Chapter 9
Chapter 9
"Wanke fuskarki ki yi kwalliyarki matata, ai na san babu wanda ya isa ya qwace minke daga gare ni.” “Ina son ka mijina...” Ta fada cikin salon jan hankali dan tabbatar da saqonta ya isa gare shi. Sai da ya dau tsawon minti daya yana maida numfashi sannan ya ce “Ni ma ina tsananin son ki matata.” Da haka suka yi sallama da shi ta gyara fuskarta cikin sauri don ta san Mummy tana can falo tana jiran fitowarta. Tun suna mota ba su isa gidan ba Ardo ya kira Mummy yana tambayarta sun iso ne? Sanar da shi ta yi ga su nan a hanya sai ya ba ta umarnin idan sun isa ta tura Aisha dakin da yake ganawa da baki na waje. Don haka suna isa kai tsaye can falon ta nufa ba tare da ta shiga cikin gidan ba. Takalman da ta gani a qofar falon shi ya tabbatar mata da baqi a ciki, don haka ta qara gyara zaman mayafin kanta da ya yi matuqar dacewa da shaddar jikinta, ta yi sallama gami da dakatawa a qofar tana jiran a amsa. Sannan a ba ta umarnin shiga cikin falon. Gaba xayansu suka amsa, sannan ta ji muryar Arxo yana fadin, “Bismillah shigo daga ciki.” Kanta a qasa ta kutsa cikin falon, sannan ta nemi guri can nesa da su ta zauna. Gwiwoyinta a qasa ta gaida Ardo sannan ta maida fuska kan wadanda ta gani a cikin falon ta fara gaishe su. Idanunta cikin na mahaifan Yasmin, jifan ta sukai da wani mugun kallo. Sam sun kasa amsa gaisuwar da ta yi musu, ita kuma tun daga gaisuwa daya ba ta qara ba, illa musayar kallo da suke yi a tsakaninsu. Yasmin a fili take watsa wa Aisha harara, su kuma iyayenta suna jifan ta da kallon tsana a fakaice. Ba ta rama martanin kallon da Yasmin ko iyayenta suke mata ba don ta san idanun Ardo suna ganin duk abinda ya ke faruwa. “Gyara zamanki da kyau Aishatu” Ardo ya fadi hakan idanunshi suna kanta. ta zauna da kyau sannan ta saukar da qwayoyin idanunta zuwa qasa tana sauraron Ardo. “Ahmadu ina tunanin wannan ita ce yarinyar da kuke qorafin kun tarar da ita a gidan Modibbo?” Ardo ya jefa wannan tambayar ga mahaifin Yasmin. “Qwarai ita ce Ardo, don ba zan manta da fuskarta da irin cin mutuncin da ta yi min ni da iyalina ba.” Mahaifin Yasmin ya amsa wa mahaifinshi cikin muryar dake bayyana bacin ranshi da irin abinda ya shiga tsakanin Aisha da su. “Ai kuwa ya zama dole ka manta da wani batanci da ya tava shiga tsakaninka da ita Ahmadu, domin wannan yarinyar da kake gani ‘ya ce ga Aishatu qanwarka, kuma wannan taro da ka zo kai da iyalinka ku ka tarar za a yi ba na komai ba ne sai na gabatar da ita a matsayin daya daga cikin jikokin wannan zuri’a tamu. Yadda Yasmin take a gurina haka Aishatu take a gurina. Don haka daga yau ka fara yi mata kallon ‘yarka kamar yadda kake yi wa Yasmin kallon diyarka ta cikinka.” “Amma Ardo...”Ardo sai kuma ya yi shiru ya rasa abin cewa domin dai ya san Ardon idan ya ce “Eh” To e din yake nufi har abada. “Umarnina ne bai samu kar6uwa a gurinka ba ko kuma jayayya za ka yi da ni Ahmadu?” “Ba haka ba ne Ardo, umarninka abin bi ne a gare mu ni da iyalina, domin duk a qarqarshin ikonka muke. Allah ya huci zuciyarka.” Da saurinshi ya yi togaciya da fadin haka. Sannan ya juyo gare ta yana murmushin da kallo daya ta