Chapter 6
Chapter 6
bana kadeshi shiyasa ya cukuykuye, ya sake lekaakwatin sai ya hango wani dan dogon karfe mai huda huda ajikinsa, jikinsakamar farar azurfa yana kyalli ya ce "Hannewannan fa, karfenmenene? Dauko muga. Hanne ta yi murmushi tadauko karfen ta mika masa ya karba ya jujjuya bai san ko meyeba ya ce"Wannan kuma na maye. Hanne ta ce "Idan najekiwo nakeyiwa dabbobi busa dashi, abun busa ne. Haisam yace abun busa kuma? Hanne ta ce "Eh kawo ka gani. Ta karbikarfen tamayar da akwatin ta rufe ta koma kan akwatinta tazauna takaikaice ta fara busawa Haisam wannan karfen kaikace Sarkin busar Sarki ne yake yi, karin busar mai dadi daalama daiwaka ce, Haisam ya buda kunnuwa yana sauraroya baza idoyana kallon yadda take yi.Can ta kyalkyale da dariya ta ce "Haka nake yi.Haisam yayimurmushi ya gyara zama ya ce "To ni abunda bangane ba,kamar yaya sai kinje kiwo kike yi? Daman a wajenkiwo ake yin busa? Waye ya koya miki kuma? Nan da nanHanne tacanja daga yanayin farin cikin da fara'a da sakinjikin da takejikinta yayi sanyi ranta ya baci. Haisam ya ce "Yakika canja nan da nan daga tambayarki? Hanne ta rushe dakuka ta kifakai da gwiwa, Haisam yayi matukar mamaki daganin wannanhali da Hanne ta fada yanzu- yanzun nan ya ce"Yaya kina dariya ki koma kuka, Hanne dago kanki. Ta dagoya ce "Gogehawayenki. Ta goge. Ya ce "Fada min meye nakukan? Hanneta ce "Wani abu na tuna shine ya sani kuka. Haisamya ce "Meye abun da kika tuna? Hanne ta sa hannu tasake gogehawayen da ke idonta ta dauko abun busar dakekan cinyartata rike a hannunta tana jujjuya shi.Tace kullum dasafe nake fita kiwo da raguna da akuyoyin iya abucan dawa. Bana dawowa sai da yamma musammanrabar asabar da lahadi. To awajan kiwo ne nakehaduwa da wani tsoho mai suna malam saleh. Wani lokaci sai yazo ya wuce ni ina kuka idan yunwa tadameni don yini nake anan kuma ba.a kawominabinci. Har dai rannan ya zo ya sameni a gingininuwa ina kuka. Yayi ta tambayata dakyar dai nagaya masa yunwa nake ji. yace '' ba.a kawo minabinci daga gida ?nace ba.a kawomun kuma bana zuwa dashi. Ya ce '' ina babata? Nace ta rasu'' shineya ce min kullum zai rinka bani abinci ina ci dakekullum da rana daga gidansa ake kawo masaabinci nan wajen kiwon rigarsu tana nan kusakusa da garinmu , shine kullum muke haduwadashi yana waka harya koyamin nima nakoya. Sai ya ce ya barmin abun busar tunda na iya, ko bayanransa dansa zai ringa kawo shanunsa datumakinsa kiwo na dinga yi musu busa. Bayan nannaga kwana biyu naya zuwa kiwo bana ganinshanunsa kuma. Hankalina ya tashi naji duk banajin dadin kiwon ni kadai babu wanda muke zama muyi hira muyi busa muyi waka tare. Sai da akadade naga shanunsa da tumakansa an kawosuwajen kiwo amma ba malam saleh bane wanisaurayi ne. Naji gabana yana ta faduwa ko lafiyaina malam saleh yake? Naje na tambayi yaron sai yace shi dansa ne kuma babansa malam saleh satinsa biyu da rasuwa shine a duk sanda naje kiwo nagadabbobinsa sai suyi ta bani tausayi ina kuka''hanne ta goge hawayen da yake zubo mata haisamyayi ajiyar zuciya. Zuciyarsa cike da tausayin hanneya ce a ransa'' hanne yarinya karama tasan bacinrai, tasan tashin hankali ta rasa kowa da zai tarairayeta wanda zata gani taji dadi baya gamahaifinta. Allah sarki , na yiwa allah alkawaribazan kyale yarinyarnan taci gaba d tagaiyara ba''ya juyo ya kalli hanne wacce har yanzu take rike daabun busarta a hannunta tana jujjuyawa.Yacekawo abun busar shima na ajiye miki, idan ba