Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

haka bayan ta riqe ha6a tana mamakin Aisha. “Ai ni har na yi course, Allah dai ya nuna min lokacin da zan fara soyayya.” In ji Ilham tana kallon idanun Aisha. “Ni kam ai na rasa ta cewa, wai don Allah ko nauyin magana da saurayi ba ki jiba a waya?” Nuratu ta fadi hakan. Dariya Aisha ta qyalqyale da ita, domin maganganunsu sun sa ta dariya sosai. Ta rasa amsar da za ta ba su don haka ta ce, “Bari in kawo muku breakfast. Domin na san irin wannan sammako ko karyawa ba ku yi ba.” “Haba sai ka ce wasu ke? Shi ya sa cikinki yake a dame da gani an san ba kya cin abinci.” Zainab ce ta fadi hakan. “Sha dayan safe ne yanzu fa. Kina nufin ina latti gurin yin break kenan?” “Qwarai kuwa! Suka hada baki gurin fadin haka. “Mu je falo ku gaisa da Yaya Mu’azzam. Da fatan dai kin shiryawa fitar da za mu yi?” Zainab ta tambayi Aisha bayan ta miqe ta nufi qofar zuwa falo. “Ni kam babu inda zan je.” Ta amsa kai tsaye sannan ta miqe ta dauki siririn mayafi ta rufa a kan hular da ta boye asirin dogon gashin kanta. “Ai wallahi ba ki isa ba, fita dole.” Maryam ta amsa mata tana dariya. “Toh, ba sai ku ja ni ba, ku ji ni da yara za su yi min rashin kunya...” Gaba dayansu suka kwashe da dariya, ita kanta da ta fadi maganar sai daga baya ta ji dariya ta qwace mata, domin dukkansu sai dai su zo sa’annin juna a shekaru. Da haka suka sanya kai cikin falon tare da sallama a bakunansu. Yana zaune a dining suna hira da Mummy, da alamun dai breakfast yake yi, domin Aisha ta ga kofi a hannunshi. Idanunshi a cikin nata yana murmushi ya ce "Aunty ashe dai diyar taki tana magana? Sun yi kama da Zainab sosai, don haka ma ta yi tsammanin shima qanin Abdul ne, amma kallo daya ta yi masa ta fahimci bai wuce shekaru ashirin da daya zuwa da biyu ba. Dariya ta yi cikin tsokana ta ce, “Uhmm! Ya ma sunan? Mu’azzam ko?” “Point of correction! Yaya Mu’azzam dai ko qanwata? Domin ko Zainab na girme ta balle ke.” Cikin salon son girma yake wannan maganar. Sai da ta nemi gurin zama kusa da Mummynta ta zauna, sannan ta watsa idanunta a kanshi ta ce “Ai Zainab tana cikin qanne na na uku ne, ka ga kai kuma qanina na biyu kenan! Don haka ni ya kamata ka kira da Aunty Humaira.” “A haba dai, ke ma kin san na girme ki, domin da ganin idanunki ba ki haura fifteen years ba.” Ya katse ta yana dariya. “Sai ka ce wata kai? Da a gobe ne ma kake neman cika sha hudu a shekaru?” Tunda suka fara tafkawa su Zainab dariya suke kwasa, domin sun fahimci tsakanin Aisha da Mu’azzam qafar gaba ce da ta baya, wato kowa yana son girma. Don haka suka yi bakam suna sauraren wanda zai saki ya bar wa daya. “Lalala...tab! Amma yarinyar nan kin ga gadon barcina, Aunty ke ya kamata ki raba mana wannan gardamar. Wai tsakanin ni da Humaira wa ya girmi wani?” Dariya Mummy ta yi amma ta qi tankawa, ganin haka ya sa Aisha ta yi saurin cewa, “ka gani ko? Mummyna kara take maka amma tabbas ta san na girme ka.” “Hmmm! Haka dai kika ce, ji ya zama dole, amma yarda ba ta zama dole