Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 24

Chapter 24

Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

amma haisam sai ramla. Hannah tace'' rauda me ya faru ,wani abun akayi ? Nusaiba tace'' ke rauda meyehaka wasan kwaikwayo ne fa kowa yasan gwajine ba gaske bane. Wai ke rauda me yasa bakya sona zauna lafiya ne ? Rauda tayi tsaki ta fice tana cewa'' duk gulmace gulmacen da ake ina sane. Dan iskan kauye yafi na burni iya iskanci da rashinmutunci ai. Hannah ta fashe da kuka, tayi kuka kamar ranta zaifita. Nusaiba na lallashinta da kyar hanna tayi shirusuka je suka yi alwalar magaruba. Bayan sallarisha'i sunci abinci karfe takwas dai dai sai suka jesuka kora dalibai kowacce ta fita ajinsu don yinprep din dare, uncle haisam ya fito daga gidansa takwas da rabi yazo ya kirawo yan hausa club donsuzo su karasa gwajin wasan kwaikwayon da sukeyi. Ta bayan wundo ya hango rauda tsaye akanbencin hannah tana ta gurza mata rashin mutuncihar cewa take da ba'asam asalin balbela ba sai tacemadina ne garinsu. Yaga hanna zaune tayi shiru tana hawaye, ran nusaiba ya baci ta taso tashigarwa hannah kamar zasu daku da rauda. Saihaisam ya leko ta wundo yayi musu tsawa ya ce sufito waje yana son ganinsu. suna zuwa gabansa kallo daya suka yi masa sukasan babu wasa yau a murtike yake kasancewarsunsan bacin ransa babu kyau sai kowacce ta fararawar jiki. Ya daka tsawa yace kowacce tayi kneeldown bayan sun yi ne ya tambayi nusaiba me yafaru. Nusaiba ta zaiyana masa dukkan abunda ya faru tsakanin rauda da hannah tun daga yammahar na yanzu ya juya ya kallo rauda yace'' raudahakane ? Ta gyada kai gami da tabe baki tace''haka ne kuma gaskiya na fada'' haisam ya fusataya kaiwa rauda mari tayi sauri ta kwanta a kasa baisameta ba. Tace' yaya haisam yau ni zaka mara akan hannah? Haisa yayi shiru hannayensa a cikinaljihu kansa a sunkuye a kasa. Can ya dago yace danusaiba ta tashi ta shiga aji. Ya dubi rauda wacce kedurkushe a kan gwiwarta a gabansa rauda tarushe da kuka. Haisam yace'' rauda tun ba yau ba,tun kuna aji daya na lura kin kafawa hanna karan zuka a makarantar nan. Yanzu kece kadai kikarage a cikin masu takurawa hanna zan iya daukankowanne irin mataki a kanki muddin baki fitaharkar hannah ba ki kiyae, idan kuma kin ki ni zanfiki farin ciki don zaki ga abunda zan zartar a kanki.Ko amratu 'yar shekara bakwai zan iya.hukuntata muddin ta nemi takurawa hannawannan alkawari nayi wa allah kuma sai na cika shidon hanna amana ce a wajena'' kamar a mafarkirauda take jin kalaman yaya haisam, tana fada aranta lallai abun nasa babbane da gaske yake'' daga karshe ya ce ta shiga aji tana sharbar kuka tamike a fusace ta shiga aji. Ya shigo shima ajin yakalli hannah wacce ido yayi mata jawur don kukayace hanna ki kira sauran yan hausa club ku tahohall ku sameni mu karasa rahazal din. Cikin ladabihannah ta amsa masa. Ya fita ya nufi hall. Hannah cewa'' rauda muje hall yaya haisam na kira'' tadago ta harari hannah tace'' bazan je ba kuma nafita daga club din ko za'a sani dole ne? Hanna zatace wani abu nusaiba taja hannunta tace ''kyaletamu tafi mu kira sauran. Hutu ya kusa karewa har ana shirye shiryen farafirst term examination. Kowacce karatu takehaikan, sunyi jarabawa an basu sakamako kafinranar hutu. Hannah ce tazo ta daya a ajinsuwannan karon, rauda ta biyu nusaiba ta uku ranarhutu bayan anyi assembly hutu da wur wuri kafin kowa ya fara tafiya haisam yazo ya sami hanna,rauda nusaiba da wasu kawayensu a zazzaune akan barandar hall suna ta hira. Bayan sun gaisheda shi sai ya ce'' hannah