Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 4

Chapter 4

A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ne dare da rana, amma cikin hikima suke gudanar da aikin nasu ba tare da ko ‘yan unguwar sun sani ba. Har izuwa yau da kwanaki uku kenan da fara aikin nasu bai samu wani qwaqqwaran bayani ba dangane da masu shiga gurin suna aikata masha’a. Hatta qananan ‘yan iska dake shiga cikin kangon suyi shaye shaye sun dauke qafa kamar sun San me ake yi Sarqar dai fara ce, kuma ba ta da tsawo sosai, da alamun idan aka sanya ta a wuya za ta dan kama wuya, amma ba sosai ba. Tana dauke da tambarin “A” daga qasa, kallon sarqar yake a zuciyarshi yake tunanin kamar ya tava ganin wani sanye da sarqar. ‘Amma a ina? shi ne abinda sam zuciyarshi ya gagara tunawa. Tun yana ganin kamar shirmen tunani yake a kan sarqar har zuciyarshi ta yi nasarar rinjayar da shi tabbas ya ta6a ganin wani sanye da sarqar ko kuma irinta a wani guri. Inda dai ya tava ganin wani sanye da sarqar ko kuma irinta ne ya kasa tunawa. Kansa ne ya kulle da zazzafen tunani, don haka ya tattara komai ya ajiye guri daya ya gyara kwanciya a kan gadon lokacin da agogo ya nuna qarfe uku da kwata na dare, Idanunshi ne suka fada kan lambar wayar Abba yayan Yasmin lokacin da yake qoqarin neman lambar Abdulqadir daya daga cikin masu gadin kangon da aka yi wa Sadiya fyade. Sama da kwanaki bakwai kenan bai sa Abba a idanunshi ba, kuma bai san a wane hali yake ciki ba. *** “Daddy ka yi waya da Ardo a kan lamarin Yaya Abdul kuwa?” Yasmin ta tambayi mahaifinta lokacin da suke zaune su uku a dinning table suna karya kumallon safe. “Muna waya da Ardo Yasmin, amma ban fada mishi komai ba daga abinda ya faru. Maganar Abdul babba ce, tana buqatar nutsuwa da haduwa fuska da fuska gurin tattauna ta da neman hanyar magance matsalar. Don haka na yanke shawarar qarshen satin nan za mu tafi Yola gaba daya don sanar da Ardo abinda yake faruwa.” “Hakan ya yi daidai Alhaji, domin na san shi kansa Ardo ba zai goyi bayan neman karuwan da Abdul ya tsunduma kanshi ba, duk da cewa Abdil shalele ne a gurinshi.” Mummy ta fadi hakan tana yatsina fuska bayan zuciyarta ya tuno mata karon battar da suka yi da ‘yar iskar karuwar da Abdul din ya ajiye gidanshi. “Amma Daddy haka za ka bar wannan ‘yar iskar karuwar ta ci bulus duk da irin rashin kunyar da ta yi muku kai da Mummy?” Yasmin ta tambayi mahaifinta tana bata fuska da nuna takaicin abinda ya faru da iyayen nata. Wani abin mamaki shine, sam Yasmin taqi sanarwa iyayenta cewa yarinyar da suka gani a gidan Abdul ita ce sanadin karayar hannunta. Ko Hidayah da take qawa a gare ta ba ta sanar da ita hakan ba. Ba don komai ta boye ba sai don gudun asirinta ya tonu. Daga ganin idanun Aisha yarinya ce da ba ta wuce shekaru sha bakwai ba. Ita kuma Yasmin tana cikin shekara ta ashirin da biyu. "Karki damu Yasmin. Tun washe garin ranar da abin ya faru na tura gidan Abdul din a yi maganinta. Amma abinda suka sanar da ni shine Abdul ya bar gidan da yarinyar a safiyar wannan rana. Duk ranar da Allah ya sake hada fuskata da ta wannan fitsararriyar yarinyar tabbas za ta kwashi kashinta a hannu.” “Ta ba ni mamaki yarinyar, ba a ta6a ci min mutunci irin