Chapter 20
Chapter 20
ta danyi mata bulala uku labourprefecr tayi mata biyu. Ga yarinyar can ma a aji tana daukar darasi babu wani zancen kisa'' haisam yafusata yayi kan sahabi da fada yana cewa'' karyazanyi musu? Yarinyar da duk makarantar nan babumai shirunta da ladabi yaushe zata ce zatayi fada dahead girl ? Kawai baza ka tsaya kayi bincike ba donsun gaya maka karya da gaskiya shine zaka yarda, kaje clinic kaga jikinta a farfashe bata san ma indahaiyacinta yake ba . Sahabi ya ce '' madam donallah ki raba mana rigima ki aika clinic a dubo idanakwai wata marar lafiya. Babu kowa ta warke tamike ba'a gabanmu hannah tazo ta wuce ba dazuko ba hannah ba ce wacce kake cewa an kusa kasheta ? Kuma kai duk wannan hakilon da kakecewa akan hannah saboda kai saurayinta ne fa shiyasa kake wannan sauran da ake duka ka tabamagana ? Principal ta lura maganar babba ce saimanya sai tace da juwairiyya ta tashi ta tafi zata aikoayi kiranta. Fuskar juwairiyya cike da murmushi ta fice principal ta kalli haisam tace'' kwarai tun ba yauba ansha fada mun kana soyayya da hannah.Dokar makarantar nan an hana daliba da malamiyin soyayya . Yanxu na gane manufarka don andaki budurwarka shi yasa kayi magana ko? Dagayau zan sa c.i.d kada ka kuskura in sake jin ance kana soyayya'' haisam ya fusata, ransa ya bacizuciyarsa ta hau tafarfasa. Ya dakawa sahabi tsawayaje har gabansa yana nuna shi da hannu ya ce''kai sahabi karya kake yi ni nafi karfin ka yi minsharri kai da juwairiyya zaku gane kuranku amakarabtar nan. Ni kake cewa ina son hannah ko ? Bayan da bakinka kazo ka sameni kana rokona inhadaka da kanwata hannah kana sonta naki nacekabarta tayi karatu ashe kana kullace dani kasaaka yi mata wannan dukkan ko ? Ke kumaprincipak kin goyi bayansu sun daki yar mutabe abanza ko ? To ni sai na daukarwa hannah fansa da kaina'' ya kada kai ya fice. Sahabi ya juya ya kalliprincipal yace'' kinji kuma inda ya lauya maganako ?tace ''kyaleshi bayan kai ma mr.ojo ya fadamun cewa son hannah yake don haka kaci gabada kula dasu. Haisam ya nufi staff qurters ya shigagidansa ya zauna a falon yana huci kamar ya kashe kansa yake ji saboda tsananin bakin ciki yau kodarasi ba zai je yayi ba. Yini yayi cur a gida ya kudiriniyyar zai dauki fansa akan duk mai hannu a cikinwannan al'amari , wai sahabi ne zaiyi masa hakasahabin da ke zuwa har gida yace ya taimakeshi yashawo masa kan hannah wai juwairiyya da kanta take cewa rashin kunya hanna tayi mata zata yidambe da ita wai shine tayi mata bulala uku itakuma principal da kanta take bin bayansu bayantasan hannah tasan halinta tasha yin kwatance daita a wajen assembly akan tafi kowa da'a da ladabishine har ta yarda da kintsin da suka yi mata ko da kyau, haka haisam ta dinga nanatawa a zuciyarsa .Haisam ya dinga nanatawa a zuciyarsa. Haisam baifita daga gida ba sai da yamma misalin karfe biyarya shigo cikin makaranta a lokacin dalibai sunaprep din yamma ya wuce kai tsaye ajinsa don yagajikin hannah, a zaune ya ganta a kan kujerarta ba laifi jikin burdin bulalan ya dan warware zazzabinya sauka sai dai bata iya bude idanuwanta sosai. Yace da ita'' hannah ya jikinki ? Cikin sanyin muryatace'' da sauki'' yace kinsha magungunan naki?Tace eh nasha'' wani masinja ya leko ajin yacemalam haisam kazo inji principal. A fusace haisam yace meye kuma? Dan aiken ya ce'' waya aka bugomaka zaka dauka a ofishinta'' ya ce gani nan zuwahaisam ya juyo ya dubi rauda da nusaiba ya ce'' kudinga kula da hannah ku