Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 22

Chapter 22

Gangar Jikinsa Na Aura Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yasan yau za'a yi tane ta kawai donshi babu mai rabashi da makarantar nan. Ya karaso da sauriya nufi ofishin principal tun daga kan baranda yakejiyo kukan hannah ya shiga a fusace gami fa yayelabulen kofar bazar ya tarar da hanna a durkushega jakar kayanta nan a gabanta, principal tanarubuta mata takardar kora {dismisal letter} takardar kora daga makarantar kwata kwata ga yaya habiba zaune yana cewa''ai idan yaga tabar makarantarzai bari shima dole ''a gigice haisam ya karaso yakalli yaya habib ya kalli principal yaga da gaskesuke sun sha kunu.Haisam ya wawuro wata adda a bayan kyaurenofishin irinta yankan ciyawa ya dora akan kirjinyaya habib. Wanda mamaki ya hana yaya habib yinmotsi daga kan kujerar da yake zaine, haisamyace''hakika zan iya kashe duk wanda yake dakokarin jefa hannah a cikin tashin hankali da wahala a rayuwarta. Ban dauka zan sameka kanadaya daga cikin irin wadannan mutane ba, ammaduk da haka ba zan karya alkawarina ba. Kaiyayana ne uwa daya uba daya da irin soyayyar damahaifanmu suke yi mana, ka duba kuma irinsoyayyar da muke yiwa junanmu don haka bana son na zama ajalinka . Ba kuma zan bar makarantarnan ba har sai na cika burina dana kudira akanhannah''hannun haisam rike da adda akan kirjinyaya habib karkarwa duk jikinsa yake hawaye neyake shatatowa daga idonsa haisam gaba ki dayansa ya canja, yaya habib ya tabbata haisam ya kai kololuwar bacin rai don shi yasan yadda bacin ranhaisam yake abun babu kyau. Da wuya dai yayifushi abu da yawa bai cika bacin rai ba sai an kaishi bango idan ya hau to kowa sai ya tsorata kumamai lallashinsa ya sauko sai an sha wuya kumaidan ransa ya baci zai iya yin duk abunda ya ce zaiyi. Hanna ta kwala kara tace'' yaya haisam kadaka kashe dan uwanka a kaina na yarda ni zan barmakarantar dan allah yaya haisam, dan allah kayihakuri''wani zazzafan hawaye ne yaci gaba dazubowa daga idanuwan haisam a tsaye yake kawaiya kurawa yaya habib ido rike da wannan adda a wuyan yaya habib. Principal kuwa tuni ta dagatsalle tayi lungu tana jiran taga yadda haisam zaiyida yaa habib sannan ya dawo kanta. A fusace yayahabib ya yinkura zai tashi haisam yasa hannu yaturashi kan kujerar ya koma ya zauna. Haisam ya ce''bani takardar hannunka''yaya habib yace son hannah kake? Ya sake fada cikin tsawa yace''tambayarka nake sonta kake shi yasa ka kasabarin makarantar? Haisam yace''burina ingahannah tana cikin farin ciki a rayuwarta kuma inkwatar mata 'yancinta kamar kowacce yarinyatunda ita ba baiwa bace gatan hannah allah, sai kuma ni a duk duniyar nan. cikin sanyin jiki habib ya mikawa haisam takardar asanyaye sannan haisam ya dauke addar daga kankirjinsa ya wurga bayan kyaure ya dauki jakarkayan hannah ya ja hannunta suka fice. Habib daprincipal suka bisu da kallo suna fita principal tayiajiyar zuciya don da kyar numfashinta yake fita saboda tsabar ta tsorata ta tabbatar yadda haisamya harzuka yau zai iya kashe yayansa balle kymaita. Bayan wani lokaci mai tsawo suna zaune shirubabu wanda ya iya magana suna tunani kawai,yaya habib ya nisa ya kalli principal ya ce'' madamyaron nan da gaske yake don jaka kada a kaishi bango ya zo ya kashe wani a dinga kai kawo akotu, ina ganin a kyalesu kawai don allah a dainadukan yarinyar balle har ya harzuka yayi kisadomin haisam zai iya aikata hakan tunda ya furtayana da zuciya sosai amma fa sai an kaishi bangodan bai taba zai yi kisa ba sai yau akan yarinyar nan, zanje in sanarwa da mahaifanmu'' ya mike yafita, principal