Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

saki jikinki ki nuna masa soyayya tsaftatacciya, kin manta yadda sirikin nawa ya ke da farin jinin ’yanmata ne? Kina son wata ta qwace shi daga gareki ne? Idan ya kira ki a waya ki dauka, ki amsa mishi da sanyin muryar da zai isar da saqon so a gare shi. Ki nuna mishin tsantsar son da kike mishi, ki dage ki qara dasa soyayyarki a kowane lungu da saqo na zuciyarshi. Yadda babu wata mace da za ta samu damar dasa mishi tarkon soyayyarta. Ki nuna mishi kulawa, da tarairaya, da qauna da soyayya yadda zai ci gaba da zama naki ke kadai. kinji Babyna?” Sakin baki kawai ta yi tana kallon Mummy yadda ta zauna tana warware mata duk yadda za ta yi ta sake riqe Abdul gam a hannunta. Duk abinda take fada haddace shi take yi a cikin qwaqwalwarta, don haka ta gyada kai cikin gamsuwa da duk maganganunta bayan ta fahimci ta kai aya a maganarta. “Yanzu ki tashi ki je ki kira shi, sannan ki ba shi haquri cikin marairaita da shagwa6a akan rashin daukar wayarshi da ba kya yi. Tare da alqawarin hakan ba zai sake faruwa ba.” Umarnin da ta da ba ta kenan bayan ta gamsu da yadda ta fahimci darasin da ta yi mata. Ba ta yi sanya ba ko musu gurin aikata umarninta. Missed calls 25 ta gani a wayar tata, daga lokacin da ta bar wayar a kan mirrow zuwa falo gurin mummy. Tana danna kiran lambarshi wani kiran na shigowa don haka ta gyara kwanciya a kan gado ta rungume filo a qirjinta, sannan ta danna ok don amsa kiran tare da fadin "Hello....” cikin sanyin murya da salon jan hankalin wanda aka yi abin dominshi. “Wash Allah, zuciyata....” Amsar da ta samu kenan daga can bangaren. Sannan ya fara sauke ajiyar zuciya yana lumshe idanu hade da dafe daidai saitin zuciyarshi da yake jin kamar son Aisha zai fasa ya fito fili kowa ya gani. Yanayin yadda yayi maganar da saukar ajiyar zuciyarshi da take jiyowa tangaran a kunnenta ya sa ta lunshe ido tana jin wani sanyi da nishadi yana kwarara duk wani sashe na jikinta. Qara rungume filo ta yi tsam-tsam a qirjinta, abinda yake yawo a jikinta ya sa ta kasa amsawa daga bangarenta sai shi ne ya katse shirun nasu bayan sun dauki kusan minti biyar a haka ya ce “Aisha zan mutu, wallahi ba ni da lafiya...” A rude ta fara jan “Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un.” Domin a yadda ya yi maganar tabbas ta fahimci bai da lafiyar. Cikin alamun muryar da ke gaf da fashewa da kuka ta ce. “Me yake damun ka Abdul? Don Allah kar ka mutu ka bar ni...” “Soyayyarki ce Aisha, son ki yana neman ya yi ajalina Babyna... ki tausaya min don Allah...” “Ni dai ka daina cewa soyayyata zai kashe ka Modibbo, ko kana son in yi kuka ne?” ta tambaye shi cikin salon shagwa6a bayan ta fahimci ciwon nashi na so ne. “A’a Babyna, don Allah kar ki yi kuka.” Ya amsa da hanzari don babu abinda ya tsana a rayuwarshi irin kukan Aisha. “Ka ci abinci kuwa yau?” Ta tambaye shi bayan jikinta ya ba ta sam bai ci abinci ba. “Ban ci abinci ba Babyna, rabona da abinci tun jiya da rana...” “Kana son yunwa ta illata min kai ne Modibbo? Ni ma ba zan sake ci ba, ka ga sai yunwar ta illata mu tare...” Ta fada cikin damuwa sannan ta sanya mishi kuka, amma na shagwaba, wanda babu ko digon hawaye a cikinsa. “Oh my