Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 11

Chapter 11

A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ba za ta tanka musu ba, sai can kuma ta ce “Na gode, amma dai ina.... shi kenan na gode ‘yan’uwana.” “Amma dai kina me?” Zainab ta tambaye ta cikin zumudi da son jin amsarta. “Amma dai ina ganin ke ce kika fi cancanta da wannan sunan” Ta qarasa tana dariya, tare da watsa fararan idanunta a kan Zainab don jin me za ta ce. “Amma wayonki ya yi yawa Smally, ni dai na san ba haka za ki ce ba" Maryam ta fadi haka tana jinjina salon waskiya irin na Aisha. “To me zan ce Maryam?” Ta tambaye ta tana zare idanu duk da ta san abin da ta fada haka ne. “Hmmn! Ai ni na rasa ma abinda zan ce, wannan azanci naki ya yi yawa Smally, wai don Allah shekarunki nawa?” Ilham ta tambayi Aisha da madaukakin mamaki a fuskarta. “Ke ni fa ba yarinya ba ce, na wuce duk yadda kuke gani na. Bari in yi tunanin yanzu ma shekaru na nawa?” ta amsa tambayar cikin qara jefa musu wata tambayar tana dariya. “Lalala.... wayo ko Smally? Kina da saurin shiga ran mutum, kin iya magana sosai, zan so haduwarku da yaya Abdul.” Zainab ce ta fadi hakan tana tunanin Aisha ba ta san Abdul-Ahad ba. Kawai ita ma sai ta biye mata da yadda ta yi maganar. “Abdul kuma? Kina nufin akwai wanda ba ya nan a cikin ‘yan gidan nan maza?” “Qwarai kuwa, ai ba Yaya Abdul ne kadai ba ya nan ba, akwai Yaya Abba shi ne Yaya ga Yasmin, suna zaune a Kaduna. Sai kuma Yaya Abdul, shi kuma yana Kaduna yana aikin dansanda...” “Ya nake jin ana magana a kan mijina ne? Allah ya sa dai ba wata ce take neman yi min qwacen miji har gida ba.” Yasmin ce ta yi wannan maganar tare da watsa idanunta a kan Aisha, tana mata kallon da ta rasa gane kanshi. “Ok... ko shi ne Abdul din da na ji Yasmin tana fadin tana da buqata ta matsu a daura musu aure?” Aisha ta tambayi Zainab, sannan ta fakaici idanunsu ta watsa wa yasmin kallon “Ki iya takunki” “Qwarai kuwa shi ne Smally...” Zainab ta amsa mata kai tsaye ba tare da shayi ko shakkar Yasmin ba. Gaba daya ‘yanmatan haushin Yasmin suke ji, don gani take kamar ta fi kowa a cikinsu, musamman da Ardo ya zabe ta a matsayin mata ga Abdul. “Oho dai, duk dan baqin ciki sai dai ya mutu, ni da Abdul mutu ka raba, takalmin kaza. Qwalelen kowacce mayya” Yasmin ce ta fadi haka cikin harzuqa, tana maganar tana watsa harara dama da hagu. “Haba ‘yar’uwa! Kar ki ba da mata mana, ina abin yake wai maye ya ci jariri? Ko kina nufin ba ki yarda da kanki da irin son da ya Yaya Abdul yake miki ba ne?” Hankalin Aisha kwance take maida mata da martani cikin hikima da wayau ba tare da ta bari sauran ‘yanmatan sun fahimci ‘yar tsamar dake tsakanin ta da Yasmin ba. “Babu abinda wata ‘yar iska za ta gwada min sai iya karuwanci da bin bokaye don sato zuciyar Abdul, hadadden saurayi irin Abdul, idan ba tsoro ba ta fito fili mu gwada mana.” “Zaman duniya ai iyawa ne ‘yar’uwa... kana koyon laifi ba don ka aikata shi ba sai don duk ranar da ka tsinci kanka a cikin masu aikata laifin ka san hanyar da za ka kare kanka. Ina ganin har yanzu ba ki gama karantar yadda ake cin ribar zaman duniyar ba. Idan kuwa hasashena gaskiya ne, kin ga kina da buqatar ki sauke duk wani girman