ba...” Sai da Aisha ta yi dariya ganin ya sare da wuri sannan ta ce “Ya ka sare tunda wuri haka qanina? Ka ga wannan jumlar maganar taka ta qarshe ta sa na qara tabbatar da cewa ni ke gaba da kai a shekaru, kawai dai ka yi tsawon qafa ne da har kake tunanin ka girme ni.” Dariya ya yi yana kallon dan tsukakken bakinta da har take kirarin ta girme shi, tabbas ya san ya girme ta, amma haka kawai yake a ranshi tana masa kwarjini ba zai iya jan musu mai tsawo tsakaninsu ba. Don haka ya ce, “Sakar miki kawai na yi qanwata, amma ke kanki kin san ni ke gaba da ke a shekaru nesa ma ba kusa ba.” Kiran wayar Zainab da aka yi ya sa Aisha ta yi shiru ba ta qara tanka masa ba, amma a fili take nuna ba ta yarda da abinda ya ce ba. Yadda Zainab take magana cikin girmamawa da ladabi Aisha ta fahimci da wanda take magana a wayar. Tunaninta bai qara tabbata ba sai da ta ji ta ce “Yaya Abdul muna gidan Aunty Aisha ne.” Shiru ta yi na dan lokaci, sai kuna ta ji ta sake cewa, “Yaya yanzu za mu shiga kasuwa, maganar ankon mu ne na ce bari in kira in yi maka tuni.” Dariya ta yi sannan cikin dan shagwaba irin wanda ake yi wa Yayan da aka shaqu da shi ta ce, "Kai Yaya, ai kai ma ka san dole ne a bikin babban Yaya mu yi shiga ta kece raini...” Shiru ta yi tana saurare daga bisani ta ce “Ammi ta ce babu ruwanta mu neme ka, shi kuma Daddy ya ce idan ya dawo da yamma zai neme mu.” Saurarawa ta sake yi, sannan ta ce, “Eh! Akwai shirye-shiryen da za mu yi namu na qannen Ango da Amarya, amma dai ba mu gama yanke shawara ba, zuwa dare ko gobe da safe zan kira ka.” Kallon ta kawai Aisha take yi, a zuciyartta tana dar-dar kada surutu ya sa ta yi wa Abdul maganarta, domin ta riga da ta nuna musu sam ba ta san shi ba. “A’a, yanzu dai anko za mu fara siyowa mu ba da dinki tun da wuri. Ka san telolin sai a hankali" Ta fada tana sosa kai. Ganin ta miqa wa Mummy wayar ya sa Aisha ta yi tunanin cewa ya yi a ba ta wayar. Sun dauki tsawon mintuna da za su kai goma suna magana da Abdul din, ba ta fahimtar abinda take cewa domin dai tana amganar ne cikin nutsuwa da hangen nesa, amma ta fahimci ya tambaye ta game da ita. Domin ta ji tana cewa, “A’a, sam ba ta tada hankalinta ba, tun jiya da aka yi maganar ban ga ta nuna bacin ranta ba.” Sai kuma ta ci gaba da cewa amsawa da “Eh ko a’a” Wani lokacin kuma ta amsa mishi da harshen fillanci. Daga qarshen maganar da suka yi ne ta fara fahimta, domin ta ji tana cewa “Eh, su biyar ne a nan. Ka san su Hafsat sa’annin Yasmin ne, dole cikin qawayen Amarya za su shiga. Su kuma nasu tsarin daban ne" Sai da ta saurara ya gama magana sannan ta ce “Dubu dari da hamsin ai ya yi musu yawa Abdul, ka san akwai hidima a gabanka, kuma daga nan gida ma za a qara musu wasu kudaden.” Dariya ta yi, sannan ta ce “A’a, ni kada ka janyo min rigima, tana ganin sa’anninta suna yin anko amma ita in ce ta jira yi zuwanka?” Shiru ta yi tana saurarenshi tsawon lokaci, sannan ta ce “Sai dai ka yi haquri, fita ai ya zama

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});