Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 21

Chapter 21

A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ko wane ne shi.” “Idan lokaci ya yi ai za ki san shi.” “Ni dai yanzu nake so in gan shi, idan kuma ba haka ba in binciko shi da kaina.” “Allah dai ya hana bincike...” Tana gama fadin haka ta tashi daga inda take zaune, ta ce wa su Maryam yanzu za ta dawo. Yana zaune a cikin falon gidansu, duk inda ta yi idanunshi suna kanta. Ba yadda bai yi da ita ba a kan ta zauna ya gama qare mata kallo babu abinda yake buqata sai ita, amma ta qiya. Sai da ta kusan cika dan teburin gabanshi da drinks kala-kala da snacks (da yake Mummy ba ta rabo da kayan ciye-ciye irinsu saboda baqin bazata). Sannan ta nemi guri ta zauna a gabanshi dirshan a qasa suna musayar kallon so da qauna... Shi ma qasa ya sauko suna zaune kusa da kusa, ganin ya kasa magana sai kallo da yake bin ta da shi, yana sauke ajiyar zuciya a kai-akai ya sa ta hura iska a idanunshi don dawo da shi cikin hayyacinsa. Tana dariya don ganin kallon da yake mata yana neman yin yawa. “Wash Allah zuciyata...” Abinda ya fara furta mata kenan tare da dafe saitin zuciyarshi da hannu biyu gami da lumshe ido. Ruwan Swan mai sanyi ta tsiyaya kadan a kofi sannan ta qara matsowa kusa da shi ta matsa da hannunta mai riqe da kofin kusa da bakinshi ta ce “Bude bakinka ka sha ruwan sanyi Modibbo.” Bai musa wa umarninta ba ita ma kuma ba ta ji kunya ba gurin shayar da shi ruwan, sai da ta tabbatar ya sha yadda ba zai mishi yawa ba, sannan ta janye hannunta. Kayan ciye-ciyen da ta ajiye a gabanshi ta fara ciyar da shi tana hada masa da lemo mai sanyi har sai da ta fahimci ya qoshi, sannan ta matsar da kayayyakin gefe daya ta dawo kusa da shi ta zauna. Sai a wannan lokacin da dan ji kunya na neman ziyartar ta, domin ta fahimci tun tana ba shi abinci dan siririn mayafin da ke kanta ya zame zuwa qasa ba tare da ta sani ba. “Allah ya yi miki albarka matata.” Ya furta cikin sassanyar muryarshi. “Amin mijina.” Ta amsa idanunta a qasa, amma fuskarta cike da murmushi don jin dad'in addu’ar da ya yi mata. “Matata kin san wani abu kuwa?” Ya tambaye ta bayan ya kama hannunta guda daya yana qoqarin dawo da hankalinta kanshi. “A’a, sai ka fada mijina.” Ta amsa masa kai tsaye bayan ta dago kanta suna kallon juna ido cikin ido, amma ba ta yi qoqarin janye hannunta na dama da ya riqe ba. “Kin san ina son ki ko?” Ya sake tambayar ta yana qara qure ta da kallo. “Na sani mijina.” Ta amsa cikin sanyin murya domin ba ta san me zai sanar da ita ba. “Kin san ba ni da niyyar cutar da ke ko?” Izuwa yanzu ta lura kamar hankalinsa yana neman tashi tun kafin ya isa inda yake son sanar da ita. Don haka ta kamo hannayenshi duk biyun ta riqe sannan ta wadata fuskarta da murmushi ta amsa masa da cewa “Na sani mijina.” “Idan ba ki manta ba, su Aunty Hassana sun ce sun za6a miki ni a matsayin mijin da za ki aura ko?” Ita ma yanzu jikinta ya fara sanyi, domin ba ta san me yake qoqarin sanar da ita ba. Don haka kai kawai ta daga masa alamar “Eh” amma sam bakinta ya yi mata nauyi gurin amsawa. “Idan duk kin amince da wadannan maganganun, me zai hana ki amince min a daura aurenmu da