Chapter 26
Chapter 26
ya sa aka daura auren ba. Zuciyarshi na quna saboda irin baqaqen maganganun da ta iya rintse ido ta kwakkwava mishi. Amma kukan da take ya danne duk wata damuwa da yake ciki. Ba zai iya ficewa ya bar ta a cikin wannan halin ba, domin Mummy ta sanar mishi tunda ta samu labarin an daura aurensu kuka take yi, kuma shi ma ya ga alamun hakan ko daga yadda idanunta suka canja kala a yinin yau kadai. Inda take zaune tana kuka ya dawo ya tarairayo ta gaba daya ya hada ta da qirjinsa ya matse tsam, duk yadda ta so ta qwace ta kasa, ya riga ya yi mata riqon da ba za ta iya kufcewa ba. Dan towel din kanta tuni ya yi nashi gurin, a yanzu qoqarinshi ya zame wanda ta rufe qirjinta da shi. Tuni ta daina qoqarin qwatar kanta, sai qoqarin qare qirjinta da ya bayyana saboda samun nasarar cire babban towel din da ya yi. Da hannunshi daya ya riqe hannayenta biyu, sannan ya ci gaba da zagaya daya hannun nashi a duk wani sashe na jikinta. Dukiyar Fulanin da suka jima suna tsole masa idanu hankalinsa ya fi tafiya a kai, domin ya gan su a fili ba kamar kwanaki ba da sai dai ya gan su a tsaye a cikin riga. Ashe duk yadda yake tunanin kasancewarsu sun wuce nan. Duk girmansu a tsaye suke kyan, ko alamar tanqwarewa babu. Farare shar da dan qaramin bakin kai samansu gwanin ban sha’awa da daukar hankalin mai kallon su. Tuni ta nemi kuka ta rasa, domin ya kashe mata jiki. Yanayin da take ciki baqo ne a gare ta, amma a ranta tana ji ba ta qi su kasance tare da shi ba har abada a hakan. Idanunta lumshe ta miqa masa wuqa da nama na kowane sashe na jikinta. A yanzu kam ya sakar mata hannuwa domin ya san ta kai gejin da ba za ta iya qwace kanta ba. Dai-dai ne daga cikin sassan jikinta bai sanya bakinshi ya tsotsa ba, sai da ya gaji don kanshi sannan ya maida kanta qirjinsa ya rungume tsam ya lumshe ido kamar yana tsoron kada wani ya qwace masa ita. Ba ta san iya adadin lokacin da suka dauka a haka ba amma ta san sun kai matuqa gurin dad'ewa. “Matata don girman Allah ki yi haquri, na san ni mai laifi ne a gurinki, amma duk abinda kike tunani wallahi ba haka ba ne, ki daure ki ba ni dama in fahimtar da ke duk wani abu da ba ki sani ba.” A kunnenta ya rada mata hakan yana shafar gashin kanta zuwa bayanta. A hankali ta zame jikinta daga nashi, ta kasa had'a ido da shi, can nesa ta hangi towel din da ta daura, lura da abinda take niyyar yi ya sa ya yi saurin dauko mata towel din sannan ya tsayar da ita tsaye, ya daura mata. Laluben idanunta yake domin ya aike mata da saqo da nashi idanun, amma ta qi ba shi damar hakan. Gefen gadonta ta koma ta zauna ta had'a kai da gwiwa, murya ciki-ciki ta cea “Lokacin sallah ya qure…” Agogon dakin ya kalla, qarfe bakwai da kwata na dare, har inda take zaune ya matso ya tsuguna a qasa ya ce "Ki yi haquri Aisha, zan je masallaci in dawo, don Allah ki kwantar da hankalinki.” Shiru ma amsa ce. Ganin da yayi ba ta da niyyar amsa masa ya sa ya kama hanyar ficewa daga dakin, don haka ta daga kanta tana bin bayansa da kallo. Hmmm! Lallai namiji ba shi da kunya, kayan jikinshi a yamutse amma a haka ya