Chapter 22
Chapter 22
ita da su Maryam har ashirin da daya duk ba ta san lokacin da suka kira ta ba. “Matata kin cinye mini lokaci gaba daya...” Ya fada yana dariya bayan ya hasko mata screen din wayarshi fuskarta. Miscalls arba’in da biyar ta gani a wayar tashi. Murmushi kawai ta yi amma ta kasa tankawa don har lokacin hankalinta bai kwanta ba. “Zan je masallaci ki je ki yi sallah ki shirya ki raka ni gidan Ardo…” Umarnin da ya bata kenan sannan ya kama hanyar ficewa daga falon, yana daf da fita gaba daya ta ji ya fara magana a waya da Ardo, domin ta ji ya kira sunanshi yana fadin gashi nan zuwa. Sama-sama ta watsa ruwa sannan ta dauro alwala. Sai da ta yi ramuwar sallolon da ke kanta, sannan ta yi matsakaicin kwalliya cikin riga da siket na English wears ta sanya hula a kanta wadda ta dace da kayan. Ta dauki babban gyale ta yafa ta fito zuwa falon. Yana zaune kushin ya qura wa hanyar dakinta ido, tana fitowa suka sakarwa juna murmushi kafin tace komai kiran Mummy ya shigo cikin wayarta. “Babyna kina ina?” Tambayar da ta fara yi mata kenan cikin kulawa. “Ina gida Mummy amma ga mu nan tahowa gidan Ardo” “Ok, to ki yi sauri, domin yanzu Daddynki ya kira wai zai zo ya taho da mu gida.” “To Mummy, ga ni nan zuwa.” “Allah ya tsare min ku.” “Amin Mummyna.” Ta amsa cikin jin dadin addu’arta garesu. A mota hira suke gudanarwa cikin nutsuwa yana sake jaddada qauna da soyayyar da yake yi mata. Sannan ya roqe ta ta ci gaba da haquri da shi a kan duk wani abu da zai taso a tsakaninsu ko da zuwa can gaba ne. Ta daukar masa alqawari kan cewa in Allah ya yarda ba za ta ta6a juya baya a gare shi ba, duk rintsi duk wuya, komai wahala… za ta kasance tare da shi koda kuwa duk mutanen duniya sun juya mishi baya. “Matata wallahi kamar kada mu rabu yanzu, ina son ki sosai.” Yana riqe da gefen mayafinta a cikin mota yake fada mata hakan, lokacin da ta yi masa sallama tana niyyar ficewa don shiga gidan Ardo. “Na san haka mijina, ni ma ina tsananin son ka sosai, amma ka ga yanzu dare ya fara yi gobe ma rana ce ko?” “Haka ne Matata, gobe ki shirya min breakfast, zan zo da wuri.” “An gama mijina.” Da qyar ya bar ta ta fice daga motar, tana kallon tsantsar damuwar da yake qoqarin 6oyewa a can qasan idanunshi. Amma ta rasa yadda za ta yi da shi tunda dai bai fito fili ya bayyana mata yadda za ta fahimta ba. "‘Yar wulaqanci… ke Smally! Yau dai na ga duk abinda kike 6oye min.” Abinda Zee ta fara ce mata kenan bayan haduwarta da su a tsakar gidan suna zaune a kan fararen kujerun da aka gudanar da saka lallen amarya. “Oh, su cakwaikwaiwa ashe a na nan? Ai na zaci kun dad'e da komawa gida. Yanzu kun kai Legas a barci” Dariya suka kwashe da ita har ita ma ta taya su darawa. Maryam ce ta amsa mata da cewa “Mun kira wayarki har babu iyaka amma da yake tsuntsun soyayya yana kanki ba ki san muna yi ba, don haka muka tambayi Mummynki ko za ki dawo gidan nan, tabbatar mana da za ki dawo ta yi ya sa muka ce komai dare sai mun jira ki kin dawo domin mu sha labari" “Ai ko kun taka zero, domin babu wani labari da za ku samu daga