Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 24

Chapter 24

A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zauna yana kallon ta. “Mene ne kuma?” Ya tambaya cikin kulawa. Kukan shagwava ta sanya masa wanda babu ko digon hawaye a cikinshi, hade da bubbuga qafa cikin wani irin salo mai saurin rikita zuciyar wanda ake abin domin shi. Galala ya tsaya yana kallonta, kasa daurewa ya yi, sai da ya kamo hannunta daya yana murzawa a hankali, muryarshi a can qasan maqoshi yake tambayar ta da “Mene ne Babyna? me kike so?” “Ni dai babu inda za ka je saidai mu tafi tare....” Ta fadi hakan cikin shesshekar kuka. “I’m sorry matata, kin ga ba dad'ewa zan yi ba, kuma komai dare zan zo in same ki a gida” “Ni dai… ni dai… ni dai a’a! bayan kai ma ina kallon yadda ‘yanmatan Amarya suke kallon ka suna hadiye miyau.” Dariya mai dan sauti ya yi, sannan ya ce “Kai matata, kishi ko?” “Eh din.” Ta amsa tana tura baki. “To ai duk yadda mata za su kalle ni bai kai yadda maza suke kallon ki da son ki ba. ke fa zinariya ce a cikin mata, duk lafiyayyen namijin da ya kalle ki dole sai wani abu mai kama da so ya d'arsu a zuciyarshi. Shi ya sa har ba na qaunar in gan ki cikin taron jama'a. matuqar akwai maza a gurin" Ba zato babu tsammani suka ga an bude qofar motar ta bngaren direba inda Abdul yake zaune. Wa za su gani? Yasmin ce tsaye ta dafe qugunta da hannaye bibbiyu, tana hura iska da bakinta, da alamun gaf take da fashewa. Kallon-kallo suka yi a tsakaninsu kowa da abinda yake saqa a zuciyarshi. “Da kyau tsohuwar kilaki, ashe har yanzu kina nan a kan mummunar sana’arki ta karuwanci? A tunanina kin shiryu tunda na gan ki a cikin zuri’armu? To wallahi ina tabbatar miki ke da Abdul sai gani sai hange, qwalelen kare da hantar kura. Kuma idan baki kama kanki ba saina tona miki asiri..." Bata tanka mata ba kuma bata saki hannun Abdul ba. don ta qara cusa mata haushi ma sai ta ci gaba da murza hannunshi da yake cikin hannunta. “Yasmin ki saurare ni mana, ki saurara ki ji bayanin da zan yi miki.” Abdul ne ya ringa fadin haka bayan ya lura muggan kalamanta a kan Aisha sun qi qarewa. Inda Allah ya taimaka ma shi ne, gurin ba gilmawar mutane sosai. Sai tarin motocin da aka yi fakin dinsu a gurin. “Ka bar ni in gama goge wannan riqaqqiyar karuwar Yaya Abdul, ba na ta taka, domin na san kai ba yin kanka ba ne, ka riga ka fada tarkon wannan annobar. To wallahi ba ki isa ba, Abdul ya yi miki nisan da ba za ki iya kamo shi ba, ‘yar iska tantiriya wacce ba ta da zuciya. Idan kin isa ki tanka kiga yadda zan yi qasa-qasa da ke a gurin nan!” Sakin hannun Abdul Aisha ta yi domin an zo inda ya dace ta yi magana. Bude motar ta yi ta sauka ta zagaya har inda Yasmin take tsaye, ta ce mortar “Anya kuwa kina kallon kanki a mudubi? Ke kin san ruwa ba tsaran kwando ba ne, don haka ni da Abdul dole ki saka ido a kan soyayyarmu, ba ki da yadda za ki yi da ni. Ina tabbatar miki da baqin cikina za ki mutu Yasmin. Ki adana mugayen kalamanki domin kin fara kai ni bango, ba don kowa nake daga miki qafa ba sai don Abdul, don haka idan kin isa ki sa shi ya daina so na.” Tana