ga safiyanu ba balle haisam. A can kuwahanna hankalinta ya gama tashi taji shiru yayahaisam baizo ya taya ta rokar babanta , sai ta daukashima yayi fushi ne yace to a bar masa 'yarsa kartayi karatun mana. Da la'asar likis hanna damahaifinta suna zaune akan lintsimemiyar tabarmar kaba a zauren kasa da rufin ciyawa hanna kukatake yau tun safe. Malam habu lallashin duniyar nantayi shiru ta hakura tama cirewa ranta makarantardon shi ya gama magana bazata koma makarantaba . Taki ci taki sha sai kuka take rafsawa. Kwatsamsuka ji sallama daga idon na da hanna tayi sai tayi ido hudu da yaya haisam , safiyanu da uwar biyusuka yi sallama suka shigo. Da sauri hanna tadauko musu tabarma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31