Chapter 8
Chapter 8
yi tunanin barci ne ya dauke ta, sai washe gari suka nemo maza aka karya qofar dakin, nan aka tsinci gawarta tsirara haihuwar uwarta, kuma jikinta da fuskarta baqi qirin alamun qona ta aka yi. Ta kumbura suntum sai wari gawar da dakin suke yi. Duk tsananin shaquwarta da ‘yanmatan gidan da irin kashe musu maqudan kudaden da take yi kasa zama a dakin da gawar take suka yi, sai wani sashi na daban suka koma da zama a cikin gidan, suka nemo lambobin qawayenta da suka sani, suka kira suna sanar da su abinda ya faru. Minti talatin zuwa awa daya gidan ya cika da manyan mata qawayen danasha. Amma ganin irin mutuwar da ta yi da yanayin da gawartata take ciki daya bayan daya suka ringa sulalewa suna barin gidan. An rasa mazan da za su yi jana’izar ta. Kuka kawai Hajiya Mariya take tana qyamar harkarsu ta ‘yan neman jinsi, a zuciyarta take tunanin “Ashe duk amintakar da suke yi da junansu ta fatar baki ce? Yau ga shi Hajiya Danasha da ta kasance jigon kafuwar qungiyarsu ta rasa masu tsayawa a kan gawarta? Me ake da irin wannan qazanta kuma wulaqanctacciyar rayuwa?” Sai da aka kira sallar Azahar a masallacin dake unguwar da gidan Hajiyar yake sannan Mariya taje da kukanta ta samu limamin masallacin ta yi masa bayanin duk halin da ake ciki. Da liman da Ladan da daidaikun mutane da ba su wuce takwas ba suka sallaci Hajiya Danasha zuwa makwancinta na gaskiya. Hajiya Mariya ita ta ci gaba da amsar daidaikun baqin qawayensu masu zuwa gaisuwa. a ranta ta yi wa kanta alqawarin daina harkar neman jinsi da bin bokaye da malaman tsibbu gaba daya. (Allah ya ba ta iko, Ubangiji ya shiryi sauran masu yi gaba daya, amin). ********* Aisha na tsaye gaban madubi tana shafa hoda a fuskarta ta jiyo vibration din wayarta da ke gefen gado. Sanin mai kiran nata ya sa sai da ta dan ja aji tana gab da tsinkewa sannan ta latsa madannin amsa kiran tana fadin “Hellooo....” Murya qasa-qasa ya amsa kamar wanda ya farka daga barci. Cikin shagwava da marairaita ta ce, “Mijina daga wayewar garin yau zuwa yanzu qarfe takwas da rabi na safe ka kira wayata sau goma sha biyu, Wai ni mene ne ne?” ta yi tambayar tana tura baki kamar yana kallon ta. “Ke ce matata... ke ce wallahi! son ki ya hana ni rintsawa dukda yau lahadi ya kamata in kai sha biyu na rana ina barci” “Ni dai babu ruwana, jiya fa muka dawo daga Kaduna, amma za ka wani ce ni ce na hana ka barci...” “To ai ni ba na gajiya da kallon ki, ko son jin tattausar muryarki, bayan kina ganin har wani rowarki Mummy ta ringa yi min.” “Allah ya huci zuciyar mijina, ai Mummyna ba ta son ka wahalar mata da diya ne.” Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce, “Duk ranar da na dauke diyar ba sai in ga wanda zai yi min rowarta ba?” Dariya ta yi kawai bakinta ya yi mata nauyi ta rasa irin amsar da zata bashi, don haka ta yi shiru tana dan dariya mai sauti da har yake iya juyota ta cikin wayar. “Yi dariya dakyau yarinya, yanzu ai lokacin ne. Kin gama shiryawa ne?” “A’a yanzu dai powder nake shafawa.”gama Ta amsa kai tsaye tana kallon powder da take ajiye a gabanta. “Wani irin powder kuma matata? Ke da na ce kada ki yi kwalliya don