kuwa da kyar take iya maganasaboda tsoron haisa tana ganin zai iya binta gidacikin dare ya kasheta. Daga karshe ta yankewakanta shawara gara taje ta sami haisam ta bashihakuri suyi sulhu . Ta kuma yi masa alkawarin baza ta sake yadda kowa ya takurawa hannah ba. Hakakuwa tayi ta sami haisam har gida cikin lumanasuka zauna ta bashi hakuri suka yi sulhu. Tana fitahaisam ya tuntsire da dariya dadi ya lullubeshoi yace HAISAM HANNAH!! Kwanci tashi su hannah sun shiga aji shida {s.s.3}sune manya . Cikin ikon allah da hukuncin allahhannah tazo tafi kusan duk yan makarantar kokarisaboda tun tana zuwa ta takwas ta fara zuwa tabiyar daga nan ta kwacewa pamella matin positiondinta ya zamana rauda ta daya. Nusaiba ta biyu ita take zuwa ta uku. Tafi tafiya saiga hannah tazo tadaya a ajinsu wani lokaci rauda ta kwace kayantaidan nusaiba mata hargistso sai ta kwance itama,haka dai ake ra fafatawa amma yanzu da sukashiga aji shida har malamai ma fada suke hannahtafi su rauda kokartawa don sau da yawa ko tambaya aka yi a aji hannah ce take amsawa sautari. Sannan a class work da assignment tafi kowa ci. An basu mukamai daban daban. Hannahabubakar imam itace shugabar dalibai {head girl}nusaiba mataimakiyarta. Rauda kuwa dake tayikaurin suna a wajen iya rawa da wasanni {games} harma ake mata lakabi da janet jacson sai aka batasocial prefrct da games prefect mukami biyu akahada mata kuma tayi murna da wannan mukaminnata. Duk ranar social night har koyawa yara rawardisco kala kala take yi. Hannah ma ta dace damukamin saboda ana son head girl ta zama mai kokari, wacce ta iya turanci sosai, mai gaskiya,ladabi da biyayya, mai kamun kanta ba ballagazaba, mai aji , da tausayi da kuma adalci to dukwadannan hannah ta hada sun don haka nema daaka tace aka zabeta. Domin a yanzu hannah kohausa bata cika yiba turanci ya kama bakinta sosai haisam har mamakinta yake idan yaji tana zubaturanci. Tana da jan aji hannah ba kasafai ta fiyeshiga cikin yan mate dinta ba suna hayaniya. Gatada tausayi musamman ga yara 'yan kananan aji.Babu ruwanta da cin zali kyma bata yardakawayenta suci zalin yara a gabanta. Tunda itace shugabar dalibai tana da ikon hana sauran prefect . wannan halaye na hannah ya sake fito mata dakyakykyawar surarta hannah ta sake gogewaabun har musaltuwa ta yi kyau kai kace ba yarafrica bace . Yaya haisam yasan irin mayukan dakayan sawar da suka dace da jikin hannah.Haisam yasan irin mayukan da kayan sawar dasuka dace da jikin hnnah . Tsadaddun riga dawando da sket kala kala yaya haisam yake hadawahannah sai dai kawai idan ta dawo hutu ta tarar yaaje mata a gidan uwar biyu, daman tun ba yaubabaya ga mahaifinta babu wani da take ganin girmansa a duniya irin haisam. Amma da yakehaisam mai wasa da dariya ne da dalibai suna wasada dariyarsu a aji kamar yadda ya saba yi musu tuna aji daya. A garin su hannah kuwa hannah hargixo take yi musu. Gani suke kawai baturiya tazotace itace hannah, duk ranar da hannah zata dawo gida hutu samari har tsayawa suke a hanyar dazata wuce suna kallonta mata kuma ta katangasuke lekowa. Ana cewa hannah ce fa yar malamhabu a garin turawa take karatu. Hannah sai tayimurmushi kawai ta wuce. A gidan su kuwa iya abuda yayanta daina magana suka yiwa hannah sunga ci gaba na hannah daga allah yake babu irin asirinda basu yi mata ba dan a korota daga makarantarko kuma ma ta haukace amma baici ba. Hannahtana dawowa da duk kayayyakin amfani wadandazata yi amfani dashi har hutu ya kare, ko ta bawasu iya abu da yayanta sai suce basa so. Sai tayi hutunta kakaf ta bar gidan iya abu

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});