kai ki zo ki zauna mu ‘yan’uwanki mu karantar da ke, idan kuma kika tsaya kallon ruwa, kina ji kina gani kwado zai yi miki qafa...” Gaba daya ‘yanmatan dakin suka kaure da shewa suna fadin, “Zancenki dutse Smally, kukan kurciya dai jawabi ne...” Da ganin yadda suke maganar farin ciki ne fal a zuciyoyinsu. Domin yau Aisha ta goge musu bak'in cikin da Yasmin take k'unsa musu. Har shiru ta yi na wasu ‘yan mintuna tana jinjina maganganun da Aisha ta ragargaza mata, cikin laluben hanyar da za ta bi ta rama abinda ta yi mata ta ce “Idan ana maganar ‘yan’uwana a cikin zuri’ar gidan nan ai ba a sakawa da irinki karere.." Karaf wannan maganar a kunnen Gwaggo Dije uwargidan Ardo, don daman duk cafter da suke yi suna zaune ne a cikin falonta. Mari mai qarfi ta kai wa bakin Yasmin da sam idanunta sun rufe ba ta lura da shigowar gwaggon cikin dakin ba. “Diyar da Ardo ya daga hannunta ya gabatar a zuri’ar gidan nan kike kira da karere? Ai son da ake yi wa wacce kike kira karere ya ninka wanda ake yi miki fitsararriya mara kunya. Ta fiki komai da komai, sakara kawai shashasha.” Da sallama suka shigo cikin falon, sannan suka janye hannun Gwaggo zuwa kan kujera suka zaunar da ita. “Yi haquri Gwaggo! Allah ya huci zuciyarki.” Mahaifiyar Abdul Hajiya Binta ita ce ta fara ba Gwaggo haquri cikin tausasan lafuzza. Mummyn Aisha kuwa harara ta watsa wa Yasmin kamar za ta rufe ta da duka. Sannan ta mai da idanunta kan tsohuwar ta ce “Ki yi haquri Gwaggo. A yanzu Yasmin ganin ta take daidai da kowa, tana ganin ta isa fadin duk abinda take so, kuma a duk lokacin da ta ga dama” A zafafe ta d'ago kanta ta ce “Ai sai ta ba da himma, amma ina mai tabbatar mata wannan hanyar da ta biyo ba mai 6ullewa ba ce. Abdul yana da damar auren mata uku bayan ita, don haka ta bi duniya a sannu.” Haushin maganganun Gwaggo ya sa Yasmin ba ta gama sauraren fadan da suke mata ba balle har ta bada haquri, ta dafe bakinta da ya fara tasowa saboda marin da Gwaggo ta yi mata ta fice daga dakin tana guna-guni. Sai da suka gama kwantar wa da tsohuwar nan hankali sannan Mummy ta umarce su da su tashi su yi sallah. Don Daddy ya ce idan ya dawo masallaci za su tafi gida. Tana yafa mayafi bayan sun idar da sallah Gwaggo ta kalli Aisha da fara’a ta ce “Aisha ba za ki tsaya ki ci abincin gidan kishiyoyin naki ba? Ko tsoro kike kada mu taru mu yi miki duka?” Murmushi kawai ta yi don rashin abin cewa, saboda sam ba a taba yi mata irin wannan wasan na jika da kaka ba, sai bayan shigowarta cikin zuru’ar su Abdul. Ammi mahaifiyar Abdul ce ta tare mata wasan da cewa, “Haba dai Gwaggo, ai tausaya muku take kada ta tsaya Ardo ya kasa cin abincinku,, saboda kallon ta kawai ya isa ya kosar dashi. Kuma na tabbata idan tana gidan nan gaba dayanku Ardo zai daina shiga harkar ku sai tata.” “Ai duk wannan kyan nata ko kusa ba ta kama qafata ba.” Ta fada tana dariya mai qarfi. “Mun dai gano ki Gwaggo, kawai kishi ne ke damun ki, don kin gan ta sabon jini...” Wannan karon Zainab ce ta amsa sannan ta janye hannun Aisha suka fice daga dakin suna dariya. Kowane daki na gidan sai da suka shiga, Aisha tai musu sallama cikin karamci da jin dadi

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});