Chapter 15
Chapter 15
ba.” An sosa wa Abdul inda yake yi masa qaiqayi, don haka ya sake yabon maigadin da cewa, “Ni ma tuni na fahimci qoqarin da kake yi Inusa, kuma ya kamata a qara maka albashi, domin ka cancani fiye da dubu talatin a wata. Amma kai kana ganin wane irin ciwo ne a jikin Abba haka? Mutanen gidan nan sun ankara kuwa?” Da matuqar mamaki a fuskar maigadin ya ce, “Amma dai kun kwana biyu ba ku hadu da Alhaji Abba ba ko Ranka ya dade?” Kai tsaye ya amsa masa da cewa, “Qwarai kuwa, tun da na dawo Kaduna da aiki na bar gidan nan ban qara haduwa da shi ba sai yau.” “Shi ya sa ba ka san da wadannan ciwukan a jikinshi ba, ina tunanin yau kimanin kwanaki tara kenan ko goma da ya dawo gida da wadannan ciwuka. Amma dai ban san ko da me ya ji su ba, ni dai na fi tunanin dambe suka yi da wani ya yayyanka shi. Abin daure kai game da ciwukan shi ne, a kullum yana sha da shafa magani a kansu, sam sun qi nuna ko alamun warkewa. A dazu ma sai na ji ciwon har wari-wari suke yi suna fitar da wani irin ruwa. Ni addu’ar da nake yi ma Allah ya sa dai ba wani abu abokin fadan nashi ya yi masa ba.” “Wani abu kamar me kenan?” Abdul ya tambaye shi da mamaki a fuskarsa. “Wani abu kamar asiri mana, ka san mutanenmu mafi yawancinsu babu tsoron Allah a zuciyarsu. Dariya Abdul ya yi sannan ya ce, “Ba na tunanin haka Inusa, wataqila dai magungunan da likitoci suke ba shi ba ya amfani da su daidai, kuma a kan lukutansu. Ko kuma lokacin warkewar ciwon ne har yanzu bai yi ba.” “To Allah dai ya kawo sauqi, domin ko mutanen gidan hankalinsu tashe yake a kan ciwon nan, shi Abban ne ma dai na ga kamar bai damu ba.” “Ciwo a jikinshi, amma a ce bai damu ba Inusa? Ai in da wanda ya damu a kan ciwukan bayan shi ne.” Shiru Inusa ya yi yana tunani, daga bisani kuma ya ce, “Ina da hujja a kan abinda na fada Ranka ya dade. Ka ga duk da wadannan ciwuka na jikinshi bai fasa fita a kowane dare kamar yadda ya saba ba. Ko yau da ya dawo gida a wannan lokacin sai da na yi mamaki sosai a zuciyata, domin lokacin dawowarshi shi ne qarfe daya da rabi zuwa biyu na kowane dare. Idan ka ga Alhaji Abba ya dawo da wuri, to kana cikin gidan ne.” Ajiyar zuciya mai nauyi Abdul ya sauke, a ranshi yake Allah wadai da sakaci irin na Baffanshi da matarshi. Sun manta yanzu dan’adam ake kiwo ba dabba ba? Kiran sallar farko da ya ji an yi daga masallaci can nesa da gidan ya sa ya mai da idanunsa kan agogon wayarshi. Qarfe hudu na asubahi. Miqewa tsaye ya yi sannan ya sa hannu a aljihun wandonshi ya zaro kudi masu dan yawa, a qiyasce za su kai dubu goma sha biyu. Inusa ya miqawa tare da fadin, “Inusa ga wannan ka sai katin waya. Zan duba mota ta idan ta tashi zan tafi gida yanzu.” Hannu biyu maigadin ya sa ya kar6i kudin yana godiya tare da yi wa iyayen Abdul addu’a. Har ya sanya kanshi ya fice daga dakin sai kuma ya juyo yana kallon maigadin dake biye da shi a baya don bude mishi qofar gidan. “Uhmm! Ba na buqatar iyalan gidan nan su san a nan na kwana, domin Baffa ba zai ji dadi ba idan na kwana a gidan nan na tafi ba tare da mun gaisa da su ba.” “An gama ranka ya dade, matuqar