Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

suke amsawa. Gaba d'ayansu tambayar ta suke kan yaushe za ta je ta yi musu kwana biyu? Matan yayyen Mummy maza da yayyinta mata duk tambayar Mummy suke da cewa “Aishatu diyar taki ba ki ba da aronta ta yi wa mutane kwana biyu ne?” Da dariya take amsa musu da cewa tana nan zuwa. Aisha ta samu kyautukan kudi masu yawa daga mazan iyayen su Abdul har matan qannen Ardo maza kuwa suka yi ta mata wasan jika da kaka, sannan suka yi mata addu’a da fatan Allah ya yi mata albarka. Su Zainab fadi suke “Wayyo Smally, kamar kada mu rabu.” Dariya ta qyalqale da ita, sannan ta ce, “Rabuwa ai dole ne, duk mai son gani na ai ya san gidanmu.” Musayar lambobin waya suka yi tsakaninta da matasa maza da matan gidan, sannan suka rabu a cikin farin ciki da qaunar juna. Yasmin dai har Aisha ta bar gidan ba ta sake ganin qeyarta ko na mahaifanta ba. Suna shiga mota a karo na barkatai ta sake jiyo vibration din wayarta a cikin jakarta. Da tsaki ta janyo jakar ta ciro wayar, duk idanun Mummy suna kanta. Abdul ne, daman ta san sai shi din. ‘Xan anace.” Ta fada a zuciyarta, gaba d'aya haushi da takaicinshi ya cika mata zuciya, gani take kamar shi ne Yasmin da take neman zame mata qarfen qafa a rayuwa. “Baby yau kuma mijin naki kike kira dan anace?” Dady yai murmushi, yana jan motar yayin da ita kuma tana zaune a sit din baya yana kallon fuskarta ta cikin madubi. Haushi da kishi ya sa ta fashe da kuka don ji take wani abu ya tsaya mata a maqoqwaro ya hana ta hadiye miyan, idan ba kukan ta yi ba sam ba za ta sami sauqi a ranta ba. Sun kusa isa gida don haka a cikinsu babu wanda ya tanka mata har suka isa. Maigadi ya bude musu get, Mummy ce ta kama hannun Aisha har zuwa falo ta zaunar da ita a kan kujera, Daddy kuma ya kulle motar bayan ya dauko mata jakarta da wayarta zuwa falo. “Shalelen Daddy har yanzu kukan bai isa ba ne?” Daddy ne ya jefa mata tambayar bayan ya zauna a kan kujera idanunshi na kan ta yayin da ita kuma ta ci gaba da rera kuka mai ban tausayi. “Baban baby ni ina ga kawai mu je mu yi wa Ardo bayani yanzu ba ta son Abdul, don haka a janye maganar aurensu in ya so sai Allah ya ba ta wani mijin saurayi, wanda ya fi Abdul-Ahad komai da komai.” Mummy ce ta fadi hakan a fusace tana kallon fuskar Daddy tana jiran abinda zai ce. Qirjin Aisha ya buga dam, ba shiri ta tsaida kukan nata kamar daukewar ruwan sama. Bakinta a ture ta kalli Mummy ta ce “Ni dai ban ce ba na son shi ba...” Dariya suka kwashe da ita gaba daya, ita kuma kunya mai tsanani ta kama ta, don haka ta boye fuskarta a tsakanin qafafun Mummy tana dan murmushi domin ta fahimci tsokanarta suke yi. “Toh, idan kina son shi ai babu amfanin kukan ki Babyna, domin na tabbata Abdul ko mata uku zai aura ba zai ta6a juya miki baya ba. Kuma ba zai taba iya daina son ki ba. Domin da bakinshi ya tabbatar min an halicci zuciyarshi ne da soyayyar Aisha. Kin ga daina sonki yana nufin daina bugawar zuciyar Abdul-Ahad.” “Ni kaina na fahimci tsananin soyayyarshi gare ta Maman Baby, ki daina damun kanki, kin ji yarinyata? Dama can Allah bai qaddara ke ce matar farko a gurin Abdul-Ahad ba.” Da