na Yasmin gaba daya a jibi ranar Asabar matata?” Da sauri ta sake riqon da ta yi wa hannayensa, sannan ta kau da fuskar ta gefe, domin akwai wasu saqonni da yake aikowa daga idanunshi zuwa nata. Idan ta kalle shi bara ta samu damar iya maida mishi duk amsar tambayar da zai yi mata ba ko da kuwa za ta cutu. Ba ta tsammaci jin wannan maganar daga bakinshi ba don haka sai da ta dauki tsawon daqiqa sittin tana saqawa da kwancewa, sannan ta ce “Ina bincikenka ya tsaya a kan wadanda suka kashe Sadiya?” Hannunta ya sake kamawa don ta dawo da hankalinta da fuskarta zuwa gareshi amma sam ta qi ba shi haxin kai. Don haka cikin sanyin murya da alamun karaya qarara ya ce, “Bincikena yana nan yana tafiya matata, kuma wallahi ina daf da kai wa gaci.” “To in haka ne, don me za ka tada maganar aurenmu bayan ka san a kan wannan yarjejeniyar na yarda zan aure ka?” A yanzu idonta yana cikin nashi, ta yi masa tambayar domin ta kasa fahimtar inda ya dosa. “Ki fahimce ni don Allah matata, auren mu kawai za a daura ba wai za a yi biki a kai ki gidana ba ne. Sai bayan gama bincikena sannan za a yi komai ki koma gidana da zaman aure.” “Idan dai haka ne ai babu amfanin daura auren kenan, kawai ka bar wannan maganar.” “Akwai amfanin daura auren mana Aisha. (Ya kira sunanta kai tsaye wanda rabon da ya kira ta da hakan tun tana gidanshi a Kaduna). Ba zan boye miki ba, a cikin kwanaki ukun nan sam ba na iya barci duk don saboda ke. Ina tsananin jin tsoron abinda zai je ya zo. Ni kuma duk abinda zai same ni na fi son ya same ni da igiyar aurena a kanki Aysha. Idan duk mutanen duniya sun guje ni ba ni da damuwa ko kadan matuqar ina tare da ke Aysha.” Sam ta rasa gane inda maganganunshi suka sa gaba, abinda ta fahimta kawai akwai wani abu da yake boye mata wanda duk iya hangenta ba ta hango shi ba. Don haka ta ce, “Ka san ina son ka Abdul, a kanka na sauya duk wani tsari da akala na rayuwata, don haka bana tunanin akwai wani abu da zai faru a gaba wandda zai sana juya maka baya sai dai idan babu rayuwa ta ko kuma Kai ka rigani mutuwa wanda kuma bana fatan hakan ta kasance. Ka kwantar da hankalinka, kamar gobe ne zaka ga komai ya wuce mun zama daya a qarqashin inuwar auratayya. Ajiyar zuciya Abdul yake saukewa da sauri da sauri wanda har yaso ya ba ta tausayi, idanun ta cikin na shi cike da hawaye take kallonshi, hannuwanshi duk biyu ya dafe saitin zuciyarsa yace “Nan zai iya fashewa ne kawai idan aka nemi a raba ni da soyayyarki Aysha...” Jingina bayanta da jikin kushin tayi, hawaye masu zafi suna tsiyaya daga idanunta ta ce, “Wai kodai mutuwa zanyi ne Abdul? Hankalin Abdul ya tashi da ganin hawayenta, don haka ya yi saurin korar duk wata damuwa daga ranshi ya fara rarrashin ta yana fada mata kalamai masu dad'i da kwantar da hankali. Ita ma Ayshar don ta kwantar da hankalinsa ta daina kukan amma bawai don nata hankalin ya kwanta ba. Sam ta kasa fahimtar inda maganganunshi suka sanya gaba, wayarta ta janyo don duba lokaci, ganin agogon falon ya nuna qarfe takwas saura kwata na dare, an yi magariba har an idar da sallar isha’i duk basu da labari, miscalls din su Zee kuwa

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});