tabbatar tana cin abincikunji ko ? Suka amsa da'' to zamu kula da ita.Sannan ya fita daga ajin ya nufi ofishin principal yana isa ofishin yayi sallama ya shiga ya gaisheta amurtike. Tace'' yayanka ne habibu yake son yayimagana dakai nace ya kira nan da minti biyar za.akira....'' kafin ta rufe bakinta wayar ta fara karahaisam yasa hannu ya dauka ya gaishe fa yayahabibu yaji da kyar habibu yake amsa wa rai a bace habib yace kai haisam mu fa ba yara bane kananakana ji ko? Saboda me zaka dinga yi mana wasa dahankaki ? Kace shekara uku zakayi a makarantarnan sannan ka bari yanxu shekara uku sun cika,Saboda me zaka dinga yi mana wasa dahankali ? Kace shekara uku zakayi a makarantarnan sannan ka baru yanzu shekara uku sun cika,last week da kazo aka gaya maka cewar ka barteaching dinnan ka dawo gida da kamfanoninbaba aiki yayi mana yawa muna neman ma'aikata, kace da zarar ka koma kafin karshen watannanzaka dawo gida kabar koyarwa gashi munji kashiru. Kujerarka na nan na jiranka ga ramla nan najiranka itama. Har anyi bikina da jidda har ta haihu'yar mutane na zaman jiranka kazo ayi bikinku. Waishin me ka zamar da mune, har nawa kake da zaka dinga juya mu ? Don haka karka sake nazomakarantar nan da kaina ka rubuta takardar barinaiki kabar koyarwa nan ka dawo gida muna nanmuna jiranka. Kai baka kishin dukiyar ubanka saigwamnati zata baka da kake mata wannan wahala,me kake nema ka samu wanda a gidanku baza a baka ba ? Haisam ya fusata yace'' ka gamamaganarka ? To bari in fada maka gaskiya ba zanbar koyarwa ba ina nan bazan dawo gidan ba'' yakifa kan wayar ya fice. Principal ta bishi da kallo harya fice. Wayar ce ta sake yin kara tasa hannu tadauka taji habib ya ce''ina haisam din? Tace ''ya fice'' ranki ya dade kema harda laifinki tun rannanbaba ya kiraki har gida ya ce kiyi murda murda kisaa koreshi daga makarantarki zai biya ki ko nawane. Kika ce bazai yu ba. Wannan yaron ko kasheshiza ayi bazai bar makarantar nan ba. Wanne irinlallashine ba'ayi masa a gida ba yaki ya bar koyarwa'' principal ta nisa tace'' habib tunda kajinace bazan iya sawa a kori haisam ba to babuyadda zanyi saboda wannan makarantar tagwamnatin taraiya ce daga kololuwa aka daukihaisam haka kuma korarsa sai daga can abuja.Dana bincika ma babban director na federal shine ya dauke shi aiki alh.sabi'u auwal abokinbabankune ko? To babu kuwa yadda za'ayi nahada baki dashi a koro haisam daga makarantarnan habib ya ce''zanzo makarantar watakila nan dasati biyu, idan na dawo daga tafiya dole ne ma yabar makarantar donyaga ana yi masa sakwa sakwa ya dauka tsoronsa ake yi don ni banga uwar dayake samu ba a makarantar'' a haka suka yisallama suka ajiye kan wayoyin. BAYAN SATI asheda sahabi ba kadai akwai malamai da yawa dasuke son hannah. Sai yanzu suka dinga baiyana.Ranar talata data zagayo haisam da sauran malamai uncle sahabi da uncle yusuf suna zaune a gindinbishiya da prep din yamma sai uncle yusuf ya aikawata yarinya ya ce taje s.s. 1a ta kira masa hannahabubakar . Haisam na zaune yana tunanin lafiyayake kiran hannah. Hannah ta karaso tazo tasurkusa ta gaishe su uncle yusuf bai amsa ba yace'' hannah yau zan nuna miki karshen taurin kai,girman kai daji da kai. Don haka kije ki karyo bulalakatuwa mai kauri dai dai tsawanki ki kawo min''haisam na zaune yana kallonsu hannah ta tashijikinta a sanyaye ta nufi dawa, can ba dadewa tataho dauke da wata zabgegiyar bulala. Tazo ta durkusa ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31