Chapter 25
Chapter 25
amma ta kasa tankawa. Ihun kuka ta fara rerawa da duk iyaka qarfinta, hankalinta a tashe sai a wannan lokacin ta ji tsanar Abdul a zuciyarta. “Wannan wane irin shirme ne Aisha? Ke da za ki rarrashe ta amma kin rungume ta kina kuka kamar wata qaramar yarinya?” Muryar Daddy ce. Ba ta san lokacin da ya shigo dakin ba ta ji yana fadin haka. “Kin ga zo nan diyata.” Ya kama hannun ta ya zaunar da ita a gefen gadon sannan ya zauna a kusa da ita ya fara rarrashin ta da cewa, “Babyna komai ki ka ga ya samu bawa muqaddari ne daga Allah. Daman tun farko Allah ya qaddari a yau za a daura miki aure da Abdul-Ahad. Don haka ki yi haquri ki kwantar hankalinki, kuka ko kuma yawan tunani da saqe-saqe bai isa ya canja komai daga abinda Allah ya qaddara ba. Ko kina so mu ma mu shiga damuwa ne?” Ya tambaye ta yana kallon cikin idanunta da suka yi kace-kace da hawaye. Da qyar ta iya girgiza kai alamar “A’a.” amma sam ta kasa amsawa saboda baqin ciki. “Ni wallahi kaina ya daure Daddyn Aisha, na rasa dalilin da ya sa Ardo ya yi daurin auren baby a yau, kuma ba tare da sanin kowa ba, domin duk matan gidan tambaya ta suke wai ya aka yi haka ta faru? Daman akwai soyayya tsakanin Aisha da Abdul ne? kuma me ya sa aka daura aurensu ba tare da an sanarwa da kowa ba? rashin sanin taqamaiman amsar da zan ba su tare da tunanin halin da Baby za ta shiga ya sa na silale daga gidan Ardon zuwa gida” “Ba ku kadai kanku ya daure game da wannan al’amari ba, kuma abinda na lura da shi shi ne, daga Allah sai Ardo da Baba Ibrahim da Baba Bello da shi kanshi Abdul suka san dalilin da ya sa aka yi wannan daurin auren. Fuskar kowane mai rai cike take da matuqar mamakin al’amarin. Amma nasu fuskokin cike yake da farin ciki, kuma harna gaji da zama ba ta ga suna da niyyar tasa iyalan gidan don warware tufkar da suka yi ba, kuma kin san idan ba su ne suka magantu ba dole mu yi biyayya a gare su" “Allah ya sa hakan shi ya fi alkhairi..” In ji Mummy. “Amin summa amin, addu’ar da ya dace mu yi kenan tunda mai afukuwa ta riga ta afku.” “Qewarai kuwa.” Hayaniyar da suke jiyowa tana tashi sama-sama a falo ya sa suka fice daga dakin don ganin ko su waye. Su Zainab ne, Mu’azzam ya kwaso su don su yi wa Aisha tsiya, ganin yanayinta ya sa suka guntse komai a cikinsu suka koma ba ta haquri tare da kalaman kwantar da hankali. Ba su bar gidan ba sai qarfe biyar na yamma. Bayan tafiyarsu ne Mummy ta tilasta wa Aysha ta je ta yi wanka ta canja kaya ko tayi fasali. Idanunta duk sun tasa saboda kuka, har a wannan lokacin ba ta daina fakar idanun su Mummy tana share hawaye ba. kanta ya yi buzu-buzu tamkar wata bararo. Zama ta yi dirshan a bandaki tana ci gaba da risgar kuka, ita kadai ta san irin takaicin da yake cikin zuciyarta. “Wai har ita Abdul zai yaudara? Bayan ga yadda suka yi da shi tun ranar da ya iso Yola ta nuna mishi ba ta amince ba shi ne zai zagaya ya sa a daura mata aure ba tare da shiryawa hakan ba? Jin an bud'e qofar dakinta an shigo ya sa ta yi saurin fara wankan tana share hawaye. Tana daure da babban tawul a jikinta wanda ya rufe ta