fice daga gidansu ko kunyar Mummynta bai ji ba.” Wanka ta sake yi, sannan ta yi alwala ta yi sallar magriba da isha’i, ta idar da sallar ta saka rigar barci ta hau gado ta kwanta, idanunta suna lumshe taji shigowar Mummy. Ita ce ta matsa mata sai da ta dan ci abinci, sannan ta kwanta barcin da sai can tsakiyar dare sa’annan ya dauke ta. ****** Lokacin da ta sami labarin yadda daurin aurenta ya kasance saboda tsananin tsorata da firgita yanke jiki ta yi ta fadi a sume. Qawayenta ne suka yi ta yayyafa mata ruwa hankalinsu a tashe domin sun rasa gane kan al’amarin. Zuwan iyayenta shi ya sa ta sake narkewa cikin kuka take fadin duk irin muggan kalaman da suka zo bakinta a kan duk wani mai hannu a cikin wannan cin amanar da aka yi mata, kamar yadda ta kira hada daurin auren cin amana da munafurci. Iyayenta haquri kawai suke ba ta hankalinsu a tashe, domin sun san ba su da yadda za su yi sai dai su zura ido tunda abin ya faru ne daga sama. Wannan daura aure na Aisha da Abdul shi ne abinda ya rushe duk wani tsare-tsare da Yasmin ta yi niyyar gudanarwa a bikin. A yamutse take har zuwa lokacin da ya dace a miqa ta gidan mijinta. Daqyar mahaifiyarta ta rarrashe ta ta yi wanka ta canja kaya, mai mata kwalliyar da aka dauko musamman tun daga Kaduna ta cancada mata kwalliya aka miqa ta gidan Ardo, kakanni da iyaye suka yi mata nasiha sannan aka dangana da ita gidan mijinta. Sai bayan tafiyar kowa aka bar ta daga ita sai qwayenta sannan suka fara tattauna al’amarin kishiyar bazatan da aka yi mata. Qawayenta na Kaduna qara tunzira ta suke yi suna ba ta muggan shawarwari na yada za ta gasa kishiyar ta yadda da qafafunta sai ta bar gidan. Idan kuma har tana taqama da kyau ne ta nemi ruwan batir ta watsa mata a fuska kyan ya gushe yadda shi Abdul zai tsane ta daga qarshe ya sake ta tare da kora irin ta kare. Bayan ya gama kwashe duk wani abu da za a kalla a ji sha’awarta. “Subhanallahi, wannan wace irin muguwar shawara ce? Wallahi kada ki kuskura su kai ki su baro ki Yasmin, kin san ko shi Yaya Abdul ba zai bar ki ba idan kika aikata wa Aisha wani mugun abu.” Aunty Hafsa ce ta fadi hakan tana watsa wa Hidaya harara, domin ta lura duk cikin qawayen Yasmin ita ta fi kowa zaqewa. “Da sauqi ai tunda mahaifinta na da kudin da zai iya fitar da ita kowane irin qangi ta shiga.” kudin Hidayah ce ta maida martani da haka, tana rama hararar da Hafsan take mata. “Ke da Allah rufe wa mutane baki, kina tunanin kudi za su yi fada da gaskiya ne? to ku zuga ta ta aikata wani mugun abin ta ga idan shari’a ba ta yi aiki a kanta ba, duk da kudin mahaifin nata.” Aunty Habiba ce ta fadi haka cikin masifa domin sun gama tunzira ta. Nan take cacar baki ta kaure a tsakaninsu qiris ya rage a bai wa hammata iska. Abinda ya ba su haushi shi ne yadda a fili Yasmin take goyon bayan shawarwarin qawayenta na Kaduna, don haka suka hada har da ita suka zage su tas! A cikin irin gorin da suka yi mata har da nuna mata yadda take ganin kowa bai da daraja a duk danginsu, don haka idan ba ta canja hali ba sai Aisha ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31