yadda yarinyar ta yi min ba, wai har ni za ta kira ‘yar bariki? Har duniya ta nade ba zan manta da wannan yarinyar a raina ba.” Mummy ta fadi haka zuciyarta na kuna. “Ki kwantar da hankalinki Mummy, shi kanshi Yaya Abdul ya san Daddy ba zai qyale wannan ‘yar iskar karuwar ta ci mana mutunci a banza ba. Shi ya sa ya yi saurin sallamarta daga gidan yana tsoron abinda zai je ya zo. Amma idan kura na yawo kare na yawo tabbas watarana za a hadu” ‘Qwarai kuwa Yasmin.” Daddy ya amsa cike da tabbaci da gamsuwa. Da fito mai qarfi ya shiga cikin falon don haka duk suka maida hankalinsu kanshi. Inda sabo ya ci ace sun saba da yanda zai shiga falon saidai ya yi fito don a san shigarshi a maimakon sallam irinta addinin musulunci. Tun suna mishi magana a kan hakan cikin rarrashi da kwantar da hankar da kai har sun haqura sun zuba mishi idanu. Kara shiga cikin nutsuwarta ta yi ta maida kai kan dankalin da take ci ko kallonshi bata sake yi ba don gudun yin laifi a gareshi. “Abba ka tashi? Barka da safiya...” Daddy ne ya fara mishi wannan maganar ya na kallon Abban daya nufi kan kujerun falon ya zauna ba tare da ya ce musu komai ba. “Yauwa! barka dai Daddy.” Ya amsa gaisuwar uban ya na watsa jajayen idanunshhi a kan Yasmin. “Ke don Ubanki baki iya gaisuwa ba ne?” Ya jefa mata tambayar cikin tsawa da daga murya. A tsorace ta taso daga inda take zaune ta na karyawa ta tsuguna a qasa can nesa da shi ta ce, “Yaya Abba ina kwana? Ka tashi lafiya?” Sai da ya gama watsa mata harara ya na kallonta ya yi sama da kansa ya na hura hanci ya ce, “Saida na roqi gaisuwar? ‘Yar iska mara mutunci. za ki tashi daga nan ko sai na yi ball dake? Shegiya mai suffar munafukai" “Haba Abba, yanzu daga shigowarka har zaka fara takura mata? Ca nake kai da ka shigo falon sai da mahaifinku ya gaishe ka?” Mummy ce ta fadi hakan don kore zagin da ya fara ma Yasmin, tasan kadan daga aikinshi ne yayi qwallo da itan kamar yadda ya fada. “Wai ke Mummy ina ruwanki da harkata? Qanwata ce kuma ina da ikon hukunta ta idan ta yi laifi. Amma na lura ke kullum burinki wannan yarinyar ta raina ni.” “Ni ban ce ta raina ka ba, amma dai ka ringa yi mata a hankali, tunda ko mu da muka haife ka ba ma matsa maka.”my “Ni fa na lura a gidan nan kun tsane ni, a kullum ni ne wanda ba ni da mutunci kuma ba na aikata abin kirki, wannan ‘yar iskar yarinyar ta bi ta kankane komai na gidan nan! Komai na yi ban iya ba, wallahi matuqar kuka ci gaba da takura min zan bar gidan nan, don babu dan iskan da ya isa ya matsa wa rayuwata. Na wuce shekaru goma sha takwas! ina da damar da zan yi abinda na ga dama da rayuwata” Yana tsaye a tsakiyar falon yake zazzage ruwan masifa iya son ranshi. Yasmin dai sadaf-sadaf ta fice daga falon, domin ta san qarshen abin a kan ta zai qare. Daddy ne ya tashi tsam daga inda yake zaune ya koma kusa da Abban ya dafa kafadarsa yana bubbugawa yana rarrashin sa kamar qaramin yaro. “Calm down my lovely Son! Ni da Mummynka ba wai mun tsane ka ba ne, a kullum babban burinmu shi ne ku zamo yara masu tarbiyya kai da ‘yar uwarka. Ka daina tunanin za ka bar iyayenka don wannan ba abu ba ne mai kyau! Tabbas kana da daman

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});