Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 30

Chapter 30

A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Yana komawa dakin ya ga Aisha tsaye jikin mudubi tana shafa mai, tun kafin ya zauna ta kalle shi da dan fara’ar da ba ta kai ciki ba ta ce, “Mijina kayi haquri, ka je ku ci abincin kada mu shiga haqqinta.” “Babu inda zan je, sai lokacin da naga dama. Ai ke ma matata ce balle ku kawo min wani fi’ili.” Cikin fada ya amsa mata da hakan. “Ni fa ba nufina in 6ata maka rai ba mijina, amma ka ga yau kwananta ne, ba na so mu yi abinda zai jefa ka cikin fushin Allah. Amma idan ka ji haushi ka yi haquri.” “Shi kenan tunda kora ta ki ke yi, kin ga tafiyata ga abincinki can a dining dinki, Allah ya tashe mu lafiya.” Yana gama fadin haka ya kama hanyar ficewa daga falon cikin sanyin jiki. A muryarshi kadai za a gane tsantsar damuwar da yake ciki. Da hanzari ta sha gabanshi ba ta jira komai ba ta rungume shi tana shafa bayanshi alamun rarrashi, Tun yana kau da kai har ya saki jiki ya karvi ragamar. Sai da ta gamsu da ganin yadda ya samu nutsuwa sannan suka yi sallama cikin daxin rai ya fice daga xakinta yana waigenta kamar kada ya tafi. Ba ta tsawaita wa kanta tunanin komai ba ta tsakuri abinci da kazar da ya kawo mata ta sake yin brush, ta bi lafiyar gado bayan ta yi addu’o’in barci. Da yake akwai gajiya a jikinta, ba ta jima da kwanciya ba barci mai nauyi ya yi awon gaba da ita. Qarfe 2 na dare Yana kwance yana barci Yasmin tana rungume a qirjinshi tana barci ya jiyo vibration din wayarshi, saboda yanayin aikinshi komai dare ba ya kashe waya, don ana yawan nemanshi idan wani aiki ya taso. Da mamaki yake kallon sunan mai kiran nashi. Daya ne daga cikin yaran da suke masa C.I.D na kangon da aka tsintsi gawar Sadiya. “Hello… An samu wani bayani ne?” Abinda ya fara tambaya kenan bayan ya danna madannin amsa kiran. “Qwarai kuwa ranka ya dad'e, wata baqar mota ce muka gani an faka daga can nesa da kangon nan, amma koda muka shiga ciki ba mu samu mace ba, sai maza ne a kwance cikin halin suma jikinsu duk ciwuka suna fitar da mugunyar ruwa mai wari.” “Subhanallah! Kun duba da kyau kuwa? Ko dai sun yi shaye-shayensu ne sun bugu?” Ya tambaya yana mamaki. “Babu alamun maye ko kayan maye a tare da su, bisa ga dukkan alamu wata suka sato don su keta mata haddi sai kuma abin ya juya kansu, domin ko a yanzu da suke a halin suma kwance suke haihuwar uwayensu.” Aka amsa masa daga can vangaren. “Aikinku ya yi kyau, ga ni nan zuwa yanzu.” Yana gama faxin haka ya katse wayar. Yasmin da tun fara wayarshi ta farka daga barci ta dago kanta tana kallon shi ta ce “Yaya ina zuwa haka da tsakar daren nan?” Sai da ya shafa gefen kumatunta don kwantar mata da hankali sannan ya amsa da “Yi haquri, kin san yanayin aikin namu. Yanzu zan je in dawo.” “Amma ya ya ai ni ma ina buqatar kulawarka, ko a haka za ka fita ka bar ni cikin wannan halin?” Nauyi ya ji kanshi ya yi masa da jin abinda ta ce. Ya lura sam ba ta jin kunyarshi ko kadan, ba laifi ta yi dauriya kuma ya same ta a cikakkiyar budurwa, amma zaqewarta da nuna zalamarta a fili shi ne abinda yake kulle mishi kai, domin ita da kanta ta ringa taimaka masa har ya samu biyan buqatarsa. “Na