Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta ce “Allah ya ba ki haquri, daga tambaya sai cibi ya zama qari?” Ita ma Mummyn Aisha dariya ta yi, sannan ta ce “Wannan salon hausar ke kika santa Aunty Maryam, abinda na sani kawai shi ne kin yi tambaya kuma na ba ki amsa.” Babu wanda ya sake tankawa a tsakaninsu, sai ‘yanmatan daga cikin dangin ne suka fara magana cikin mamaki suna fadin “Laaaa! Aunty wannan kyakkyawar dama diyarki ce? Ya sunanta?” Da fara’arta a fuska ta amsa musu da cewa “Sunanta Aisha, kuma ‘yata ce duniya da lahira. Duk mai neman qarin bayani ko kuma tambaya a kanta ya jira shigowar Ardo.” Da wannan maganar ta rufe bakin duk mai niyyar yin magana a kan Aisha. A dunqule Ardo ya ba su bayani a kan Aisha, kuma bai ba kowa damar tambaya a kanta ba, umarni ya ba da a matsayinsa na babba daga cikin zuri’ar sun san ba zai kawo musu abinda ya san cutuwa ba ne a gare su. Don haka yana umartar su da su riqe ta tamkar ‘ya’yansu na cikinsu. Kuma ita din ‘ya ce ga Aishatu qanwarsu, da mijinta Yusufa. Har qasa ta ringa duqawa tana gaida su daya bayan daya, kuma abinda ta lura da shi shi ne, duk sun yi na’am da bayyanarta a cikinsu. ‘Yanmatan kuwa gaisuwa suka yi ringa yi suna fada mata sunayensu daya bayan daya. Matasa mazan dangin su ma da fara’a suke gabatar mata da kansu suna musayar lambobin wayoyin juna don sada zumunci. Abinda ta lura shi ne daga mazan har matan burinsu kowa ya fi samun kar6uwa a gurin ta. Fuskarta qayace take da murmushi, kowa da matsanancin fara’a take gaida shi, bayan Ardo akwai qannensa maza guda biyu da suke qarqashin ikonshi, su da iyalinsu. Yawa ne da su sosai, kuma da ganin su ake gane gane fulani ne, abin da ya ba ta mamaki shi ne: duk kyau da farar fatar da suke dauke da su ba sa gani, kyawunta kawai suke magana a kai. Bayan an gama tattaunawa a kan Aisha ana shirin addu’ar tashi daga zaman Yasmin ta miqe tsaye ta dubi tsakiyar idanun Ardo ta ce “Ardo kafin a yi sallama ina da magana idan an ba ni dama” Nan take idanu suka koma kanta, kowa yana sauraron abinda zata ce. Mamaki ne matsananci a fuskar iyayen zuri’ar, don yaro bai cika samun ikon magana ba sai abinda aka zartar a kan ko waye sai dai ya bi umarni. “Fadi maganarki, an yi miki izni” Mahaifin Abdul shi ya yi maganar, bayan ya kallo idanun mahaifinshi ya fahimci ita yake jira. Ba tare da wata kunya ko tsoro ko shakkar abinda zai biyo bayan maganar tata ba taci gaba da kallon Ardon ta ce, “Idan zai yiwu ina buqatar a gaggauto da daurin aure na da Abdul zuwa nan kusa, domin ina cikin matsananinci halin da zan iya fad'awa wata mummunar hanyar matuqar babu mijin aure a kusa da ni" Shiru ne ya gifta tsakanin mazauna falon na wasu mintuna, ba a jin motsin komai sai hucin iskar A.C da ya wadaci tafkeken falon taron. Kayan cikin Aisha ne suka yi wani irin hautsinwewa ba tare da sun shiryawa hakan ba. Fitsarin da ya cika mata mara ya sa ta rintse idanu, sannan ta yi qasa da kanta, sad'af-sad'af ta fice daga falon zuwa cikin gida. Daya bayan daya ‘yanmata da matasan samarin dangin suka ringa sulalewa suna ficewa daga falon. ‘Yanmatan dai cikin gidan suka shiga gurin Aisha, yayin da samarin suka nufi qofar gida suna kakabin al’amarin a zuciyarsu. Yasmin tana zaune