Chapter 1
Chapter 1
A Dalilin DA NAMIJI 3 NA Fareeda Abdallah Tana zaune daga ita sai dan kamfai a gaban dan tsamurmurin Bokan da ta kira shi da sunan “Arne na Kan Tudu” Ta sha matuqar wahala kafin ta samu isa gare shi, motarta a can bakin titi ta bar ta, sannan ta yi tafiyar tsawon awa biyu tana hawa kan tudun don isa gurin "Arne na Kan Tudu”. Ta zagaya guraren bokaye har biyar duk amsarsu iri daya take kasancewa da bokan da qawarta Mariya ta kai ta gurin shi. Tana da tabbacin buqatarta za ta biya, tazo inda za a share mata hawaye. amma bokan yana da sharudda kafin a isa gurinsa. Shi yasa ba ta zuwa gare shi sai ta ga buqatarta ta sha gaban kowane boka da take harka da shi. Amma ta san da ta kawo mishi matsalarta yake magance mata. Babu wata buqata tata da ya gaza biya mata. kowane Daya daga cikin sharuddanshi shi ne, sharuddanshi “Za ki daina bin duk addinin da kike kai har na tsawon kwanaki uku kafin ki je gare shi. Na biyu kuma tun daga gurin da kika ajiye abin hawanki za ki tube kayanki tsirara ba abinda za ki sanya a haka za ki fara hawa kan tudun da bokan yake zaune. Tafiya ce kuma ta tsawon awa biyu. Daf da isa gurinshi za ki ga wani dan kamfai rataye a ganyayyaki sai ki dauka ki sanya, sannan ki qarasa gurinshi. Kallon ta yake da manyan idanunshi jajaye masu firgita qaramin yaro, qaton kan da yake d'ore a d'an siririyar wuyarshi shi zaisa a yi tunanin a kowane lokaci kan zai iya rinjayar jikin. Ihu mai qarfi ya qwalla bayan ya gama kallon qwayar idonta. Busashhen hannunshi mai nuna alamun rashin jini ya buga a qasa yana babbaka dariya, nan take hoton kyakkyawar fuskar Aisha ya bayyana. “Kin zo a kan wannan, kuma kin je gurin mugaye har biyar sannan kika zaiyarce ni, ko ba haka ba?” Ya tambaye ta cikin tsawa da daga murya yana watsa manyan idanunshi a kanta. “Haka yake mugu dan muguwa jikan mugu, tatta6a kunnen mugwaye. Wadancan sun kasa saboda rashin qwarewarsu a kan mugunta shi ya sa na zo gare ka shugaban mugwaye. don na san babu abinda zai gagare ka dan gidan mugu.” Ta amsa cikin daga murya kamar yadda ya yi mata tambayar, tare da yi mishi kirarinshi. Duk wannan yana daga cikin qa’idojinshi. Idanuwanta tsaye suke kyam a kan fuskar Aisha tana murmushin mugunta, don tana ganin lokaci kadan ya rage mabudi da mukullin rayuwar Aishan ya dawo hannunta. Ta sha alwashin maida Aishan kadarar da za ta samar mata da biliyoyin kudi, sannan daga qarshe ta lalata rayuwar yarinyar saboda wahalar da ta sha kafin ta samu biyan buqatarta a kanta. Dariya ya qyalqyale da ita, sa6anin dariyar dazu da ya yi ta cikin babbar murya. Wannan karon dariyar siririya ce mara dad'in sauraro.in “Tabbas za ki samu biyan buqata idan ba ki manta da qa’idojina ba" Ya fadi hakan yana kallon ta, bayan ya katse dariyar tashi kamar an yi ruwa an dauke. “Ban manta ba mugu dan muguwa, jikan mugu. Tatta6a kunnen mugwaye.... a kwana biyu....” Ta daga yatsunta guda biyu tana kallon qwayar idanunshi. “Yauwa muguwa, rayuwarki a mugunta za ta qare. matuqar kina tare da mugu a kwana biyu buqatarki za ta biya. Yarinyar da kanta za ta neme ki idan kika ga haka buqata ta biya. Sai ki kawowa mugu budurwar da zai sha jininta a matsayin ladan aikinki, amma wannan aikin naki yana da sharadi muguwa.” “Na