Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

karatu banda wasa '' kowacce jikinta yayi sanyifuskarsu alamar basu ji dadin wannan batu na class master dinsu ba . Suna son haisam saboda kula dasoyayya da yake nuna musu wasa da dariya akoda yaushe sai wasu dayawa daga cikinsu sukarushe da kuka. Babu kamar rauda, nusaiba dahannah, ai kuma gara rauda da nusaiba akanhannah wani sabon tashin hankali ya rufta mata fiye dana dazu. Haisam zai bar makarantar nan itakuma ina zata dosa ?''.Haisam ma wani tsananin bakin ciki ne yamamaye a zuciyarsa yana tsananin son yan ajinsa.Baya so ya tafi ya barsu yana tausayinsukasancewar yan yara babu kuma wani malami komanyan daliban da zasu zauna suna basushawarwari kamar hannah, wa zai kula da hannah? A bar zancen kudin makaranta da siyayya(provision )ita kanta tana bukatar a kula da ita dakara karfafa mata gwiwa wajen idan ta tafi hutugida ta dawo makaranta. Koda a gida an ce baza tadawo ba tasa kuka har sai an dawo da ita. Ga wasuabubuwa da suka yi mata nauyi a aji ma'ana bata ganewa sai shi haisam da kansa yake nunnunamata har sai ta gane. Allah sarki hannah ya fada azuciyarsa ji yake kamar ya rushe da kuka dantsananin bakin cikin rabuwa da dalibansa. Ammaya daure ya dinga lallashinsu, idan wadannnansuka yi shiru sai wadansu su rushe da kuka. Haisam har ya gaji da lallashi yace su tashi su tafidakunansu sai gobe zasu hadu a wajen assemblyhutu, suka nufi dakunansu kowacce na sharbehawaye. Haisam kuma ya nufi gidansa dake staffqurters yana mai matukar jin ba dadi a ransa. Kowayayi shiru ya daina kuka amma banda hannah. Nusaiba da rauda suka dinga lallashinta amma takidainawa taki cin abinci sai tayi kamar tayi shiru tadaina sai ta tuna ta rushe da kuka. Haka ta yini curtana kuka. Rauda tace waini hannah kukan nan dakike yi kinfi kowa son yaya haisam ne ? Ni fa munfikusa da shi babana abokin babansa ne. Kuma yayana auwal abokinsa ne. Haka kuma yata ywadaya uba daya ramla budurwarsa ce koma nacematarsa ce don har ansa musu raba, sanda mukeamerica yan gidansu a gidanmu suke sauka insunje kuma da muka dawo nan kasar saboda yayahaisam ma aka kawoni makarantar nan tunda yana malami yace da abbana makarantar akwai karatu.To harni na hakura na daina kuka ke ba za kihakura ba kamar kinfi kowa sonsa. Ya ce dai kekanwarsa ce kuma ni a sanina 'yan uwansa duk akano suke na sansu kuma amma ni ban sanki ba.Kuma duk yan uwansa babu masu kama dake ke kamar balaraniya kike ko buzuwa ce ni ban saniba'' nusaiba tace'' haba rauda meye haka in ba yaruwarsa bace zai fada ne ? Hannah ta sake rushewada kuka. Daman abunda rauda take yi mata yaisheta. Tunda aka kawo ta malam haisam yacekanwarsa ce taga rauda tana kishi da ita. Wai ya za ayi ace hannah kanwar yaya haisam ce bayan itakadai ce kanwarsa a makarantar. washe gari da sassafe dalibai suka shirya kayansutsaf na tafiya gida suka saka kayan makaranatar(uniform) suka dunguma babban dakin taro (hall)don yin assembly hutu. Hannah nusaiba sukakinkimo jakunkunan kayansu na sakawa sukakuma rarrataya jakar litattafansu a baya. Akwatinsu kuwa da katifu da bokitai a wani daki ake lufgawaa rufe. Ba.a tafiya dasy gida. A bakin hall din sukaajiye jakunkunan sannan suka shiga cikin hall dindan yin assembly. Kallo daya haisam yayi wahannah yasan tasha kuka kuma tana cikin tashinhankali . Principal ta sanarwa dalibai cewa an basu hutun kwana arba'in da biyu. Don haka ranar dakwana arba'in da biyi ta cika kowacce daliba kadata kara ko kwana daya. Idan ta kara to za.a koratagida. Baza a karbeta ba. Sannan tayi musu nasihohiakan