God! I’m sorry my wife.” Ya fada cikin yanayin damuwa. Sannan ya fara rarrashin ta cikin tattausar murya tare da daukar mata alqawarin yanzun nan zai yi wanka ya fita zuwa gidan abinci don raya qundunsa. “To, ni dai daga yanzu kada ka sake zama da yunwa...” Ta fada bayan ta tsaida kukan. Magana take tana tura baki kamar yana kallon ta. “Na daina matata, amma sai idan kin yi min alqawarin ba za ki sake qin daukar wayata ba, ko kina so in bar aikina in dawo kusa da ke in zauna ne?” “A’a!” ta amsa da sauri, duk da tana son ta ringa ganin shi a kusa da ita a kowane lokaci, amma tana son ya maida hankali a kan aikinshi da bincike a kan wadanda suka kashe ‘yar’uwarta Sadiya. “Idan na kira ba ki dauka ba wallahi ciwo nake ji a zuciyata, don Allah matata ki daina wahalar da ni ta hanyar rashin jin sassanyar muryarki kin ji?” Ya roqe ta da salon magana irin ta qaramin yaron da bai da qarfi ko dabara sai abinda mahaifiyarshi ta sanar da shi. “To na ji, kuma na daina mijina. Daga yau ba zan sake qin daukar wayarka ba, matuqar ina kusa da wayar, kuma ban yi barci ba. Ka yi haquri da qona zuciyarka da na yi ta hanyar rashin jin muryata ka ji mijina?” Ta amsa da irin salon muryar da ya yi amfani da ita wurin isar da rokon shi. “Yauwa matata, shi ya sa a kowane daqiqa na agogo son ki qara ninkawa yake a zuciyata. Ai ke ba kya laifi a gurin mijinki, kuma har abada ba na tunanin za ki yi min laifin da zai sa in yi fushi da ke. Idan ma za ki yi ko da zuwa gaba ne na yafe miki, duniya da lahira.” Ya fadi hakan cikin nishadi. A muryarshi ta fahimci abinda yake fada har a zuciyarshi iya gaskiyar kenan! “Na gode mijina! Shi ya sa nake tsananin son ka! Allah ya bar min kai mijina.” “Zuciyata domin ke aka halicce ta matata, ba na tunanin a duniya za a sami namijin da yake yi wa masoyiyarsa ko da kwatankwacin son da nake yi miki ne. wallahi ina tsananin son ki har ban san yadda zan kwatanta miki rin tsananon son da nake miki ki fahimce ni ba matata. Da zan iya bude zuciyata in nuna miki irin son da nake miki da na yi hakan matata.... ina sonki Aisha, wallahi ina tsananin sonki. zan iya bada rayuwata don in ceci taki rayuwar Aisha... ina sonki, don Allah kiyi haquri dani ki soni ko da kashi daya bisa dari na irin son da nake miki ne matata...” Ya qarasa maganar yana jan ajiyar zuciya sauri sauri, da hanzari ya sanya hannunshi na dama ya dafe saitin zuciyarshi don ji yake son Aisha yana qoqarin fasa qirjinshi ya fito. “Nima ina sonka Abdul, kawai dai bansan yanda zanyi in nuna maka irin son da nake maka bane, amma insha Allahu inai maka tanadin rayuwa da farin ciki mai dorewa har qarshen rayuwar mu idan mu ka yi aure, ka daina barin soyayyata tana wahalar da kai mijina. Bazan yafewa kaina ba matuqar son da kake min ya cigaba da wahalar da kai mijina...” Ta fada bayan tayi kokarin daidaita natsuwarta daga duniya nishadin da kalaman Abdul suka cilla ta. “Baki da laifi ko kadan matata, soyayyarki a zuciyata wani al’amari ne da Ubangiji kadai yasan dalilin da ya jarbceni dashi. ki daina zargin kanki akan yanda sonki ya zama jinin jikina, wallahi baki da laifi ko kadan.” Ajiyar zuciya na sauke mai nauyi

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});