amince da duk wani sharadi matuqar zan sami biyan buqatata mugu dan gidan muguwa, jikan mugu, tattava kunnen mugwaye.” “Kamar yadda wadancan mugayen suka sanar da ke yarinyar tana da shiri a jikinta, don haka idan ba mu samu damar shiga jikinta ba mugu zai dauki ladan aikinshi a jikinki, ta hanyar tsotse jinin jikinki gaba daya.” Ba taji wani dar ko tsoron abinda mugu ya fada a matsayin sharadi aikinta ba, domin tana da tabbacin babu abinda zai gagare shi a kan al’amarin Aisha. Da qwarin gwiwa da na zuciya ta baro gurin Mugu bayan ta ajiye masa dan kamfanshi a inda ta dauka. Ba ta damu da tsirarun motocin da suke wucewa suna kallon ta a lokacin da take tsaye tana maida kayan jikinta ba. Tana gama sanya kayanta ta ja motarta a guje ta bar gurin tana dariya da farin cikin nan da kwanaki biyu buqatarta za ta biya. * ** Kamar kowane lokaci, da sallama ta amsa wayar, fuskarta dauke da qayataccen murmushi kamar yana kallon ta. ba kamar yadda ta saba jin muryarshi ba, yau muryarshi a matuqar sanyaye take. Hankalinta a tashe take tambayarshi da cewa, “Lafiya kake kuwa Abdul? Me yake damun ka?” Sai da ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi sannan ya amsa mata da cewa “Aunty wai don Allah ya kuke so in yi da raina ke da diyarki ne? Yau kwana daya da yini daya sam ta qi daukar wayata, rabon da in ji muryarta tun shekaran jiya da muka rabu da ita a gurin Ardo. Idan wani laifi na yi mata bai kamata ta hora ni da rashin jin tattausar muryarta ba. A da da ban samu Aisha ba soyayyarta mai sauqi ce a zuciyata, ina da jarumta da kwarjini da nake iya ci gaba da aikina, duk da son ta ne danqare a zuciyata, amma a yanzu da na same ta bai kamata a wahalar da ni ba. Wallahi ba ni da wani jarumta a kan Aisha, ina son ta son da ban san iyakarshi ba. Don Allah ku tausaya min kada son Aisha ya zama ajalina.” Ya qarasa maganar yana shesshekar numfashi, da alamun gaf yake da ya saka kuka a kowane lokaci. Tausayinsa ne mai tsanani ya rufe ta, har ga Allah ba ta da masaniyar Aisha ba ta daukar wayarsa. Tana cikin yin wannan zancen zucin ta hango fitowarta daga dakin da yake a matsayin nata, ta yi kwalliya da riga da siket na kayan turawa, kai tsaye gurinta ta nufo tana murmushi. Ba tare da ta amsa mishi ba ta katse wayar ta maida hankalinta gaba daya kanta tana maido mata da martanin murmushin da take mata. Dan nesa da ita ta zauna tana jiran jin abinda zata ce, don ta lura bakinrta akwai abin cewa. “Babyna zo nan.” Ta umarce ta tare da nuna mata gefen ta a matsayin gurin zamanta. Kusa da ita ta dawo ta zauna amma maimakon ta zauna a kusa da inda take zaune a kujera sai ta zauna a qasa kusa da qafafuwanta. Tare da maida hankalinta gaba daya kanta. “Babyna, me Abdul ya yi miki ba kya daukar wayarsa?" Ta tambaye ta tare da qura mata ido don jin amsar da za ta ba ta. kunya ce matsananciya ta kawo mata ziyarar bazata, don haka ta sunkuyar da kai qasa tana matsa ‘yan yatsun qafarta. “Mummy ni fa kunyarshi nake ji, idan na dauki wayar tashi me zan ce mishi?” ta tambaye ta bayan ta yi jarumtar korar duk wata kunya da take neman hana ta sakewa da wacce ta dauke ta tamkar diyarta da ta haifa. “Haba Babyna, wace irin kunya kuma? Ki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31