haka shima malamai zasu kwace'' hanne tayi murmushita mika masa ya karba ya jujjuya ya bude zip dinjakarsa inda ya saka tsakiyoyin nan nata ya saka yamayar da zip din ya zuge ya ce'' yanzu abunda za.ayi kije kicin gashi can ya nuna mata da hannunsaya ce kice uwar biyu, tazo inji malam haisam kinji ku taho tare'' hanne ta mike cikin ladabi tana maiamsawa cikin ladabi ta nufi inda ya nuna mata tanatafe tana kara tsuke damarar data ci da gyale akugunta.Haisam ya bita da kallo har ta kure yayimurmushi ya girgiza kai'' bayan tafiyarta da kamarminti biyar sai ga hanne da uwar biyu sun taho tare bayan uwar biyu ta gaishe da haisam durkuso harkasa duk da ta haifeshi tama yi jika dashi amma aidurkusama wada ba gajiyawa bace irin abunalherin da haisam yake yi musu ita da abokanaikinta na kicin sune masu dafawa yan makarantaabinci. Duk ranar da yake duty idan yazo kicin duk sai ya bisu da kudi dukkaninsu don haka allahallah suke malam haisam yazo kicin bayan sungaisa ya ce'' uwar biyu wata alfarma nake si kiyimin idan baza ki takura ba '' uwar biyu ta sakegyara gwiwoyinta da ta durkusa tace'' haba malamhaisam menene ni kuwa a duniya zaka nema ina dashi na takura ai babu sai dai ma nayi murna yauharka nemi wani abu a wajena , mai yi maka kansada kafarsa. Kana yi mana alheri allah ne zai sakamaka da alherinsa'' haisam yace '' amin na gode .Ba wani abu bane daman wannan yarinyar da kikagani kanwatace amma daga kauyenmu taci makarantar nan babanta ya kawota dazu. Tokasancewar acan basu iya karatuba basu san ancea diko kayan makaranta ba da sauran saye saye .To shine naga dasu koma gida gashi garinbakusaba shine nace zan baki ita ki tafi da itagidanki kamar kwana biyu haka kafin na diko mata kayan makaranta( uniform) da sauransiyayya sai tazo ta koma hostel. Uwar biyu tace''allah sarki malam haisam ai wannan ba wani aikibane babu komai ai sai mu tafi daman na gamadaure ledata tafiya kawai zamu yi'' haisam ya ce'' tona gode '' yasa hannu a aljihu ya dauko kudi ba tare daya kirda ba ya mikawa uwar biyu yace '' toga wannan don ku samu ku saisayi dan abundababu'' uwar biyu ta karba zuciyarta cike da farinciki da mamaki irin wannan yawan kudin da koalbashinta na wata baikai wannan haka ba, gashidaman wata yayi nisa. Tayi ta godiya da da shi albarka har ya gaji da amsawa. Ya kalli hanne yace'' hanne inaga yau duk a wunin nan baki ci abinciba ko? Hanne ta sunkuyar da kai tayi murmushitace'' na karya da safe'' uwar biyu tayi caraf tacea.a.a tin karin kumallon safe kuna ta tafiya ko?Haisam yace nisa , don haka uwar niyu kuje ki bata abinci taci ta koshi.Haisam yace ki siya mata tsiren nan na bakintasha dan alla '' uwar biyu tace to in allah ya yardayanzu kuwa'' haisam yaci gaba da cewa'' sannan kisai sabulun wanka da mai me kamshi ki bata tayiwanka , karki barta ta sharba yanxu duk fuskartata kwabe da kwalli. Hanne ki daina yin wannan dige digen kinji ? Hanne tace to uwar biyu tayidariya tace'' ai da haka suma zasu zamo 'yan matasu koyi yadda ake kwalliya me kyau irin na yanboko ko hanne? Haisam yace'' ina ganin har kantasai an wanke , anyi mata sabon kitso, ko kinyi kitsomuga kan? Hanne ta zame dankwalinta ta durkuso da kanta ta nuna musu wayyo allah kowa ya kallikan hanne zai san bata da uwa a gidan ko wanitsayayyen mafadi ko kuma kazamar uwa allah yabata gashi ne irin kanannadaddennan na fulani kobuzaye ko larabawa mai laushi mai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31