gama fadin haka ta bar gurin ta ci gaba da tafiya a qasa ba tare da sanin inda ta dosa ba, tana jin Abdul yana qwala mata kira, amma sam ba ta saurare shi ba. “Hankalinki ya kwanta, tunda kin tunzura ta ta tafi ko Yasmin? To amma fa kin yi a banza, domin kin san ba zan bar ta ta tafi gida ita kadai ba…” Yana gama fada mata haka ya biyo Aisha da sassarfa har sai da ya cim mata. “Aysha ki zo mu tafi in kai ki gidan?” “Na hutar da kai, je ka ji da matarka.” Ta fada ba tare da ta kalle shi ba. “Don Allah fa na ce, ina za ki je a daren nan?” Dada Ya tambaye ta hankalinshi a tashe. “Na Allah ai ba sa qarewa, ba zan rasa mai taimaka min ba.” Hannunshi ya sanya ya finciko hannunta da qarfi, taga-taga ta yi za ta fadi da hanzari ya yi mata masauki a qirjinshi, ya sanya hannunshi duk biyu ya rungume ta. Ture shi ta yi ta qwace jikinta, sannan ta zame ta tsuguna a qasa ta saka masa kuka mai tsuma zuciya. Bai saurare ta ba, illa kiran Mu’azzam da ya yi a wayarshi ya fito waje ya same shi. Mukullin motarshi ya amsa ya ja hannun Aisha tana kuka ya saka ta a ciki. Sannan ya yi masa umarnin ya kai ta gida. Har suka isa gida ba ta tanka wa Mu’azzam ba, ba ta kuma daina kukan ba, sannan ba ta daina sauke ajiyar zuciya ba. tana ganin kiran Abdul yana shigowa wayarta, amma ta qi dauka, daga qarshe ma sai ta kashe wayar gaba daya don har a lokacin haushin sa take ji. Kuma ta yi alqawari a ranta ba za ta sake halartar duk wani taro da za a yi na bikinshi da Yasmin ba har a gama bikin. Washe gari ba ta kunna waya ba sai bayan qarfe uku na rana, bayan ta tabbatar izuwa wannan lokacin an daura auren Yasmin da Abdul. Abinda ya ba ta tsoro shi ne yadda qirjinta ke buga wa fat-fat sai ma danganta hakan da kishin an daura auren Abdul da wata matar ne ba ita ba. Kiran wayar Maryam ne ya fara shigo mata, da dariya ta dauka domin ta san sai ta yi mata tsiyar yau ta yi wuyar gani. “Smally kin san me yake faruwa kuwa?” Ta tambaye ta a rude muryarta har rawa take yi. “A’a, ban sani ba, ba ni labari…” Aysha ta tambaye ta bayan ta lura kiran Zainab ya shigo a lokacin suna tsaka da magana da Maryam. “Yanzun nan aka daura aurenki da Yaya Abdul, bayan an daura mishi da Yasmin" “Haba dai… da wasa kike ko?” Ta tambaye ta bayan ta ji kayan cikinta sun juya ba tare da ta shirya wa hakan ba. “Wallahi da gaske nake…” Katse kiranta ta yi ta dauki na zainab tana sauke numfashi sauri-sauri. “Amarya ce… Amarya ce… Amarya ce amarya ce Amaryah…” Abinda Zainab ta fara fada wa Aysha kenan cikin muryar dake bayyanar tsantsar murna da farin ciki. Katse kiran ta yi hankalinta a tashe ta dauki wayar Mu’azzamn da ya shigo. “Aunty Humaira, yau kin tabbata Aunty a gare ni tunda kin zama mata a gurin Yaya Abdul…” Bude qofar dakinta da Mummy ta yi cikin sanyin jiki yasa ta saki wayar a qasa tana kallon ta. Sai da ta iso daf da gadon ta nemi gurin zama ta zauna sannan Aisha ta mirgina kusa da ita ta dora kanta a cinyoyinta. Muryarta na rawa ta ce “Mummy wai haka ne? wai an daura aurena da Abdul?” Kai kawai ta iya daga mata

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});