ba kai ne ka fada musu ba ba za a tava jin haka daga bakina ba.” Yana tafe a mota yana tunani tare da saqe-saqen maganganun da suka yi da maigadi a zuciyarsa, har ya isa gidanshi. Sai da ya gabatar da sallar asubahi sannan ya kwanta da nufin rintsawa zuwa qarfe bakwai na safe, awa daya daidai ya dauka gurin shiryawa don haka takwas da minti ashirin a ofis ta yi masa. Sai da ya nitsa bayan ya gama duba wasu fayil sannan ya dauko wayarshi a laluba lambar Yasmin. A lokacin tana tare da Hidaya tana ba ta labarin duk abinda ya faru cikin farin ciki da murna. “Yanzu dai kina nufin kin haqura da karatunki kenan gaba daya?” Hidaya ta tambaye ta da mamakin wauta da rashin hankali irin na qawar tata. “Qwarai kuwa! Ke kin ga laifina?” Yasmin ta amsa mata kai tsaye ba tare da shakkar komai ba a cikin zuciyarta. “Hmmm! Ai ni na rasa ma abinda zan ce. Kawai dai sai in yi miki fatan Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi.” “Amin qawata, yanzu kika yi magana...” Waqa mai taken “A so da kaunar juna zan so a ce ka tausaya min, komai wuya da dadi ni da kai a ce ba za mu rabe ba, a so da qauna da amana zuciya tana son rarrashi... Kawalwalniyar soyayya ta shige min ruhuina...!” shi ne ringing din da ta saka a lambar Abdul. Jin sautin waqar yana tashi ya sa ta lalubo wayar tata tare da sake qawata fuskarta da fara’a. “Kin ga dan halak ya kira ni. Kamar yana da masaniyar maganarshi muke yi.” Ta fadi hakan tana kallon Hidaya, sannan ta latsa madannin amsa kira. Hidaya dai ba baki sai kunne, domin al’amarin qawar tata yana kwance mata kai a duk sa’adda suka had'u. Sai a yau ta sake tabbatar da rashin hankalin Yasmin. Don haka ta yi tagumi tana kallon yadda Yasmin take magana a wayar tana kashe ido kamar Abdul yana gabanta. “mijina barka da asuba, ina fatan ka wayi gari zuciyarka cike da soyayyar qanwarka kuma matarka nan da kwanaki shida kamar yadda na tashi, zuciyata cike da soyayyarka da dokin ganin ka.” Sai da ya numfasa a zuciyarshi jin yadda ta iya jero wadannan dogayen kalmomin ba comma, balle fullstop, a tunaninta wai hakan zai burge shi. Bai amsa tambayar da ta yi masa ba ya ce, “Kin tashi lafiya?” Murmushi ta yi kamar yana kallon ta, domin a daren jiya ta gano abinda ke saurin karyar mishi da zuciya, don haka ta amsa masa da cewa “Na tashi lafiya qalau mijina, ina fatan kai ma hakan?” “Alhamdu lillahi. Na tashi lafiya har ga ni a ofis na fara aikin da yake gabana.” “Allah ya taimaka mijina, don Allah ka kular min da kanka.” Ta fadi hakan a marairaice cikin salon kwantar da kai hade da roqon alfarma. “Kar ki damu, na gode da kulawarki.” Ya amsa cikin jin dad'i. “Aikina ne in kula da kai mijina, balle ma wannan ba komai ba ne a cikin kula da qauna da soyayya da tarairayar da na tanadar maka idan mun yi aure... “ “Uhmmm! Na ce ba...” Cikin sauri ya katse maganar da take yi jin tana neman bata masa lokaci bai tambaye ta dalilin da ya sa ya kira ta ba. “Ina jin ka mijina!” Ta amsa tare da qara maida hankali a kan wayar. “Wai wane irin ciwuka ne a jikin Abba? su
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31