san kina buqatar kulawa, amma haquri za ki yi kin san yanayin aikin namu, da yake ma na ga matar tawa jaruma ce, kin cancani kyauta mai tsoka a bisa tsare min kanki da kika yi duk tsawon wannan lokaci.” Murmushi ta yi, sannan ta sumba ce shi a kunci don tsananin jin dadin maganganunsa, sannan ta ce “Kyautata shi ne ka mallaka min kanka da soyayyarka na har abada mijina, idan ka yi min haka ka gama min komai.” Murmushi ya yi don nuna gaskiyar abinda zai fada. “Idan soyayyata ce kin samu Yasmin, kar ki ji komai.” Ya na gama faxin haka ya yi mata sallama a gurguje ya fice. Ganin motar Abba ne motar da samarin suka yi amfani da ita bai ba shi mamaki ba, domin yau kwanaki uku kenan da ya sami qwararan hujjoji da suka tabbatar masa Abba yana cikin samarin da suka yi wa Sadiya fyade. Dalili daya ne ya hana shi kama Abban shi ne jiran a gama komai na kwaramniyar bikinshi. Sai da suka rufe hancinsu sannan suka iya daukarsu Abba zuwa asibiti saboda irin warin da ciwukan jikinsu Abba yake yi. Basu sha wata wahala ba bayan zuwansu asibiti, kasancewar Abdul ya nuna musu I.D card dinshi na qwararren jami’in tsaro. Bai koma gidanshi ba sai da gari ya waye, a lokacin qarfe shida da rabi na safe. QARSHEN TIKA TIKA TIK! Dakin cike yake da jama’a suna mamakin labarin da Abba yake fada musu cikin mawuyacin hali, idan ka dauke Aisha da ta ke watsawa Abba kallon tsantsar tsana babu wanda bai tausayawa halin da su Abban suke ciki ba. Abban ya nisa cikin matsnaninciyar azaba ya ci gaba da faxin, “Yarinyar da muka sace a gurin cin abinci muka kai ta wani kango muka yi mata fyade, ita ce jiya muka gani a gefen titi muka sake daukar ta a matsayin karuwa, ba mu gane ta ba sai da muka isa cikin gangon muka tuve don biyan buqatarmu. Ashe ba mutum ba ce Aljanah ce, wani abu ta watsa mana sannan ta vace daga gurin…” Yana gama faxin haka ya fara ihu cike da azabar ciwukan da suke jikinshi. Ko kafin likitoci su yi wani yunquri don ba shi agajin gaggawa rai ya yi halinsa, kamar sauran abokansa. Kasa ci gaba da tsaiwa Aisha ta yi a cikin dakin, saboda tsantsar tashin hankalin da take ciki. Ji take kamar a yanzu ne suka kashe ‘yar’uwarta Sadiya. Hatta shi kanshi Abdul din haushinsa take ji. Domin dan’uwansa shi ya aikata mata abinda ba za ta tava mantawa da shi ba. QARSHE Kwanaki bakwai da Yasmin ta ci burin Abdul ya fara yi a dakinta domin ta quntata wa Aisha ta yi su ne a gidan iyayenta gurin zaman makokin dan’uwanta. Jin irin abin da Abba ya aikata ga ‘yar’uwar Aisha da kuma ganin irin mutuwar da ya yi hakan ya yi matuqar sanyaya wa Yasmin da iyayenta jiki a kan Aisha. Har daki Yasmin ta biyo ta da kukanta tana roqonta gafarar abinda ta yi mata. Tare da roqon su shimfida zaman lafiya a gidan mijinsu. Ba ta ja da zafi ba ta amince bayan ita ma ta roqi afuwar Yasmin din a kan duk wani savani da ya tava shiga tsakaninsu. Tana shiga cikin bedroom dinta ya janyo ta jikinsa ya rungume yana fada mata kalamai masu gardi kan irin son da yake mata. Da alama duk ya fi su jin dadin hadin kan da suka samu. Arxo har gida ya zo ya ba ta haquri kan abinda su Abba suka yi wa Sadiya, kunya da nauyin Arzo

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});