Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kin yi barci ko? Yi haquri na tashe ki daga barci.” “Me kake yi har yanzu ba ka yi barci ba mijina?” “Ina tare da Ardo ne, kasa haquri na yi da rashin jin tattausar muryarki a daren nan. Shi ya sa na kira don in ce miki ina son ki” “A gaban Ardon kake wannan maganar?” Dariya yayi qasa-qasa, har yanzu ba ta ji jarumtaka kamar yadda yake da a muryarshi ba, da alamun har yanzu a cikin damuwa ya ke. “Ardo zai hana ni magana da iyalina ne?” “Mijina kamar akwai abinda kake 6oye min ko?” Ajiyar zuciya ya sauke kamar ba zai amsa tambayar ta ba, sai can kuma ya ce “Me ya sa kika fadi hakan matata?” “Kawai dai a jikina ne na ji hakan. Kuma ko don irin soyayyar da nake maka ai ya cancani in fahimci idan kana cikin damuwa ko kana cikin farin ciki. Sai dai kuma idan kai a gurinka ban kai matsayin da za ka fada min damuwarka ba..” “Oh my God! Wallahi ba haka ba ne, kin san dai ba na son in tayar miki da hankali ne. damuwata mai sauqi ne idan ke kina cikin farin ciki.” “Ta ya kake tunanin hankalina zai kwanta idan har wanda nake so zai kasance cikin damuwa?” “To yanzu dai ki kwantar da hankalinki ki kwanta ki yi barci, gobe idan na zo sai mu yi maganar.” Ajiyar zuciya ta sauke cikin damuwa, amma ta kasa cewa komai. “Mene ne kuma matata?” Ya tambaya hankalinsa a tashe. “Kana so in daina walwala in shiga cikin damuwa ko Abdul?” Ta tambaye shi muryarta na rawa-rawa, tana shirin fashewa da kuka. “A’a, a’a. Wallahi ba na son damuwarki matata, hasali ma tsoron halin da za ki iya kasancewa a ciki ne ya sa nake 6oye miki damuwata.” “Na yi maka alqawarin ba zan damu ba, yanzu dai ka fada min taka damuwar.” “Mu bari zuwa gobe Aisha don allah, kin ga yanzu ina tare da Ardo ne.” “Allah ya kai mu goben…” Dif cajin wayarta ya dauke gaba daya, kuma abin cajin yana falo, don haka ta haqura ta kwanta tana saqe-saqe a cikin zuciyarta har barci ya dauke ta. Qarfe goma na safiyar washe gari ya iso gidansu cikin rakiyar abokansa guda biyu, don haka ba su samu wani isasshen lokaci na tattaunawa ba. sun yaba qwarai da breakfast din da ta shirya musu, tare da taimakon Zainab. Abinda ya ba ta dariya shi ne yadda Abdul yake ta wani kakkare ta a lokacin da take gaisawa da abokan nashi a falon baqin gidansu. Hatta Zainab sai da ta yi mata tsiya a kan hakan. Dariya ta yi sannan ta kashe surutun bakinta da cewa “Ina laifin mutum don ya yi kishi a kan iyalinshi?” Qarfe hudu na yammacin ranar Juma’a ne aka shirya za a yi “Fulani Day" maza da matan da za su halarci gurin duk shigar kayan fulani za a yi. Haka ma Amarya da Ango. Irin kayan da za su sa kenan. Hudu da kwata sun gama shiryawa tsaf domin babu African time, ita ma Aisha ta yi kyau sosai cikin kayan fulanin tamkar Bafulatana ta gaske. “Wallahi Smally jikinki yana da kyau, duk kayan da kika sanya sai ya amshe ki tamkar da su aka halicce ki.” In ji Zainab kenan kuma da iyakar gaskiyarta take wannan maganar. “Na gode…” Abinda Aisha ta ce kenan ta fice daga dakin zuwa falo domin ta san tunda ta tanka su Maryam ma sai sun tanka. An shirya komai na gurin gudanar da taron Fulani Day cikin tsari, domin hatta mutanen da za su