idan suka je gida su dinga taya iyayensu aikibanda yawo a gari gidan kawaye balle kuma masu samari. Mataimakin principal ma ya tofa albarkacinbakinsa. Ya jawa daliban kunne akan su zamamasu da.a da ladabi da biyayya a duk inda suke.Saura malamai ma suka yi musu nasihohi akan suyiamfani da abunda principal ta fada musu damataimakinta. Sai kuma daga karshe malami uku da suka zo bautar kasa suka yiwa dalibanmakaranta sallama akan in sun tafi sun tafi kenanba zasu dawo ba. Malaman yan bautar kasar suneuncle haisa, rose iliya da hassan bawa. Dalibaimasamman ma yara sunji ba dadi saboda sun sabada malaman. Musamman haisam saboda kirkinsa da wasa da dariyarsa yasa kowacce daliba tahi tanasonsa. Musamman daliban da take koyarwa sunamatukar bakin ciki da rabuwa da malaminsuwanda ya kware wajen koyar musu da geography.Nanfa dalibai suka rode da surutu wasu na kukawasu na fadin'' we miss you ! We miss you so much!! Uncle haisam, we miss you more, stay don'tgo please. A haka dai principal da sauran malamaisuka fice suka umarci daliban suma su tafi dukwacce aka zo dauka. Hannah da nusaiba a bakinbarandar hall din wajen jakunkunansu suka zauna.Nusaiba tace'' allah yasa dady na tun jiya yaxo kano daga abuja. Ya kwana a kano yau da safennan ya kamo janyar kazaure. Kar ace yau zai tahodaga abuja gaskiya sai yamma zai karaso kazaurewallahi murna nake yi kaman za'a sani a aljannah.Dama ace ina rufe idona na ganni a gida'' hannahtayi murmushin karfin hali don babu walwala a zuciyarta dama ace duk wanda son zuwa gida yadaga hannu sai tafi kowa daga hannu dan ta zaunaa makaranta. Nusaiba ta kallo hannah wacce tunsafe bata murna. Musamman ma yanzu da taji ancehutun kwana arba'in da biyu za'ayi sai ranta yasake baci. Ga kuma babban tashin hankali haisam zai tafi. Nusaiba ta kula hannah ko irin dan dokintafiya gida bata yi. Sai surutu take ita kadai hannahbata sauraron ta sai wani tunani take daban.Nusaiba ta dan zungureta da gefen hanni tace''waike hannah meke damunki ko murna bakya yigida fa yau zamu'' hannah ta nisa sannan ta sake yin murmushin karfin hali tace'' me kika gani ?Wallahi nima ina murna dama na bude ido in gannia gida yanzu'' nusaiba tahi dadi da wannangudunmawar hira da hannah ta fara bata tace'' nikuma ina zuwa gida fruit salad zansa ayi min in ciwallahi shi nake marmari ''Nusaiba ta zabura tace'' meye makani,kwatantamin yadda yake nima idan naje gida incea soyamin'' hannah tace'' ai shi makani dafa shi akeyi. Ba kisan gwaza ba ? Nusaiba tace'' gwaza!gwaza!! Menene ma gwaza ? Oh cocoam zaki cemun. Kai allah ya sawake inci gwaza sai kace wata yar kauye ? Hannah tayi shiru don tasan ita yarkauye ce kuma acan su gwaza abun marmari ne.Nusaiba tace. A ina kuke samun gwaza ni banaganin ta ma ko a kasuwan abuja'' hannah tace mumuna samu'' uncle haisam ne ya tunkaro wajen dasuke zaune , su duka suka mimmike tsaye don girmamawa gami da cewa , good morning sir'' yace'' morning hannah, good morning nusaiba. Yauyammata sai gida naga nusaiba sai murna kike yiko ? Nusaiba tace yaya haisam murna yau nakelamar za'a sakani a aljanna. Haisam yayi dariya yace '' hannah kefa, kema kina murna kaman za a sakaki a aljannah ? Hannah tayi murmushin karfinhali tace'' eh'' ina murna nima, shigowar wata motakirar end of discussion ce ta katse hirar da suketazo ta tsaya. Kafin mutumin da yake ciki ya fitodaga motar nusaiba idris ta daka tsalle mike dagudu ta nufi wajen motar nan tana cewa babama oyoyo. Ya taho shima da saurinsa ya rungume ta suduka murna suke

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});