taso ga safiyanu yazodaukarki, idan muka saukeki a gidan uwar biyuzamu wuce dashi dan musa can jahar katsina acan yake neman aure zamu kai kayan gaisuwarsurukai'' su duka suka kyalkyale da dariya. Hannahtace ''oh yaya safiyanu daman aure zai yi ko ya fadamana sunanta ranar nida nusaiba muka ga hotontaa motarsa muka ce budurwarsa ce ya ce wai shi babudurwarsa bace'' nusaiba tace'' haka ne kuwa a bayan hoton an rubuta dan musa har nake cewadan musa kuma sunan mace dan musa ya ce ehhaka sunanta. haisam yayi dariya , sannan ya juya ya kallo raudatasha kunu ta kawar da kai gefe daman tundaakayi wannan abun bata cika yiwa hannahmagana musamman idan taga haisam da hannah.Ga uwa uba hannah ta kwace mata position tazo tadaya , sai take jin haushin kamar ta kashe hannah. Haisam ya ce'' rauda ni ba kano zanje ba sai mundawo daga danmusa don gida ma nace kada aturomun da mota auwal zaizo daukarki ko direba?Tace '' sai dai direba yaya auwal yanamaiduguri''yace''oh haka ne fa, to ki gaishe dasuhajiya sai wahen jibi zanzo kanon. Idan muka tafi yau ba damar muyi tafiyar dare dole mu kwanasannan washe gari mu dawo kazaure wata kila inkwana a cikin gari jibi muje kanon da safiyanu .Rauda tace zasu ji . Allah ya kiyaye hanya. Hannahta kira wasu juniors suka dauki jakunkunanta sukazuba mata a mota. Tayi wa kawayenta sallama tana zolayarsu su tana cewa yau itace farkon tafiya dukmakarantarn ta barsu su yan kwantai ne. Rauda tatabe baki tace'' yanxu wata kila har kowa ya isagida ke baki isa gida ba, saboda hanyar garinkukwalta ce sambel ba kasa ba'' hannah da nusaibane kawai suka gane rauda bakar magana ta fada, wato hannah bakauyiya cekenan take nufi saihannah tayi murmushi kawai ta tafi ta shiga motatana dagawa nusaiba hannu har suka fita get . a gidan uwar biyu su haisam suka sauke hanna ,haisam ya shiga cikin gidan bayan ya bawa uwarbiyu kudaden motarsu da wanda zasu kaiwamahaifin hannah suka yi godiya yayi musu sallamaya juya ta tafi har yaje kofar fita ya juyo yace '' koyanzu zaku tafi mu ajiyeku a tashe'' hannah tayi sauri tace yaya haisam da yamma zamu tafi ina soinje gidajen kawayena a nan cikin gari. Yayimurmushi ya ce'' wato akuyar daure ta samu sake,su hannah an iya yawo ko? Su duka suka yi dariyasannan ya fita. Damisalin karfe biyar uwar biyu dahannah suka isa babban mutum , suka je suka iske gida a hargitse anyi tashin hankali. Malam habumahaifin hannah kuka wiwi. Cikin rikice da rudanihannah ta tambaya meya faru babanta yake kuka.Iya abu ta tuntsire da dariya tayi buda da shewatace'' tambayi ubanki. Karshen tuka tiki tik yauallah ya nuna mana gaskiya'' hankalin hannah da uwar biyu ya sake tashi sosai, suna so suji me iyaabu take nufi da wannan habaici nata. Malam habuya sharbe hawaye da babbar riga ya ce''muje zaurein fada muku abunda ya faru'' da yake damantsakar gida suka iske su. Suka je zaure sukazazzauna malamhabu ya nisa gami da langabar dakai yace'' idan ka haifa dole a jawo maka, damanance dan kuka shi ke jawa uwarsa zagi. Uwar biyu dahannah su dai sun kagu suji abunda ke faruwayace'' yanzun nan babu dadewa watakila kunhadu da wata bakar katuwar mota a hanyar shigowa garin nan wata fitsararriyar yarinya cetazo ta cimun mutunci a kofar gidan nan har ta taramun mutane. Hannah tace''wacece baba? Cikinrudani da fargaba ta tanbaya. Ya ce'' farko da tazosai ta tsaya ta karemun kallo a wulakance sannantace naji kunya wallahi yasa naji kunya. Dama yarinyar yar talakawa ce yake bata mun lokaciakanta to baba bari in

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});