yi masa ta san bai kai ciki ba ya ce “Muna miki maraba da zamo wa daya daga cikin zuri’armu. Da fatan za ki manta da abin da ya taba shiga tsakaninmu na batanci? kamar yadda muka manta har abada ni da iyalina” Murmushi ne ya wadaci fuskarta duk da tana tabbacin maganar da ya yi iya le66anshi ta tsaya, sanin da ta yi ba shi da wuta ba shi da aljanna, bai isa ya cutar da ita ba sai abinda Allah ya qaddara zai faru a kanta “Na gode. Ina fatan za ku manta da mayar muku da maganar da na yi a haduwarmu ta farko?” “Kar ki damu Aishatu, duk dan Adam ajizi ne, kuma rashin sani shi ya sa duk muka aikata wannan kuskure. In Allah ya yarda hakan ba zai sake faruwa a tsakaninmu ba.” Mummy ce ta fadi hakan tana murmushi. “Yasmin ba ki gaisa da ‘yar’uwarki ba, ko har yanzu kina riqe da 6atancin da ya ta6a shiga tsakaninku a zuciyarki ne?” Ardo ne yai wannan tambayar ga Yasmin bayan ya lura kowa ya maida magana ita ce kawai ta yi shiru, kuma har a wannan lokacin ba ta saki fuskarta ba.Kafin ta furta komai sai da ta taso daga inda take zaune ta dawo kusa da Aisha, sa’annan ta miqa mata hannu suka yi sallama a tsakaninsu (musabiha), irin kallon da take wa Aisha mai hade da murmushi kallo ne mai isar da ssalon “za ki gani in dai ni ce”. Aisha ba ta yi qasa a gwiwa ba gurin mai da mata da martanin kallon mai isar da saqon “In ga alkhairi, ta Allah ba taki ba.” Ba tare da ta matsa daga kusa da Aisha ba ta dubi Ardo ta ce “Ba haka ba ne Ardo, wa ce ni in qi bin umarnin tsohon mijina matuqar ina son aljanna? Kawai dai mamaki ne ya kama ni da wata matsananciyar kunya, ashe akwai dangantaka mai qarfi a tsakaninmu da Aiaha, amma rashin sani ya sa duk mun yi wa juna mummunar fahimta. In Allah ya yarda wani abu makamancin wanda ya shiga tsakaninmu a baya ba zai sake faruwa a gaba ba. Zan riqe ta qanwa ta jini kamar yadda nake riqe da sauran qannena na wannan zuri’ar.” Gaba dayansu sunji dad'in abinda ta fad'a, ita ma Aisha fuskarta yalwace da fara’a duk da ta fahimci inda maganganun nata suka dosa. “Alhamdulillahi! Dama haka ake son duk musulmi na qwarai ya kasance mai yafiya ga dan’uwanshi musulmi. Sai Allah ya yafe mana kura-kuran da muka aikata tsakaninmu da shi. Yasmin ki jagoranci ‘yar’uwarki Aisha zuwa cikin gida inda za a gudanar da taro kamar yadda muka saba. Ahmadu kana iya shiga cikin gida kai da iyalinka kafin sauran ‘yan’uwa su gama had'uwa.” Har qasa dukkansu suka duqa suka yi godiya ga Ardon, sannan suka yi masa sallama suka nufi cikin gidan kamar yadda ya ba su umarni. Suna zaune cikin dakin taron, a lokacin jama’a ba su gama haduwa ba, amma mafi yawancin dangin sun hallara, idanu sun yi yawa a kan Aisha, don haka ta takure a kusa da Mummynta, hannunta na dama yana cikin na ta, tana matsawa a hankali. Mummyn Yasmin ce ta kasa haquri sai da ta jefa wa Mummyn Aisha magana cikin shagu6e, “Aishatu ashe kin ta6a haihuwa ba mu da labari?” Da yake Mummy mace ce mai gaskiya da rashin barin ko ta kwana take ta ba ta amsa kai tsaye ta ce, “Qwarai kuwa ga zahiri! tunda kin gan ni da ‘ya?” Dariya ta yi cikin kunya da son basarwa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31