daram a inda take zaune tun farko tana jiran hukuncin da za a zartar a kan ta. Iyayenta kuwa ji suke ina ma qasa za ta tsage su shige don matsananciyar kunyar da diyar tasu ta basu, rashin samun gurin 6uya yasa suka sadda kawunansu qasa suna wasa da yatsun hannayensu. Ardo shi kanshi rasa abin cewa ya yi, don haka ya yi shiru yana jinjina qarfin hali da rashin kunya irin na Yasmin. Iyayen Abdul ma sadda kai suka yi qasa sun kasa cewa komai, don maganar ta girmi tunaninsu. Ba su ta6a tunanin haka daga Yasmin din ba. Mummyn Aisha kuwa zuciyarta da tunaninta kashi tamanin yana kan Aisha, tana tunanin ko a wane hali take ciki? Duk wani mazaunin falon shiru ya yi ana jiran wane hukunci mai gayya mai aiki wato zai zartar a kan maganar? “Alhaji ina ganin a duba maganar yarinyar nan! Tunda ta iya bude bakinta ta yi irin wannan maganar a gabanmu tabbas tana cikin wani hali. Idan zai yiwu a dawo da daurin auren nasu zuwa sati mai zuwa. Ko me ka ce Alhaji Babba?” Daya daga cikin qannen Ardo mai suna Alhaji Bello ya yi wannan bayanin yana kallon Ardo bayan ya yi duba da yadda lokaci yake tafiya har ana daf da kiran sallar azahar ba tare da sun yi duba a kan maganar Yasmin ba. “Shawararka yayi daidai Bello. Amma da sharadin matuqar aka daura aurenta da Modibbo a sati mai zuwa ba za ta qarasa karatun da take yi ba, domin tun da farko ba komai ya sa muka nisanta kwanakin bikin ba sai don ta samu daman kammala karatunta” Ardon ya fadi hakan da sanyin murya, domin yarinyar ta yi abin da bai ta6a tsammani ba. Alhaji Ibrahim, d'aya qanin mai bin Alh. Bello sai kuma Ardo shi yayi mata tambayar “Ta amince da abinda aka zartar na rashin ci gaba da karatunta?” Kai tsaye ta amsa ta amince, sannan ta miqe zuwa cikin gidan, fuskarta qunshe da fara’a mara misaltuwa. Ganin shigwarta bai sa sun yi shiru daga hayaniyar za6a ma Aisha sunan da za su ringa kiran ta da shi ba, tunda sunansu daya da Mummynta. Tana zaune tana bin su da idanu fuskarta dauke da murmushi, amma a can qasan zuciyarta Allah ne kadai ya san zafi da turirin da take ji, yadda son Abdul ya shiga zuciyarta farat xaya sam ta manta da bayanin maganar aurenshi da Yasmin. “Inna lillahi wa inna ilaihirraji’un! Yanzu idan Abdul ya fasa aurena ina zansa kaina?” Ba zato babu tsammani wannan tambayar ta fado a ranta. Take ta yi istigfari tare da addu’ar kada Allah ya sa hakan ya kasance. Tana son Abdul son da har ba ta san iyakarshi ba, ba ta fatan wani abu ya gifta tsakanin soyayyarta da Abdul-Ahad. “Smally tunanin me kike yi haka? Tun dazu ake ta miki magana ba ki san muna yi ba?” Zainab wacce Aisha ta fahimci ciki daya suka fito da Abdul saboda tsananin kamannin da suka yi, kuma a shekaru ba za ta wuce sa’ar ta ba. Ita ta jefo wa Aisha wannan tambayar bayan ta hura iska a idanunta, wanda ya yi sanadin dawo da ita daga duniyar tunanin da ta fa d'a. Lumshe idanuwa ta yi ta bude, gami da sauke ajiyar zuciya mai nauyi, sannan ta watsar da ko wane tunani ta maida hankalinta a kansu gaba d'aya. “Hmmm! Wa ne suna na ji kin kira ni da shi haka?” Ta tambayeta ta na murmushi. “Smally! Ko sunan bai yi miki ba ne?” Hafsat ce ta amsa mata tambayar da tayi. Dariya Aisha ta yi, kamar

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});