tun daga qirji har zuwa rabin santala-santalan cinyoyinta, wani qaramin towel din ta rufa a kanta, domin ta dauke ruwan dake diga daga gashin kanta, saboda wanke kan da ta yi. Idanunsa qur a kanta kamar yau ya fara ganin qirar jikinta. Harara ta watsa tare da jan wani dogon tsaki ta nufi gaban madubi ta janyo kujera ta zauna domin ganin yadda ya yi dai-dai a kan gadonta. Ya kasa magana sai bin ta yake da ido yayin da ita kuma jira take ya tanka ta zazzage mishi duk wani takaici dake danqare a zuciyarta. Da alamun neman ta inda zai fara magana yake yi, don haka ta fara shafa mai tana watsa masa harara ta jikin mudubi. Har ta gama shafa mai ta goga powder a fuskarta bai ce komai ba. akwatunan kayan sawarta ta nufa ta bude na saman ta dauko best fara qal, da wandonta fari mai kama da dan pant ta ajiye su a gefe daya, sai da ta sauke akwatuna har guda uku ta bue na hudu ta ciro atamfar Super Holland wacce aka yi wa dinkin riga da siket ta ajiye kusa da inner wears dinta. Lura da ya yi tana kici-kicin daga akwatunan ta maida saboda nauyinsu ya taso da hanzari yana fadin, “Matata bari in taimaka miki…” “Dakata!” Ta katse shi tun kafin ya ida aje numfashin maganarshi. “Da can kai kake taimaka min? ko kuma yanzu wani sabon salon iyayi ne? wallahi Abdul ka ba ni mamaki, ban ta6a tunanin kana daga cikin maza masu tsananin son kansu ba. tun a shekaran jiya na fada maka ban amince da daura aurenmu ba sai bayan cikar alqawarinmu, amma ka yi biris da ni, ka je ka yi abinda ranka yake so. Don haka ka shirya kwasar duk wani wulaqanci da za ka gani daga gare ni.. haka kawai? Ina zaman zamana za ka jaza min in zama mara alqawari a gurin ‘yan’uwana? A gabanka na sanar da su na amince zan aure ka ne idan ka miqa wadanda suka kashe Sadiya gurin hukuma aka yanke musu hukunci daidai da abinda suka aikata, amma babu wani bincike da ka yi ka zo ka yi qulla-qullarka ka sa aka daura min aure da kai. Ga wannan fitsararriyar matar taka da ba ta ganin kowa da mutunci.. kai kuma ka zama sullutun namijin da bai iya daukar kowane irin hukunci ga wanda aka… " Jin kunenshi ba za su iya ci gaba da sauraren wadannan qananan maganganun nata ba ya sa ya daka mata tsawa yana fadin, “Ya ishe ki haka! Na san na yi miki ba daidai ba, da na sa aka daura aurenmu ba tare da son ranki ba, amma ya kamata ki saurara ki ji uzurina, kafin ki yanke min duk wani hukunci da kike ganin ya dace.” “Me zan saurara?” Ta katse shi tana kuka. “Qarya? Ko kuma irin maganganunka na yaudara da ka saba fada min a koda yaushe? Na dawo daga rakiyarka Abdul, wallahi ka fice min daga rai. A hakan ne har kake iqrarin sadaukar da taka rayuwar a kan tawa rayuwar? Wannan ai zalunci ne da rashin sanin girman alqawari…” duk yadda ta so ta ci gaba da magana kuka ya hana ta, don haka ta zube a tsakar dakin tana ci gaba da jan sautin kukan. Hankalinshi ya kai qoluwa gurin tashi, ya san zai fuskanci qalubale daga gare ta na daura musu auren da aka yi, amma bai ta6a tunanin za ta qi ba shi hadin kai ya wayar mata da kai a kan dalilin da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31