kada wasu maza su kalle min ke dukda dai na san hakan ba mai yiwuwa ba ne.” “Su waye wasu maza mijina, taro ne fa na family daga qannenka sai iyayenka ka ga ai babu bare balle har a kalle maka mata ko?” “Su qannan nawa ba maza ba ne? Ni fa wallahi ina tsananin kishin wani ya gane min mata, kuma kar ki kuskura ki yi musu dariya balle har su yi sha’awar ki.” Ya fadi hakan cikin fada. “So kake su dauke ni a matsayin miskila mai girman kai? Kada ka manta taro ne da Ardo ya hada don gabatar da ni a matsayin daya daga cikin ‘ya kuma jini ga danginku, ka ga dole in sanya murmushi a fuskata ko don su karbeni da hannu bibbiyu.” “Wane irin kaya za ki sanya?” Ya tambaye ta duk da haka bai sassauta maganarshi ba. “Doguwar rigar shadda da mayafinta.” Ta amsa kai tsaye zuciyarta na neman 6aci da fada-fadan da yake mata. “Ban yarda ba.... ni wallahi ban yarda ki yi wannan shigar ba matata, kawai ki nemi kayan da kika san sam ba za su yi miki kyau ba, wannan qaton hijabin Mummyn naki za ki sanya, ban yarda kina budewa wasu garada fararan haqoranki ba. In ban da Ardo ya hana ni zuwa taron da duk wannan kallon da za su yi miki bara suyi ba...” Haushi da masifar da yake neman ya tsiro mata da shi wai duk don yana kishinta ya sa ta katse wayar ta jefa ta a kan gado. Sai da tayi minti goma tana maida numfashi da jujjuya maganganun Abdul a zuciyarta. Sannan taci gaba da shirinta, kuma bata fasa sanya kayan da tayi niyya ba. Tana ganin kira har sau goma sha daya, a kira na goma sha biyu ta dauka rai a 6ace ta ce “Wai meye ne? Idan kuma masifan ne ba ka gama ba sai ka dora daga inda ka tsaya...” Tana jin yadda yake sauke ajiyar zuciya sauri-sauri, muryarshi da dan rawa-rawa ya ce “Allah ya ba ki haquri matata, ni wallahi ba masifa nake miki ba, kawai son ki da nake yi ne ya haddasa min tsananin kishinki a zuciyata, don Allah ki yi haquri” “Na ji!!!” Amsar da ta bashi kenan ta sake katse wayar. Bai yi fushi ba ya sake kiran wayarta. Sai da ta tsinke sau biyu, sannan ta dauka a karo na uku. Shiru ta yi ba ta ce komai ba don har a lokacin ba ta sauko daga dokin zuciyar da ta hau ba. “Matata ba ki haqura ba ne? Don Allah na ce ki yi haquri...” “Na haqura, amma gaskiya ka 6ata min rai Abdul, irin kalamin da ka yi amfani da su gurin bayyana min salon kishinka suna nuna kamar ba ka yarda da son da nake yi maka ba ne, kana tunanin a gaban idonka ne nake son ka a bayan idonka zan ci amanarka ne? Ba ka yarda da ni ba ne?” Tana gama jera masa wadannan tambayoyin ta fashe da kuka, domin idan ba hawayen ta zubar ba ba za ta samu sauqin quncin da ya mamaye zuciyarta ba. “Oh my God! Matata don Allah ki yi haquri, wallahi ban yi wadannan maganganun don in bata zuciyarki ba, don Allah ki yi haquri kin ji matata, ko kina son ni ma in yi kukan ne?” sai da ya dau tsawon lokaci yana rarrashin ta har ta daina kukan gasken ta koma yin na shagwa6a, tana bayyana mishi irin son da take yi masa sannan ta haqura. “Ni a haka ma zan je gurin taron da hawaye a fuskata tunda dai na fahimci mijina bai son kwalliyar.” Ta fada tana turo baki kamar yana kallonta.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31