halarci gurin a qididdige suke. Kati ne aka raba ga duk wadanda aka gayyata zuwa gurin. ‘Yansanda ne guda uku a qofar shiga gurin, dole sai ka ba da kati sannan za ka wuce zuwa ciki. Mu’azzam shi ma ya samar musu nasu katin, don haka suna zuwa ciki suka wuce kai tsaye. Isarsu da kusan minti goma Amarya da Ango suka isa gurin cikin shiga ta alfarma ta kayan saqin Fulani, gashin kantin da yake kan Amarya ya sha dutsawu, da kayayyakin kwalliya irin na Fulani. Ta yi kyau babu laifi, domin amarya ce duk muninta kuwa ranar aurenta sai ta yi kyau. Abdul ya yi kyau sosai cikin kayan domin tun farko shi mai kyau ne, duk hangen Aisha ba ta ga namijin da kayan suka kar6e shi irin mijinta Abdul ba. "So hana ganin muni" Inji fareedah Minti goma shabiyar da isowar Amarya da Ango zuwa gurin ana tsaka da gudanar da taron, babban abokin Ango yana ba da tarihin ango cikin harshen turanci, wani kuma yana gefe yana fassara maganganun da harshen fulatanci. Hankalin Aisha ya yi nisa gurin sauraren yadda Abdul yake sha’awar aikin dan sanda tun yana yaro da yadda har burinshi ya cika na kasancewa dan sanda mai gaskiya da amana. An fara gabatar da tarihin da yadda soyayyarshi da Yasmin ta kasance ne ta ji ringing din wayarta, abin mamaki shi ne, Abdul ne yake kiranta, kafin ta dauki wayar sai da ta kalli gurin zaman ango da Amaryarshi. Ba ya nan a mazauninshi sai Yasmin ita kadai tana juya idanu dama da hagu. “Ki sauko ki same ni a gurin motoci, ina jiran ki.” Umarnin da ya ba ta kenan, da yake hall din da ake taron bene ne. Tana sauka qasa ta ja ta tsaya, domin ba ta san ko a gurin wace mota yake tsaye ba. caraf ta ji an cafke hannunta an janye ta zuwa cikin mota. Ba ta tsorata ba domin ta san idan ba Abdul ba babu namijin da ya isa yayi mata haka. “Matata ya kamata ki koma gida yanzu.” Abinda ya fara fada kenan muryarshi a dan fusace. Kallon shi ta yi na wani lokaci don karantar yanayin fuskarshi. Da alamun an 6ata masa rai, domin bai da walwala ko kadan. “Saboda me zan tafi? Bayan yanzu aka fara gudanar da komai?” “Dole za ki tafi yanzu Aisha, domin mafi yawancin samarin gurin idanunsu bai kai kan kowace yarinya ba sai ke. Minti ashirin da biyar zuwanmu gurin mutane shida sun yi min magana a kan in taimaka in shige musu gaba a kan ki. Ban san me zai faru ba idan kika tsaya har aka gama gudanar da komai.” Ya amsa mata yana numfashi sama-sama. “Haba!! sai ka ce ni kadai ce mace a gurin bayan duk ga qawayen Yasmin masu digiri?” “To ke suka gani, kuma a kanki suke magana… kowanne da tsamin bakinshi Abdul na ga tauraruwa a cikin qannenka, don Allah ina kamu daga gare ka babban Yaya…. kunne na ba zai iya sauraren wadannan maganganun ba.” “Da sauqi ai tunda gani ba dauka ba ne. duk maganganun da za su yi sai gani sai hange.” “Ganin ma ba za su yi ba, dole ki tafi gida yanzu.” Cikin masifa ya amsa mata da hakan. “Toh, waye zai kai ni gidan?” Ta tambaye shi tana tura baki, ba don ranta ya so ba. Shiru ya yi na dan lokaci, sannan ya ce “Bari in shiga in turo Mu’azzam ya kai ki gidan” Har ya bud'e qofa yana niyyar ficewa, ta janyo gefen rigarshi don haka ya dawo ya

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});