gare ni, sai ku ne ma da nake jira ku ba ni labarin abinda aka yi ba na nan.” “Kin isa ma kice ba za ki ba mu labari ba? ai yau na yi takaicin ina ma zan iya zama quda in je in maqale don ganin yadda Smally take rikita bawan Allah” “Saboda tsabar tsegumi kike fatan zama quda?” Aisha ta tambaye ta tana dariya. “Ai ba ita kadai ba har da mu gaba daya.” In ji Ilham tana dariya. “Ai kuwa da hakan ya kasance da kun bata wasan, domin ina ganin qudaje har hudu a falonmu zan nemo sheltox in fesa musu duk su mace, kun ga gulma ta yi kyau kenan ko?” Dariya suka sake kwashewa da ita gaba dayansu. Sannan ta zame zuwa cikin dakunan matan gidan don duba inda Mummy take a zaune. Ba su dad'e ba Daddynta ya iso suka wuce zuwa gida tare da Zee, domin ta maqale dole sai ta ba ta labari shi ya sa ta yi wa Ammi (mahaifiyarsu) kamar yadda ta ji suna kiran ta waya ta sanar da ita a gidansu Aisha za ta kwana. “Ashe kin san yaya Abdul, amma shi ne kika bar ni ina ta haukan cewa idan ya zo zan hada ki da shi?” Tambayar da ta fara jefa wa Aisha kenan bayan sun yi daidai a kan katifa duk suna sanye da kayan barci. “Wa ya ce miki na san shi Zee?” Harara cikin wasa ta watsa mata tana murmushi, sannan ta amsa da cewa “Ina ganin lokacin da kuka bar gidan Ardo tare da shi dazu, kuma sai a lokacin na fahimci dalilin da ya sa Yasmin take matuqar jin haushin ki.” Akwai qauna da shaquwa mai qarfi tsakanin Aisha da Zainab, don haka ba ta boye mata komai ba game da soyayyarta da Abdul yayanta, amma ta boye mata duk rikita-rikitan dake cikin soyayyar tasu da kuma aihinin yadda aka yi ta hadu da Abdul. Tagumi ta yi hannu bibbiyu ta ce “Allah sarki Yaya Mu’azzam, ashe bai da rabon aurenki, duk da bai fada min ba na fahimci yana tsananin son ki.” Dariya kawai ta yi ba ta ce komai ba. “To amma ta ya aka yi Yasmin ta san Yaya Abdul yana son ki?” Ta tambayi Aisha da mamaki. “Akwai ranar da ta ta6a ganina a gidanshi na Kaduna tun kafin in dawo nan gida Yola” Ta amsa mata a taqaice. “Au, dama kin yi zaman Kaduna?” “Qwarai kuwa.” “Amma wallahi na ji dad'i da ya kasance za ki auri yaya Abdul, daman can duk ‘yanmatan family ba a so hadin Yasmin da Abdul ba, saboda baqin halinta da girman kanta.” “Hmm! matar mutum ai kabarinsa.” Ta fadi hakan don ba ta so hirar tasu ta yi tsawo har ya kasance sun ci naman Yasmin. “Qwarai kuwa Aunty Smaily.” Harara Aisha ta watsa mata, sannan tace, “Tun lokacin da na so ki kira ni da Aunty ba ki kira ni ba sai yanzu? Wannan shi ne daga baya (wai an yi sadaka da bazawara).” Dariya ta yi ta ce “Ai yanzu ya zama dole in ce miki Aunty, idan ba haka ba Yaya Abdul ya yi quli-qulin kubura da ni” “Can dai ta matse miki. Ni kin ga kwanciyata.” Tana gama fadin haka ta juya mata baya ta daga hannuwa sama tana karanta addu’ar barci. “Mu kwana lafiya.” Ta amsa mata bayan ta fahimci ta gama addu’a. Qarfe goma sha biyu da rabi na dare kiran Abdul ya yi mata ya tada ta daga barci, murya qasa-qasa irin ta wacce ta fara barci ta amsa wayar tana fadin “Hello!” “Matata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31