haka suka shawo kanta ta yi watsi da duk wata damuwa daga zuciyarta. Kiran Ardo da ya shigo cikin wayarta shi ya sa ta qarasa wartsakewa gaba daya har ta samu qwarin gwiwar ci gaba da linka son Abdul-Ahad a cikin zuciyarta. “Ina fatan ba ki dauki maganar auren Abdul da Yasmin kin sanya ta a zuciyarki har ta zame miki abin damuwa ba Aisha?” tambayar da Ardo ya fara yi mata kenan bayan sun gaisa, ya yi mata ban gajiyar taron gabatar da ita ga zuriyarsu. A kunya ce ta amsa masa da cewa “A’a.” “Ki kwantar da hankalinki Aisha, a sati mai zuwa idan Allah ya kai mu za a daura auren Yasmin da Modibbo, amma hakan ba shi ne zai hana maganar aurenki da shi ya tabbata ba. Ko a yau idan Abdul ya gama binciken wadanda suka hallaka ‘yar’uwarki Sadiya ya miqa su suka fuskanci hukunci zan daura aurenki da shi. Tun fil azal Allah bai qaddari ke kadai za ki zauna da Modibbo ba, don haka ki kwantar da hankalinki, kuma kada ki nuna wa Abdul komai da ya danganci kishi da 6acin ranki, hakan shi ne zaisa ya cigaba da gudanar da binciken da yake yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.” Da haka suka yi sallama da Ardo bayan ta yi masa godiya tare da alqawarin in Allah ya yarda ba za ta sa6a wa umarninsa ba. *** ****** Yana zaune a cikin motarshi a qofar get din gidan, baqin cikin da ta qunsawar zuciyarshi ita da mahaifanta ya sa sam bai yi niyyar shiga da motar ko harabar gidan ba. Duk da agogon motar ya nuna masa qrfe goma da kwata na dare, hakan bai sa ya fasa kiran lambarta ba. Umarni ya ba ta a kan cewa ta fito qofar gidan yana jiran ta. Da murna take canja kayan barcin jikinta zuwa riga da siket na atamfa, wanda ya kama jikinta sosai, duk yadda ta so ta saka jarumta a ranta hakan ya qi yiwuwa, qirjinta na bugawa kadan-kadan, amma fa ko kusa ba ta nadamar abinda ta aikata a can Yola a gaban zuri’arsu. Wanda iyayenta suka kira rashin kunaya, kuma wai a fadarsu za ta yi nadama a can gaba, musamman alqawarin da ta dauka na daina karatun da ta dauki tsawon shekaru biyu da watanni shida tana yi a jami’a, wata uku suka rage mata amma ta za6i watsar da karatun a kan soyayyar wanda bai damu da ita ba. Qwanqwasa qofar motar ta yi bayan ta ja qofar domin budewa, ta ji a kulle take daga ciki. Sai da ta gyara zamanta a kan kujerar mai zaman banza ta kusa da direba sannan ta kashe murya cike da yanga ta ce "Yaya Abdul barkanmu da dare.” Harara ya watsa mata, sannan ya ci gaba da kallon ta qasa da sama. Haushinta matsananci yake ji a zuciyarshi, domin ya san ba don Allah da Annabi ta roqi a kusanto da daurin aurensu ba. Ko ma mene ne dalilinta ita ta sani, amma yana da tabbacin dalilin nata ba ya rasa nasaba da ganin Aisha a cikin zuri’arsu. “Sai na ji kin buqaci a kusanto da daurin aurenmu saboda kina da matsanancin sha’awa ko?” Tambayar da ya jefa mata kenan yana kallon qwayar idanunta don jin shi ma rashin kunya za ta yi masa? Sai da ta gama tattaro dan ragowar yawun da ya rage mata, sannan ta yi qarfin halin cewa, “Ko me na yi ka fi kowa sanin dalilin da ya sa na aikata shi Yaya Abdul, kuma ba don buqatar kaina na nemi a kusanto da

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});